Salon Kwalliyar Zance a Wakar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris

    Citation: Abdullahi, M. (2024). Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Saidu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 311-315. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.042.

    Salon Kwalliyar Zance a Waƙar Sa’idu Faru Ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris

    Na

    Musa Abdullahi
    Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau
    abdullahialhaji707@gmail.com
    08037765415

    Tsakure

    Waƙa wata hanya ce ta isar da saƙonni cikin salo mabambanta, wato ta baka ko rubutacciya.Waƙoƙin baka da rubutattu hanya ce mai gamsarwa wajen isar da saƙo. A wannan maƙala, an yi ƙoƙarin bibiyar waƙar Sa’idu Faru ne makaɗan baka, kuma makaɗan fada, domin fito da irin hikima da fikira da zalaƙa da basirar da Allah ya ba shi wajen sarrafa harshe. A cikin wannan waƙa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kwalliya da nuna darajar da Sarki yake ɗauka da shi, inda yake siffanta Sarkin Zazzau da wasu dabbobi masu daraja da ƙrfi da kwarjini. Haka kuma da danganta shi da gidan da ya fito na sarauta. Nazarin zai taɓo waƙar da Sa’idy Faru ya yi wa Sarkin da taƙaitaccen tarihin Sarkin da ire-iren kirarin da ake masa a wurare mabambanta. An bi hanyoyi da ya kamata da amfani da dabaru akan yi ƙoƙarin nemo waƙar ta Sarkin Zazzau da sauraronta; don zaƙulo bayanan da ake buƙata a waƙar, da kuma saƙon zuwa ga gaɓar da ake magana a kai. An yi ƙoƙarin ɗora wannan bincike a kan Ra’in mazahabar Nason Adabi a Al’adu (Folk – Cultural Theory) wanda William Bascom ya ƙirƙira, sannan kuma aka samu mabiya daga ƙasar Amurka waɗanda suka bunƙasa shi. Binciken ya ƙare da sakamakon da aka samu yayin gudanarwa.

    1.1 Gabatarwa

    Fito da saƙonni daga waƙoƙin baka muhimmin abu ne da yake ƙara fito da fasahar makaɗan baka tun a asali har zuwa yau, haka kuma har zuwa gobe. A bisa ɗabi’a ta mutum, an ce, idan kana da kyau ka ƙara da wanka, yakan so a daraja shi da nuna wasu halaye ko ayyukan da yake aiwatarwa na ƙwarai a haskaka shi da kwalliya mai kyau. Hakan ta sanya makaɗan baka amfani wannan dama wajen shirya waƙoƙi da nufin fito da kwarjinin mutum ta hanyar siffanta darajar da mutum ke da shi inda suke danganta mutum da dabbobi masu ƙarfi da iko wajen kwarzantawa. Makaɗan Hausa sukan yi amfani da kwalliya a waƙa ta hanyar ambaton asali da dangantakar wanda suke wasawa da iya mulki ko kyauta da karimcinsa da makamantarsu.

    Maƙasudin wannan maƙala ita ce duba yadda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kwalliya a waƙar da ya yi wa Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris, ya yi amfani da wasu kwalliya wajen isar da saƙonni da suka zama tubalan ginin kwalliya ga Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris. Waɗannan hanyoyin isar da saƙonni kywa da mawaƙin ya yi amfani da su sun haɗa da siffanta Sarki da danganta halin Sarki da irin darajar wasu dabbobi a gwarzaye da ambaton kyawawan halayensa da adalci da iya mulki da kuma kyautata da karamcinsa. A wannan nazari an yi amfani da ɗiyoyin waƙoƙi da makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Zazzau na Alhaji Dakta Shehu Idris da nufin kwarzamta shi a kan halaye da ɗabi’u da makamantarsu.

    2.1 Takaitaccen Tarihin Waƙar Baka

    Masana sun yi ƙoƙarin bayyana asalin samuwar waƙar baka a ƙasar Hausa, daga ciki akwai ra’ayin Gusau (2003:5-6) inda ya kawo hasashe guda uku waɗanda yake ganin sune asalin waƙar baka, waɗannan hasashe kuwa su ne; Ra’ayi na farko, suna ganin ana jin ɗan Adam ya ƙagi waƙa ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta, daga nan ya gano noma sai waƙa ta ƙara haɓaka. Ra’ayi na biyu kuwa, an nuna cewa, ana ganin waƙa ta samo asai ne daga wani maroƙi ‘Sasama’ domin haka a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutumin ne. A ra’ayi na uku kuwa, ana ganin waƙa ta samo asali ne daga bautar iskokai.

