Tarihin Yake-Yaken Turawa a Arewacin Nijeriya: Tsokaci Da Misalai Daga Littafin Gandoki

    Cite as: Haruna Umar Maikwari da Muhammad Sani Lawan (2021) Tarihin Yaƙe-Yaƙen Turawa a Arewacin Nijeriya: Tsokaci Da Nisalai Daga Littafin Ganɗoki. Takardar da aka bugu a Mujallar ƊUNDAYE VOL. 2. NO. 4. A watan Disamba, 2021. A shafi na 123.

    Tarihin Yaƙe-Yaƙen Turawa a Arewacin Nijeriya: Tsokaci Da Misalai Daga Littafin Ganɗoki

    Daga

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Da

    Muhammad Sani Lawan

    Department of Hausa Language.
    Sule Lamiɗo University Kafin-Hausa, Jigawa State
    msanilawan@gmail.Com
    (+234) 08063161900

    Tsakure

    Wannan maƙala mai taken “Tarihin Yaƙe-Yaƙen Turawa a Arewacin Nijeriya: Tsakaci da misalai daga Littafin Ganɗoki”. An tsara ta ne bisa manufar bayyana yaƙe-yaƙen da Turawa suka yi a Arewacin Nijeriya, da abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin da kuma irin rawar da wasu suka taka wajen ganin sun ƙi yin mubayi’a ga Turwan kai tsaye. An yi amfani da dabarun bincike na karance-karancen wasu bugaggun littattafai don ganin ko yaƙin ya tabbata. Babban abin da muƙalar ta gano shi ne yaƙe-yaƙen da Bello Kagara ya faɗa a cikin littafinsa na Ganɗoki sun tabbata kamar dai kama Kwantagora da Fatika da Zariya da Sakkwato da Kano da ma sauye-sauyen wasu sarakuna da Turawa suka yi bayan sun ci Arewacin Nijeriya da yaƙi. Duk waɗannan bayanai sun tabbata a tarihi sai dai an ɗan yi wa labarin ƙari wanda zai sa mai karatu ya nishaɗantu, kuma ya yaba da ƙwazon al’ummarsa.

    1.0 Gatararwa

     Kafin ƙasar Nijeriya ta samu ‘yancin kai, an yi fama da yaƙe-yaƙe da Turawan mulkin mallaka. An gudanar da yaƙe-yaƙen tun a Kudancin ƙasar (Nijeriya), abin ya kai har a Arewacin ƙasar. Turawa sun yaƙi Arewacin ƙasar kuma sun kafa mulkinsu. Shagari, (2007) da Mani, (2007) da Aminu, (2015) duk sun bayyana cewa, Turawan mulkin mallaka sun yaƙi wasu manyan garuruwan Arewacin Nijeriya. Sun kuma zo da bayanin yadda lamarin ya gudana.

     Kafin Turawan mulkin mallaka su kakkame wasu manyan garuruwan da binciken ƙasar Nijeriya sai da aka yi ba ta kashi da su, ko da yake yaƙe-yaƙen da aka yi su suka samu nasarar kama wannan yanki tare da kuma ɗabbaƙar mulkinsu.

     Malam Bello Kagara, ya zo da tarihin zuwan Turawa a ƙasar Hausa da kuma yaƙe-yaƙen da suka wakana. Duk da cewa a wannan littafi akwai ‘yan ƙare-ƙare ciki, wannan bai hana aka zo da wasu yaƙe-yaƙen suka faru a zahiri ba tare da ƙari ba.

     Wannan maƙala za ta duba wasu yaƙe-yaƙen da aka yi a Arewacin Nijeriya da kuma yadda suka auku da yadda Malam Bello Kagara ya kawoa cikin littafinsa.

    1.1 Manufar Bincike

    Babban manufar wannan bincike ita ce nazartar wasu yaƙe-yaƙe da suka gudana a Arewacin Nijeriya lokacin da Turawan mulkin mallaka suka zo. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali kan:

    i.                    Bayyana yaƙe-yaƙen da Turawa suka yi a Arewacin Nijeriya.

    ii.                  Fito da abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin.

    iii.               Bayyana irin rawar da wasu suka taka wajen ganin sun ƙi yin mubayi’a ga Turwan kai tsaye.

    1.2 Ra’in Bincike

    An zaɓi a saka wannan maƙalar a ra’i tarihi da yanayin wuri (Historical Geographical Theory). Wannan ra’i yana magana ne a kan asali da dangantakar labarun gargajiya da al’umma. Kuma tana tantance hikimamin ɗan Adam da al’adunsa ta lura da tarihin al’umma da yanayin mazauninta. Gusau, (2015:19). Lura da cewa wannan ra’in yana magana ne a kan tarihin al’umma ya sa muka ga ya dace mu yi amfani da wannan domin kuwa Malam Bello Kagara ya yi amfani da tarihin faruwar wani yaƙi da Turawan mulkin mallaka suka yi a Arewacin Nijeriya ya gina labarinsa a cikin littafinsa na Ganɗoki.

    1.3 HanyoyinGudanar da Bincike

    Wannan maƙalar ta kammala ne ta hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da muƙalu da masana da manazarta suka gudanar. Lura da cewa, labarin da Malam Bello Kagara ya zo da shi a littafinsa na Ganɗoki akwai ƙamshin gaskiya a wasu bayanai ya sa maƙalar ta bi hanyar karance-karancen wasu littattafai don gano gaskiyar abin da ya tabbata da kuma warware inda ƙari ko ruɗani suka bayyana. Yin wannan shi ya ba da damar:

    i.                    Tantance ingancin duk wasu bayanai da aka samu a cikin littafin Ganɗoki.

    ii.                  Samun bayanai game da yaƙe-yaƙen da aka yi a Arewacin Nijeriya.

    iii.               Samun bayanai sahihai na ainihin abin da ya faru lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka.

    2.0 Wane ne Malam Bello Kagara?

     Malam Bello Kagara shi ne marubucin littafin “Ganɗoki”. Kuma sananne ne a sha’anin rubutun zube. Littafinsa (Ganɗoki), ya zo na biyu a gasar da aka yi a shekarar 1933. An haife Malam Bello Kagara a shekarar 1890 a Kagarar Madakin Tegina ta Jihar Neja, amma mahaifinsa mutumin Sakkwato ne. Malam Bello na da wayo lokacin da Turawa suka yaƙi al’ummar Kwantagora, kuma da shi aka yi gudu a wannan lokaci, bai wuce ɗan shekara goma sha ɗaya ba. Da aka sako Sarkin Sudan, da shi da iyayensa aka koma da su a Kwantagora har aka yi wa mahaifinsa Alƙalin Kagara. Ya yi karatun Arabiyyaa wajen ubansa. Da Turawa suka fara kafa makaranta a Kano an aika da shi ya yi karatunsa a can. Bayan ya ƙare karatu ya fara aikin malanta. Bello ya shaidi wasu yaƙe-yaƙe da idonsa, kuma yana da labarin abin da ya faru. Ya yi amfani da abin da ya sani na zuwan Turawa a Arewacin Nijeriya ya gina littafinsa. Mafi yawan abubuwan da ya faɗa a littafin gaskiya ne, sai dai kuma ya saka almara a ciki.

    3.0 Littafin “Ganɗoki”

     Wannan littafi shi ne wanda Malam Bello Kagara ya rubuta, kuma shi ne littafin da ya zo na biyu a gasar da aka yi a shekarar 1933, wadda hukumar Talifi ta shirya.

     Littafin na da shafuka arba’in da takwas (48), an nuna tsare-tsaren gargajiyar Bahaushe ta fuskar mulki da yadda ake shirya kai hare-hare da yaƙe-yaƙe a ƙasar Hausa.

     Dangane da yaƙe-yaƙe da Hausawa kuwa, littafin ya shafi shigowar Turawa a ƙasar Hausa da irin yaƙe-yaƙen da aka yi kafin a kafa mulkin mallaka a Arewacin Nijeriya.