    2.2 Kwalliya

    Kwalliya ado ce da ke ƙara fito da kyau a zahiri ko da kuwa abin da ya yi kwalliyar ko aka yi mai kwalliyar bai kai haka ba. Domin akan ce “Ko kana da kyau ko ƙara da wanka” wannan na nuna cewa komi mutum yake yi wajen mu’amala da mutane ya riƙa kyautatawa, don biyan buƙatun da ya dace da kuma farantawa mutane rai. A waƙar Sa’idu Faru ta Sarki Shehu Idris ya haskaka Sarki ya kwarzanta shi ya siffanta shi ta hanyar yi masa kwalliya da sigar darajar ƙarfi wajen danganta shi da karamar da wasu dabbobi, wadda kowa ya ji sunayensu, an san cewa su ne kan gaba da kuma jagoranci a daji alal misali, irin su bijimin Sarki, da taron giwa da jan zaki, wannan waƙar ta fifita shi da ɗaukaka shi fiye da sauraron abokan neman sarautar da suka yi takarara, kuma ya kayar da su, Allah ya ba shi sarautar zazzau a wannan lokaci.

    Makaɗan baka, suna amfani da ire-iren waɗannan hanyoyi domin su siffanta mutum tare da kamanta mutum da halaye na dabbobi wato dabbantarwa masu kyawon hali ko kuma marasa kyawun hali, ya danganta da irin waƙar da saƙonnin da suke ciki.

    2.3 Ra’in Bincike

    Ra’in mazahabar Nason Adabi a al’adu (Folk – Cultural Theory) wadda cikin, William Bascom (1912-1981) ya ƙirƙire ta, shi ne ra’in da ya cancanci karɓar wannan nazari. Wannan mazahaba tana kallon yadda hikima da sauran dabarun fasahar baka suka danganci abubuwan da al’umma suke gudanarwa. Har wa yau, mazahabar ta faɗaɗa zuwa ga abubuwan da suka danganci fasahar zamani ta amfani da na’urorin kwamfuta wajen alaƙanta maganganun adabi da al’adu.

    2.4 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

    Kakan kakan Sa’idu Faru sunansa Alu Mai Kurya, mutumin Sabon Birnin Gobir ne, wanda yake ya yi kiɗan Kurya tun zamanin Sarkin Gobir Babari.  Alu Mai Kurya shi ne mai kiɗan kurya, idan Sarkin Gobir Babari ya fita fagen fama, wato yaƙi. Domin haka Alu Mai ƙidan kurya shi ne tushen kiɗa a zuri’ar su Sa’idu Faru. Alu  ya yo ƙaura daga Sabon Birni zuwa garin Faru da ke yankin  Maradun shi da sauran iyalansa gaba ɗaya sakamakon halin zamantakewa na yaƙe- yaƙe a wancan zamani. Alu Mai Kurya shi ne ya haifi Audu, shi kuma Audu ya haifi Abubakar, shi kuma Abubakar ya haifi Sa’idu Faru. Kamar yadda tarihi ya nuna Audu bai ɗauki sana’ar kiɗa da muhimmanci ba, noma da kasuwanci ya tasa a gaba.; Akwai uban ƙasar Faru da ake kira Ɗangaladima shi ne dalilin da ya sa Abubakar ya shiga harkar kiɗa da waƙa, shi ne wata rana ya ce wa Abubakar kai ɗan makaɗa ka ne, amma ka ƙi sana’ar gidanku ta gado.

    Ana cikin haka sai ga wani baƙon mawaƙi wanda ake kira Zumbul ya zo daga garin da ake kira ‘Yar kasuwa. Zumbul ya nemi gidan masu kiɗa da waƙa sai aka kai shi gidan Abubakar.Da suka gaisa bai tsaya ɓata lokaci ba, shi Zumbul ya tambayi Abubakar cewa yaya za a yi ga uban ƙasar Faru? Shi kuwa Abubakar nan da nan ya jagoranci Zumbul sai gidan uban ƙasar Faru. Kan hanyarsu zuwa gidan uban ƙasar; Abubakar ya yi wa Zumbul bayani dangane da mai riƙon ƙasar Faru. Da suka isa ƙofar fada, sai Zumbul ya shiga rera waƙa. Wannan haɗuwa tasu da wannan mutum Zumbul shi ya assasa sanadiyar da mahaifin Sa’idu Faru ya kama sana’ar kiɗa ta waƙa.