     Ganɗoki shi ne sarkin yaƙin wancan lokaci, duk da yake mawallafin ya gina littafinsa kamar tatsuniya, amma kusan a ce wani ɓangare na littafin abu ne da tarihi ke tabbatar da faruwarsa (wato ya faru a zahiri). Idan aka yi la’akari da yadda mai littafin ya gina labarinsa yana cewa, “A lokacin da Turawan mulkin mallaka suka nufo ƙasar Kontagora sai ya tarbe su da yaƙi. Wannan maƙalar za ta duba yadda tarihi ya tabbatar da waɗannan abubuwa

    4.0 Asalin Kwantagora

     A cikin wani littafi da wani D. O. (District Officer) ya rubuta, ya ba da labarin zamansa a Kwantagora tun farkon zuwan Turawa. Ya ce “Na je Kwantagora ni ne ma na wakilci Razdan na wurin lokacin da ya tafi hutu. Ainihin barikin garin kamar mil ɗaya yake daga gari, kuma ga wani cikin sagagi. Bayan wurin kuma sai mutum ya yi tafiya mai nisa duk yana cikin sagagi bai kai gida ba. Cikin kowace tafiyar mil ɗaya da ka yi, ba za ka ga mutum fiye da shida ba. Watau idan ka tsaya wuri ɗaya, ka yi mil ɗaya Gabas, ka yi mil ɗaya Yamma, ka yi Kudu ka yi Arewa, to, iyakacin mutanen da za ka gani ke nan. Ita Kwantagora dai duk labarinta tun can farko na karkashe jama’a ne, da shafe garuruwansu. Ainihin sarkin da ya fara cin Kwantagora shi ne Sarkin Sudan Umaru Nagwamatse, ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarautar Sakkwato. Saboda tsananin tsoron Umaru da ake yi a Sakkwato sai al’amarin ya zama tilas gare shi ya fito ya bar ta. Saboda haka ya fito daga Sakkwato, sai ya yi kudu yana tafe yana yaƙi. Ya kuwa tara rundunar mabiyansa masu yawa. Galibi mabiyan nan nasa kuwa, duk masu fitina ne sosai su ma. To shi ne ya zo da mutanensa ya kafa Kwantagora. Dalilin da ya sa aka sa wa wannan sabon gari sunan nan, an ce Sarkin Sudan da kansa ya ce wa mabiyan nan nasa su kwantad da gorunansu tun da sun yi garin kansu. Domin da a nan ƙasar kusan duk matafiyi ka gan shi da gora rataye, ciki ne zai zuba guzurinsa. To su ma mutanen nan na Sarkin Sudan da gorunansu suke tafe. Da suka kafa gari, shi ya sa Sarkin ya ce masu ai sai sun aje goruna, amma maimakon ya ce su ajiye sai ya ce su kwantad da su, wannan ko shi ne mafarin sunan nan na ‘Kwanta-gora’ ke nan. A hankali-a hankali har sunan ya zama Kwantagora, yadda ake ambatonta a yanzu.

     Daga ainihin wurin nan da Umaru ya kafa, sai ya yi tafiya mai nisan gaske ya kai hari, ya samo ganima mai yawa, domin shi jarumin gaske ne. Ya kashe na kashewa, ya kamo na kamawa, ya washe gidajen mutane ya bautar da su ta inda duk Sarkin Sudan ya bi ba za ka iske komai ba sai kufai. Wane mutum! Har zuwa rasuwarsa kuwa haka ya yi ta yi.

     Da babban ɗansa ya gaje shi sai ƙasar ta sami zaman lafiya, ba tashin hankali. Bayan rasuwar babban ɗan, sai ƙanensa ya hau gado. Shi kuwa ƙanen babban ɗan nan kamar ubansu yake wato shi ake kira Sarkin Sudan Ibrahim. Ya ƙware sosai wajen yaƙi kuma ga shi da fitina. Shi ne Turawa suka zo suka same shi yana sarautar Kwantagora, ya yi yaƙi da su, amma daga baya suka samu kama shi suka kai shi Yola. Sannan kuma a ƙarshe suka mayar da shi kan sarautarsa.

     Sarki Ibrahim shi ne wata rana Turawa suka rubuta masa wasiƙa suka ce ya kamata ya daina irin yaƙe-yaƙen nan da yake yi. Ya kuma zo ya bi su. Sai ya ce “Kuna iya kashe ni amma ba dai ku kama ni ba, kuma ko banza idan zan mutu, zan mutu da bawa guda runtse a bakina”. Allah bai nufe shi da cika wannan alƙawari da ya yi ba, domin a Zariya Turawa suka kama shi suka sa masa ankwa. Bayan sun tafi da shi ne ya yi masu alƙawali ba zai ƙara tada fitina ba, saboda haka aka mayar da shi kan sarauta.