    An haifi Alhaji Sa’idu Faru a tsakanin shekarar 1936-1938, lokacin mulkin Sarkin Musulmi Hassan Ɗan Mu’azu zuwa farkon mulkin Sarkin Musulmi Abubakar III. Sannan kuma ya yi karatun mahammadiyya daidai gwargwado, ya kuma yi karatun yaƙi da jahilci, ya bi mahaifinsa yadda ya kamata sannan kuma ya tafi yawon kiɗa da waƙa fiye da mahaifinsa.

    2.5 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris

    Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris Ɗan Malam Idrisu Auta (Mai Unguwar Limancin Kona) Ɗan Sarkin Zazzau Malam Sambo, Ɗan Abdulkarimu Sarkin Zazzau. Ya fito ne daga cikin Zuri’ar gidan Sarautar Katsinawa na Zazzau, ƙarƙashin jagorancin Kakan Mahaifinsa wato Malam Abdulkarimu Sarkin Zazzau, wanda shi ne Sarki na farko a gidan sarautar Katsinawa na Zazzau, kuma shi ne Sarki na uku a jerin Sarakunan ƙasar Zazzau na mulkin Fulani a Zazzau.

    An haifi Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris a ranar ashirin ga watan Fabrairu na shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da talatin da shida (20th February, 1936), a Unguwar Rimin Tsiwa cikin garin Zariya. Ya  yi karatun addinin musulunci a wurare da dama kamar gidan Malam Bawa, da makarantar Malama Aminatu ‘yar Liman Muhammadu Lawali Kwarbai, da gidan Abubakar da ke Unguwar Iya Zariya, inda a nan ne ya sauke  Alƙur’ani mai girma. Daga nan sai aka sanya shi makarantar boko da ake kira Town School a ƙofar Kuyambana cikin garin Zariya a shekarar 1947 – 1950. Ya yi karatu a Middle School a shekarar 1950 – 1955. Daga nan ya tafi Katsina Training College a 1957. ya kumaAlhaji Shehu Idris ya yi aikin koyarwa a Firamare a shekarar 1958 a garin Hunkuyi,  da Zangon Aya.,  Daga baya aka yi masa sauyin wurin aiki zuwa Faki, daga nan ya koma makaratar firamare ta Ƙaura Zariya a 1961. Ya sami sauyin aiki zuwa  ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautun jihar Kaduna.

    An naɗa shi sarautar Wakilin ofis na Zazzau daga baya kuma aka naɗa shi sarautar Ɗan Madamin Zazzau, haka kuma hakimin Birni da kewaye a shekarar 1973. Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris, ya hau gadon sarautar Zazzau bayan rasuwar Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu a shekarar 1975, shi ne Sarki na goma sha takwas (18) a mulkin Fulani, kuma Sarki na haɗu  a gidan Sarautar Katsinawan Zariya. Ya rasu, a  ashirin ga watan Satumba, 2020. Sa’idu ya bar matan aure huɗu da ‘ya’ya da yawa maza da mata. (Fagaci 2020).

    2.6 Alaƙar Makaɗa Sa’idu Faru da Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris

    Alaƙa ta ƙullu sosai tsakanin makaɗa Sa’idu Faru da Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris tun zamanin Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu, tun shi Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris bai zama Sarki ba, yana hakimi. Duk makaɗa da mawaƙar da suka zo Zariya idan Sarki Muhammadu Aminu zai yi sallama ga mawaƙan ko makaɗan, ta hannun shehu Idris ake bayarwa, kuma duk sallamar Sarki Muhammadu Aminu ya bayar tufafi ne ko kuɗi sai Shehu Idris ya yi wa makaɗan ko mawaƙan wata kyauta ta daban. Wannan hali na Shehu Idris da yake yi wa baƙin makaɗa ya sa duk makaɗan da Allah ya kawo Zariya suna jin daɗin wannan ɗabi’a ta Shehu Idris tun kafin ya zama Sarki, don haka da ya zama Sarki makaɗa da mawaƙa suka dinga zuwa, a cikinsu akwai makaɗa Sa’idu Faru wanda ya zo Zariya tun farkon shekarar da Allah ya ba Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris Sarautar Zazzau a shekarar sha-huɗu ga watan Nuwamba, shekara ta 1975.