     Labarin mayar da Sarkin Sudan Ibrahim kan gadon sarauta ta sa da Turawa suka yi nan da nan ya watsu ko’ina ƙasar Hausa, mutane suka yi ta murna. Sarki Ibrahim tattaɓakunnen Mujaddadi Shehu Usumanu Ɗan Fodiyo ne. duk kuwa zamanin da aka yi Kwantagora ba tare da sarki yana nan ba, to, Turawa da taimakon soja su ne suka riƙi garin. Saboda haka da dawowar sarki sai soja da Turawa suka janye jikinsu suka bar garin, suka je kamar mil biyar (5) suka kafa sansani, nan da nan garin ya soma cika, mutanen da suka gudu suka riƙa sulalowa suna komawa, suna ta aikin sake gina gidajensu. Kafin da a jima sai garin Kwantagora ya koma yadda ya kamata ya zama cike da mutane, kowa kuma yana ta harkar gabansa a cikin kwanciyar hankali da lumana.

     Ko da yake a lokacin duk hankula a tashe suke, duk da haka Turawa sun sa a ci gaba da sha’anin sa abubuwan da za su kyautata zaman ƙasar. A ƙarshen watan Yuli na (1903) ne waya ta iso Kwantagora. Kuma bayan ‘yan watanni kaɗan, da sabuwar shekara ta kama, cikin watan Fabrairu na (1904), Gwamna Lugga ya ziyarci Kwantagora. A wannan zuwan da ya yi ne, ya bai wa Sarkin Sudan Ibrahim takardar tabbatar da shi a sarauta. Sarki kuma ya yi alƙawalin zai yi biyayya da gaskiya. Har ma da gwamna Lugga ya tambayi sarki ko yana da wata magana, sai ya ce, “A’a, ba ni da abin da zan ce, sai dai ina roƙon gwamnati ta taimake ni wajen sa jama’a su bi duk irin umurnin da na ba su”. Mani, (2007:50-53)

    5.0 Ganɗoki

     Marubucin ya yi amfani da tauraronsa wato “Ganɗoki” yana bayar da labarin yaƙe-yaƙen da ya halarta. Ga abin da yake cewa:

    “Watarana ya tara yara yana zana masu yaƙoƙin da ya halarta duka. Ya ce musu da shi Shehu Usmanu Ɗan Hodiyo ya yi yaƙi a Alƙalawa, da Alwasa, da Tsuntsuwa da sauran irinsu. Tafiyar Sarkin Musulmi Bello Birnin Gwari da zamanin Shaihu da shi a tsakani. Dukkan jihadin da Fulani suka yi suka mallaki ƙasar Hausa da shi a ciki. Shi ne kanwa uwar gami cikin basasar Kano da yamutsin malam Halilu Bauci. Sa’ad da Umaru Nagwamatse ya fita yaƙe-yaƙensa har ya bi da Basawa da Kamukawa da Dakarkarawa, da Gwarawa da shi ciki. Komawar Ibrahim Sarkin Sudan na Kwantagora, Birnin Gwari zamanin Sarkin Gwari Barau da shi a ciki. Shi ne ma wanda ya kori sarkin Maraɗi da Hasau waɗanda Gwarawa suka gayyato” (Ganɗoki, 2001:1)

     Wannan labari da mawallafin littafin ya faɗa cewa Ganɗoki ya halarci yaƙe-yaƙe akwai ƙari a cikinsa, sai dai za a iya fahimtar haka a cikin tarihin marubucin.

     A littafin an bayyana cewa Ganɗoki ya tara yara yana gaya masu labarinsa sai suka ce suna son su ji yadda ya yi wannan gwagwarmayar yaƙe-yaƙe, sai shi (Ganɗoki) ya ce masu:

    “Daidai ne amma labarin nan kun rigaya kun karanta shi a cikin littattafai.

    Suka ce, duk da haka ba za a yi kamar naka ba” (Ganɗoki, 2001:2)

     A wannan bayani da Ganɗoki ya yi ya nuna cewa, labarin da yake tafe da shi gare su (wato yara) sun riga sun taɓa karanta shi a cikin littattafai. Wannan ya nuna cewa labarin da zai ba su ba wani abu ne baƙo a wurinsu ba.