    3.1 Salo A Waƙoƙin Baka

    Wannan wata hanya ce wadda makaɗi ke kyautata zaren tunaninsa ya sarrafa shi cikin azanci don ya cim ma burinsa na isar da saƙo a waƙa. Salo a waƙoƙin baka abu ne wadda yake daɗa fito da ainihin kyansu ko muninsu, ta haka za a iya gane waƙoƙi masu karsashi, masu hikima da balaga da kuma waƙoƙi marasa ma’ana da inganci. Ma’auni ne na rarraba zaƙin waƙa ko ɗacinta. Haka kuma, wata dabara ce da za a iya yi wa harshe ado da ita kuma haya ce ta sarrafa harshe a jujjuya shi ta yadda za a iya taƙaita manufa ko a sakaya ma’ana ko kuma a kaifafa tunani. Gusau, (2023)

    A waƙar Sa’idu Faru ta Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris, ya yi amfani da salon kwalliyar zance domin taa ɗaya daga cikin dabarun da makaɗi yake ɗaukar siffar wani abu ya ba wani abu ba tare da ambaton suna ba a tsakani. Wannan salo ne dake kawo hoton abu yadda mawaƙi ke buƙatar mai karatu ko sauraron waƙarsa ya kale shi da idon zuciyarsa ko tunaninsa. Yahaya, (1997:14).      

    3.2 Waƙar Makaɗa Sa’idu Faru na Sarkin Zazzu Alhaji Dokta Shehu Idris

    Waƙar:Gagara Gabas bajimin Sarki

    Asma:Allah ya biya maka buƙata kai ab babba ga gidan Sambo

    A nan mawaƙin na ƙoƙarin nuna wa jama’a da shi kansa Sarki cewa shi ne ya yi nasarar hayewa gadon Sarautar wato shi Allah ya zaɓa. Ya danganta shi da bajinta inda kowa ya san cewa dabba ne wanda ya riƙa ya kuma fi sauran dabbobi ƙarfi ba yadda za su yi da shi. Irin wannan kwalliya da ya yi wa sarki shi ne zai ƙara fito da darajarsa da kwarjini a idon mutane da duniya baki ɗaya.

    Waƙar: Toron Giwa ƙi fasawa x 2

    Amshi: Gogarma Magaji jan zaki,

    : Gagara gasa bijimin Marafa,

    : Shehu halaliyar gidan Mamman.

    Sa’idu Faru ya yi ƙoƙarin nuna matsayin ƙarfin mulkin da Sarkin Zazzau Alhaji Dakta Shehu Idris yake da shi, inda ya siffanta irin ƙarfin da wannan dabba ke da shi wato Giwa, ya ce toron Giwa. A nan yana nufin riƙaƙƙen Giwa nauyi ya yi amfani da wannan kwalliyar ne domin ya nuna irin karɓuwar da Sarki ya samu a masarautar.

    Waƙar: Namijin Zaki Shehu kai da karfi.

    Amshi: Ba a haye maka cikin birni,

    : Ba a haye maka cikin daji.

    A nan yana ƙara nuna irin isan da sarki yake da shi da kuma cewa duk ta inda aka biyo domin a danne Sarki ko a ci galabansa, to ya fi ƙarfinsu duka gaba da baya (magauta). 

    Waƙar: Mai abu nai ya karɓi abu nai x 2

    Amshi: Karyar ƙulle- ƙulle ta ƙare x 2

    : Gagara gasa bijimin Sarki Shehu halaliyar Gidan Mamman.

    Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna wa jama’a a cikin waƙar cewa mai abu nai ne ya karɓi abun don haka wai bare ba ne, masu shiga da fice da ƙulle – ƙullen hassada ta ƙar daga yau domin ya yi nasara a kan su ya zamo Sarki.

    Waƙar: Wasu ‘yan Sarki na biɗar Sarauta x 2

    Amshi: Raggo na kwance bai sani ba x 2

    :Yana shigifa ana mai tsibbu

    Waƙar: Koda ka zo ba a baka sarki

    : Domin ka cika nunafunci

    Amshi: Gagara gasa bijimin Sarki Shehu halaliyar gidan Mamman

    : Allah ya biya maka buƙata kai ab babba ga gidan Sambo

    A nan makaɗa Sa’idu Faru yar nuna yadda ake gwagwarmayar neman sarauta ƙarara da nuna cewa sai an riƙe an tashi tsaye duk abin da mutum ke nema sannan Allah yake ba mutum ba a kwanciya a ce haka kawai a sama nasara kuma ya sai mutum ya zama na kwarai ga al’umma ba munafurci ba cutarwa.

    Waƙar: Shehu gizago ba ka da sabo x 2

    Amsa:Mai kai kaba cire hannunka karka je a sassake ma hannu x 2

    Makaɗa Sa’idu Faru ya sake yi wa Sarki wata kwalliya da siffanta shi da gizago wajen ƙarfin mulki da tsaro ba wargi.