    6.0 Yaƙin Bida

    Bida gari ne a cikin jihar Neja ta yau, kuma ta kasance tana daga cikin garuruwan da Turawa suka yaƙa a yunƙurinsu na kafa mulkin mallaka. Ko shakka babu labarin ya tabbata, kuma Malam Bello Kagara ya bayyana haka cikin littafinsa (Ganɗoki). A wannan littafi ya yi amfani da tauraronsa (Ganɗoki) ya ayyana shi ya fara bayar da labarin kuma ga abin da yake cewa:

    “Bayan jimawa kaɗan ina cikin Kwantagora, sai muka ji Turawa sun kama Bida da yaƙi, suka tarar Abubakar ke sarki” (Ganɗoki 2001:4)

     Wannan ya nuna Turawa sun taɓa faɗa garin Bida da yaƙi. Wannan lamari haka yake ko shakka babu Turawan Mulkin Mallaka sun taɓa shigowa a Arewacin Nijeriya domin kafa mulki irin nasu. Ba Ganɗoki kaɗai ya faɗi haka ba hatta ma da Mani (2007:48) ya bayyana haka a cikin littafinsa mai taken Zuwan Turawa Nijeriya Ta Arewa cewa Turawa sun taɓa kama Bida da yaƙi kuma suka yi nasara a kan Bida. Ya ƙara da cewa, a wannan zamani da aka yi karon batta lokacin Sarkin Bida Abubakar ne ke riƙe da ragamar mulkin garin.

     Ganɗoki ya ƙara da cewa:

    “Da suka sauka a Bida, suka tarad da zarumawa cunkus, da bindigogi masu yawa. Sai dai Maku ya tafi yaƙi ƙetare da waɗansu mazaje kaɗai ne ba su tarar ba”. (Ganɗoki, 2001:4)

     A wannan labari da marubucin littafin Ganɗoki ya faɗa yana da ƙamshin gaskiya, saboda Mani (2007:48) ya bayyana cewa, lokacin da Turawa suka yi yunƙurin kama Bida sai suka buƙaci Sarkin Bida Abubakar ya zo ya bi su, sai bai je ba. Su kuma suka naɗo wani sabon sarki mai suna Muhammadu Maku wanda Ganɗoki ya ce ba su iske shi ba ya je ƙetare da shi da wasu. Kuma ya bayyana cewa wannan shekarar 1900 sarki biyu ke ga Bida a wannan lokacin.

     Marubucin Ganɗoki ya bayyana cewa, Turawa sun shiga ƙasar Nufe. Wato yankin Nufawa. Ga abin da ya ce:

    “Sai Nufawa suka shiga sulke da buke suka tarbe su da yaƙi, shi kuwa sarkin Nufe Abubakar yana cikin gida, sai addu’a yake yi. Da ya gama ya shiga sulke, da ɗamara da tama’imu, ya yi cunkus ya fito ya hau sai ka ce giwa domin kwarjini da Allah ya ba shi”.

     Idan aka ce ƙasar Nufe wato yankin da Nufawa suke zaune, kuma wannan yankin ya haɗa da Bida. An bayyana cewa an yi ɗauki ba daɗi tsakanin Nufawa da Turawa masu yunƙurin kafa mulkin mallaka.

    7.0 An Kashe Wasu Daga Cikin Mayaƙan da Ganɗoki Ya Faɗa

     Da Turawa suka buƙaci Bida su ba da kai bori ya hau, sai Sarkin ya ƙi, sai ya haddasa yaƙi tsakaninsu. Wannan yaƙin da aka yi Turawa ne suka samu nasara a kan al’ummar Bida. Kuma da suka ci garin da yaƙi sai suka tabbatar da Muhammadu Maku a matsayin Sarkin Bida. Ga dai abin da Sarkin Yaƙi “Ganɗoki” ya faɗa game da abin da ya auku”

    “An kashe Saba da Basharu ɗan Aliyu Gandi, da sauran jama’a masu yawa. Bayan yaƙi ya ƙare, aka aiko sarki ya dawo, sai aka naɗa Muhammadu Maku.”

     Wannan ko shakka babu Turawa sun auka wa Bida, kuma bayan sun yi nasara a yaƙin Bida wato sun kashe na kashewa sun kama na kamawa wasu tuni sun bi tun da an kawar da mulkin Abubakar. Don haka suka tabbatar da mulkin da suka ba Muhammadu Maku, suka rantsar da shi a matsayin Sarki. Mani (2007:48)

    8.0 Yaƙin Kwantagora

     Wato bayan Turawa sun ci Bida da yaƙi sun karkata akalar yaƙinsu zuwa Kwantagora. Marubucin littafin “Ganɗoki” ya bayyana haka a cikin littafinsa inda yake cewa;

    “Turawa suka tashi daga Bida suka nufo Kwantagora “Tudu makwantar rikici” a nan sunka sauka Wushishi, Ganɗoki ya kashe Alƙali”. (Ganɗoki, 2001;6)

     A tarihin da Mani (2007) ya kawo ya bayyana cewa bayan da Turawa suka ci Bida sun garzayo zuwa Kwantagora, inda a nan ma sun yi yunƙurin kama Sarkin Sudan Ibrahim, amma ba su samu kama shi a nan Kwantagora ba. A cikin labarin da Manu (2007) ya bayar ya ce, “Shi Sarki Ibrahim shi ne wata rana Turawa suka rubuta masa wasiƙa suka ce ya kamata ya daina irin yaƙe-yaƙen nan da yake yi. Ya kuma zo ya bi su. Sai ya ce:

     “Kuna iya kashe ni, amma ba dai ku kama ni ba, kuma ko banza idan zan mutu, zan mutu da bawa guda runtse a bakina”. Ubangiji bai nufe shi da ciki wannan alƙawari da ya yi ba”.

    Wannan ya nuna ke nan shi ma Sarkin Sudan na Kwantagora sai da Turawa suka aiko masa wasiƙa kuma da ya yarda da ba a yaƙe sa ba. Amma irin amsar da ya bayar a wasiƙar ta sa aka yaƙe shi.

    9.0 Kwantagora ta Faɗa Hannu

     Wato dai bayan Sarkin Sudan ya ƙi aminta da kiran da Turawa suka yi masa, sai su kuma suka shiga farautarsa, wanda ya yi sanadiyyar kama garin nasa na Kwantagora. Ga dai abin da Sarkin Yaƙi Ganɗoki ya faɗa a cikin labarinsa:

    “....Bayan haka mutanen Wushishi da Ugu da Kagara suka haɗu da Sarki a dawan Wushiba. Gudun nan fa ya zama dole a gare mu.....”

     Wannan jawabi da marubucin “Ganɗoki” ya kawo ya yi daidai da abin da Mani (2007) ya faɗa cewa, “Sarkin Sudan Kwantagora gudu ya yi kar Turawa su rutsa da shi a garinsa a ji kunya.”

    10.0 Gudun Sarkin Sudan Ƙasar Birnin Gwari

     Bayan Sarkin Sudan ya samu labarin Turawa na tafe su kama shi sai ya shirya ya fita wato ya gudu don gudun jin kunya. A wannan gudun kuma an bayyana ya bi ta Birnin Gwari. Ga yadda lamarin yake a littafin Ganɗoki:

    “Ana cikin gudun nan an tasam ma Birnin Gwari. Ni sarkin yaƙi na tafi wurin sarki da kaina na ce, “Ranka ya daɗe ga mu korarru, ga Turawa biye da mu, ga mu kuma da Sarkin Gwari Barau......”

     A yunƙurin Sarkin Sudan na gudu daga garinsa ya bi ta Birnin Gwari yayin da Turawa suka bi bayansa da nufin su kama shi.

    11.0 Birnin Gwari ta Shiga Hannu

     Bayan da Turawa suka fahimci Sarkin Sudan ya gudu sai suka biyo baya suna so su kama shi. Shi kuma Sarkin Sudan shi da tawagarsa suka gudu suka bi ta Birnin Gwari Turawan suka bi su ta can, wanda sakamakon bin su can ne suka kama Birnin Gwari. Marubucin littafin Ganɗoki ya bayyana haka a cikin littafin yake cewa:

     “Ana cikin gudun nan an tasamma Birnin Gwari. Ni sarkin yaƙi na tafi wurin sarki da kaina na ce, “Ranka ya daɗe ga mu korarru, ga Turawa biye da mu, ga mu kuma da Sarkin Gwari Barau......”