    Waƙar: Zariya an daɗe ana sarauta, tun zamanin Abdulkarimu bawa

    Amsahi: Amma wanga yanayi sai kai ka riƙe ƙasa tai kyau x 2

    Waƙar: Ba karya ba inji sankira x 2

    Amshi: Gagara gasa bijinin Sarki Shehu haliliyar gidan Mamman,

    : Allah ya biya maka buƙata kai ab babba ga gidan Sambo

    An nuna a waƙar cewa yanzu aka sama wanda ya da ce da iya mulkin ƙasa wato tun zamanin Sarki Abdulkarim da ya wuce ba a sanna irin wannan jajirtacce ba sai yanzu da Sarki Shehu Idris ya hau.

    Waƙar: Namijin zaki Shehu ko da ƙarfi Ba a haye maka cikin birni,

    :Ba a haye maka cikin daji.

    Amsa:Gagara gasa bijinin Sarki, Shehu halaliyar gidan Mamman.

    A waƙar an nuna da danganta darajar Sarki da ƙarfin da yake da shi namijin zaki ne shi ya yi zarra duk cikin masu neman sarautar.

    Waƙar: Ga wani ya zo biɗar sarauta x

    : Bai samu ba ya ɓata fuska x 2

    Amshi: Har ya sake datse na ƙarfi x 2

    A nan makaɗa Sa’idu Faru na ƙoƙarin nuna wa jama’a cewa wasu da suka nemi takarar sarauta da Sarki Shehu Idris ba su cancanta ba saboda irin halayyar da suke da su shi ya sa ba a zaɓe su ba.

    Waƙar: Kolo ya so a bashi Sarki x 2

    : An yi bida yana cikin daji x 2

    Amshi: Bai huta ba da wulakanci x 2

    A waƙar makaɗa Sa’idu ya yi amfani wata siffa inda ya dabbantar da wanda yake nufi ba tare da ambaton suna ba. Inda yake fifita Sarki Shehu Idris a kan duk sauran da suka nemi takarar hawa karagar Sarautar Zazzau.

    3.3 Kammalawa

    Wannan maƙalar ta yi duba ko nazari kan waƙar da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris, lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar Zazzau, inda ya kwarzantashi da yi masa kwalliya da ɗaukaka shi, an dubi taƙaitaccen tarihin shi kan sa Sa’idu Faru da na Sarkin Zazzau Shehu Idris da alaƙar da ke tsakaninsu da kirarin Sarkin Zazzau da bayani kan waƙar da Sa’idu Faru ya wa Sarkin mai suna “Gagara Gasa Bijimin Sarki’ da kammalawa sai kuma Sakamako.

    3.4 Sakamakon Bincike

    Dangane da Sakamakon wannan aiki da aka gudanar an gano cewa dai makaɗan Fada Waƙoƙinsu na cike da fasaha da balaga da hikima iri-iri. Hakan na ba su damar iya sarrafa habaici da zambo da zuga da kwalliya da kambamawa da shaguɓe ta hanyar faɗawa jama’a irin halayen kowanne mai sarauta da yadda suke tafiyar da mulkinsu.

    Haka kuma, an gano cewa makaɗa Sa’idu Faru mutum ne mai iya shaguɓe da habaici ga abokan hamayya da basu yi nasara ba wurin neman sarauta da koda ko zuga gwanin da ya yi nasara wato wanda ya ci sarautar. Sauran ‘ya’yan Sarakunan da ba su samuu sarauta ba suna gani ba yadda zasu yi, duk da cewa sun san da su ake cikin waƙar, amma ba yadda za su ce da su ake saboda ba a ambaci suna ba.

    Manazarta

    C.N.H.N (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Zaria, ABU Press.

    Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe waƙa (Sabon Tsari), Zaria, Amana Publishers Limited.

    Fagaci, A. M. (2020). Shekaru Arba’in da Biyar a Sarautar Zazzau 1975 – 2020. Published by Darul Hikima Enterprises, No. 11 Hospital Road, Tudun Wada, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

    Funtuwa, A. I. (2011) “Rabe-Raben Makaɗa da halayensu da kayan kiɗansu, cikin waƙoƙin Baka na Hausa” Littafi na biyu. Katsina: Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Tarayya.

    Gusau, S. M. (1988) “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye – Yanayensu”, kundin Digiri na uku. Kano, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2003), Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers.

    Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a ƙasar Hausa; Yanaye- Yanayensu da sigoginsu Kano; Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2003) Jagorar Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    N.E.R.D.C (1990) Hausa Meta Language, University Press Limited Ibadan, Nigeria

    Umar, M. B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishing Company Limited

    Usman, D. Et’al (2000). Alhaji Shehu Idris, The 18th Fulani emir of Zazzau. Publishers Printers and Marketers of African Books Malali, Kaduna, Nigeria.

    Yahaya, A. B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.