    12.0 An Far ma Fatika

     Garin Fatika yana daga cikin garuruwan da marubucin Ganɗoki ya kawo a cikin labarinsa. Ya nuna cewa, garin ya fuskanci barazanar yaƙinsu (wato su tawagar Sarkin Sudan na Kwantagora). Ko da yake shi cewa ya yi sun yi wannan yaƙin ne don su samu abinci a hanyarsu ta gudu daga Turawa. Ga yadda abin yake a littafin:

    “.... aka kama garin da yaƙi muka tarad da Sarkin Filanin Fatika Muhammadu Tukunyar Gwari shi ke sarauta. Aka washe makwabtansu muka yamutsa ƙasar Zazzau”

     Ba a samu labarin da ya tabbatar da wannan magana a cikin littafin Ganɗoki ba, ta yiwu saboda mantuwa ko wani dalili na daban da marubucin littafin bai ambata ba.

    13.0 Yaƙin Zazzau

     Zazzau ta fuskanci barazanar yaƙi tsakaninta da ‘yan tawagar Sarkin Sudan, kuma wannan barazana ta bayyana a cikin labarin da sarkin yaƙi Ganɗoki ya bayar. Ga abin da yake cewa:

    “A nan ne hankalin Zage-zagi ya tashi, suka yi yunƙurin taimaka wa Fatika. A taƙaice wannan yaƙi da Zazzau ake yi.” (Ganɗoki, 2001:12)

     An tabbatar da sahihancin wannan labari domin Mani (2007:54-55) ya bayyana cewa, ko da Likita Miller ya zo daga Kano ya tarar mayaƙan Sarkin Sudan Kwantagora sun kewaye garin Zariya. Daga ganin haka sai Likita Miller ya aika wa Gwamna Luggard takarda cewa Sarkin Sudan Kwantagora ya kewaye garin Zariya yana son ya yaƙe su, ya kama garin. Shi kuwa Sarkin Sudan har da cewa ya yi idan ya samu nasarar cin Zariya da yaƙi zai fara sare kan Likita Miller. Da Luggard ya ji haka sai ya laɓaɓo da mayaƙansa ya kama Sarkin Sudan a nan Zariya.

    14.0 An Tafi da Sarkin Sudan a Yola.

     Da Turawa suka kama Sarkin Sudan na Kwantagora, sai suka tafi da shi Yola, daga can kuma suka yanke shawarar su mayar da shi ya ci gaba da mulkinsa. Ba mamaki ko da sun yi wani sharaɗi da shi. Amma dai ga abin da Ganɗoki ya faɗa a matsayin dalilan da ya sa suka mayar da shi:

    “Daga nan suka zarce da shi suka nufi Yola suka bi ruwa da shi. A wannan tafiya Turawa sun ga bidiri da abin mamaki da sihiri da tashin hankali ga Sarkin Sudan. Idan suka sa shi cikin ɗakin kwano suka rufe sai su gan shi a waje yana salla, ga ƙofar kuwa kulle kamar yadda take, ga ‘yan sanda da soja tsaye bisa aikinsu. Idan sun je kogi za su haye sai ya ƙi shiga jirgi, su su shiga su bar shi a nan sai su tarar da shi a wancan gacin zaune yana jiran su. Idan ya yi hushi sai ya fitar da harshensa ya naɗe shi a ka kamar rawani ko kuwa ya miƙe ƙafarsa guda ta tokare bangon ɗakin da yake ciki, in ya huce ya jawo ta ta koma daidai da ‘yar uwarta.” (Ganɗoki, 2001:14)

     A bayanin da muka samu a Littafin Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa kuwa an bayyana cewa an tafi da sarki, bayan sun tafi da shi ya yi masu alƙawalin ba zai ƙara tayar da fitina ba, sai suka dawo da shi suka mayar da shi a kan sarautarsa. Mani (2007:52).

    15.0 Yaƙin Turawa a Sakkwato

     Ba a nan kaɗai Turawa suka tsaya ba, sun kuma nufi Sakkwato da yaƙi yayin da suka tarar Sarkin Musulmi Attahiru ne sarki a wannan lokaci. Ga yadda lamarin ya gudana a cikin tarihin Ganɗoki.

    “Ina cikin haramar tafiya, sai na ji Sakkwato ta tashi, abin da ya gudana gare mu duka ya same su. Har sarkin Musulmi ya yo haramar tafiya hajji, sai na ga ba gindin zama gare mu a cikin wannan ƙasar. Na ce wa Inda Gana mu ba abin da ya fi sai mu bi rundunar nan ko hajji mu samu mu yi, domin mu ba mu da wata sana’a sai yaƙi, ga shi kuma ya yi tazgaro a wannan ƙasa.”

     Wannan ko shakka babu idan muka lura Ganɗoki yana magana ne a kan gudun da Sarkin Musulmi ya yi daga Sakkwato ya nufi Saudiyya (Makka) don gudun kar Turawa su iske shi.

     Wannan tarihi ya sake tabbatuwa idan aka yi la’akari da abin da Aminu ya faɗa a cikin aikinsa mai taken “Baƙin Dole. Ya bayyana cewaa shekarar 1885, Daular Musulunci da Shehu Mujaddadi ya kafa a Sakkwato ta fara samun ƙalubale daga Turawa. Aminu (2015:105).

     Daga cikin dalilan da ke ƙara tabbatar da faruwar waɗannan yaƙe-yaƙe akwai waƙar Nijeriya ta Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari in da yake cewa:

      Sai Lugard ya zo ya kammale,

       Suka bar shi da wagga ɗawainiya.

      Ya mai da ƙasa ta Sarauniya,

       Zamanin mulkin Victoria.

      Ya haddasa mulkin Ingila,

       Ya tabbata ba wata tankiya.

      Shi ya ci Kano da ƙasar Nufe,

       Har Borno da Bauchi da Zariya.

      Kwantagora garin su Nagwamatse,

       Da ƙasar Daura da Haɗejiya.

      Su Ilori da Yola ta Adama,

       Haka nan ya bi su biyan-biya,

      Dag kano sai ya nufi Sakkwato,

       Ya game mulkinsu gaba ɗaya.

      Babu sauran jayayya da shi,

       Da ma Kudu sun bi da gaskiya.

         (Shagari: Waƙar Nijeriya, 2007:4-5)

     Waɗannan baitoci da Alhaji Shehu Shagari ya kawo a cikin waƙarsa ta Nijeriya su ma suna ƙara tabbatar da faruwar wannan yaƙi tsakanin mutanen Arewacin Nijeriya da Turawan Ingila (Turawan Mulkin Mallaka). Kamar yadda littafin Ganɗoki ya tabbatar.

    16.0 Kammalawa

    Bisa waɗannan dalilai na tarihi da aka samu daga wajen masana daban-daban suna tabbatar da faruwar wasu yaƙe-yaƙe da Malam Bello Kagara ya kawo a cikin littafinsa na Ganɗoki. Wannan maƙala ta kalli yadda tarihin zuwan Turawa ya kasance, kamar dai soma yaɗa manufofinsu da saka wasu wakilansu a wasu garuruwa kamar Kwantagora, Wushishi, Zungeru, Fatika, Zariya, Kano, Sakkwato da sauran yankunan Arewacin Nijeriya. Haka kuma ficewar wasu sarakuna kamar Sarkin Musulmi Attahiru duk an danganta labarin da abin da marubucin littafin Ganɗoki ya faɗa a cikin labarinsa. Da wannan muna iya cewa, littattafan zube da aka gina su da salon labari, suna iya kasancewa labaran gaskiya, kuma suna iya kasancewa labaran da aka yiwa ƙari. An yin nazarin abin da ke cikin littafin Ganɗoki wanda Malam Bello Kagara ya rubuta, kuma an tsamo labarin gaskiya cikinsa.

    MANAZARTA

    Aminu, N. (2015) “Baƙin Dole: Nason Al’adun Turawa ga Al’adun Hausawa a  Lardin  Sakkwato da Gwandu da Argungu 1903-2010”. Kundin Digiri na  Uku a Jami’ar  Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

    Bello K. (1933) Ganɗoki. Zariya: NNPC

    Ibrahim Y.Y. (2002) Tarihin Rubuce-Rubuce A Cikin Hausa. Zariya NNPC.

    Ƙaura, H. L. (2014) Maƙwabtan Hausawa A Cikin Rubutattun Ƙagaggun

      Labara Gasar Farko Ta (1933)

    Mukhtar, I, (2002), Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labari, (Tsari Na Biyu),Kano: A.J  Publishes

    Malumfashi, I. (2009), Adabin Abubakar Imam Sokoto: Garkuwa Media Services,  Ltd,.

    Mani, A. (2007), Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa. Zariya: NNPCTop of Form

    Shagari, A. U (2007) Waƙar Nijeriya. Zariya: NNPCBottom of Form

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.