Gudummuwar Mata Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Kasar Hausa

    Citation: Haruna Umar Maikwari da Muhammad Sani Lawan ( 2021). Gudummuwar Mata Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa. Maƙalar da aka buga a Proceeding on Women and Their Contribution to Hausa Society. Shafi 229-238

    Gudummuwar Mata Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Da

    Muhammad Sani Lawan

    Department of Hausa Language.
    Sule Lamiɗo University Kafin-Hausa, Jigawa State
    msanilawan@gmail.Com
    (+234) 08063161900

    Tsakure

    Mata sun kasance manyan mataimaka ga kowane al’amari na tafiyar da rayuwa kama daga zamantakewa, tarbiyya, tattalin arziki da makamantansu. Wannan maƙala za ta mayar da hankali ne wajen duba irin gudummuwar da mata suke bayarwa ta fuskar bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Manufar wannan maƙala ita ce; (i) Bayyana sana’o’i da kasuwanci da mata ke yi daga cikin gida da wajen gida har ma da wasu ƙasashe da ba na Hausa ba. (ii) Fito da muhimmancin waɗannan sana’o’in da kasuwancin da matan suka tsunduma domin taimaka wa al’umma. (iii) Bayyana ta yadda waɗannan sana’o’i da kasuwanci suka taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar Hausa. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙalar ita ce, ta karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da maƙalun da aka buga a wasu mujallu na ilimi daga jami’o’i daban-daban.Sakamakon binciken da wannan maƙalar ta fitar shi ne, an gano cewa mata suna yin kasuwanci da sana’o’i a cikin gidaje da ma wajen gida, kai wasu ma har sukan fita wajen garin da suke har wani gari, wasu kuma har wata ƙasa ba ma ƙasar Hausa ba. Wannan kasuwanci na saye da sayarwa yana da muhimmanci, haka sana’a wato sarrafa wani abu kamar dai saƙa, ɗinki, abinci, kayan sanyi, koda da makamantansu duk waɗannan sana’o’in da mata ke yi a cikin gida da waje ba ƙaramar gudummuwa suke bayarwa ga haɓakar tattalin arzikin ƙasar Hausa ba.

    1.0 Gabatarwa.

    Hausawa kamar sauran al’ummu na duniya suna da al’adu da suke gudanar da rayuwarsu a kan su, hasali ma da waɗannan al’adun ne ake iya gane su. Idan kuma aka yi maganar al’adun Hausawa, to wajibi ne a taɓo sana’o’in Hausawa na gargajiya. Sana’o’in Hausawa na gargajiya sun ƙunshi, noma, da kiyo, da ƙira, da saƙa, da sassaƙa, da jima, da rini, da dukanci, da koda, da dako, da su/sarkanci, da wanzanci, da kaɗi da dai sauransu. Ko a duniyar yau, sana’a tana daga cikin manyan hanyoyin da ake bunƙasa tattalin arziki na kowace al’ummar duniya. Tun fil azal Bahaushen mutum yana da hikimomi da fasahohin samar wa kansa abubuwan gudanar da rayuwa a cikin sauƙi. Waɗannan abubuwa da yake samarwa yana samar da su ta fuskar sana’o’i, da kasuwanci, da fatauci, da aikatau, kuma su ne suka ƙara inganci ga tafiyar da tattalin arzikinsa. Bugu da ƙari Hausawa ba raggaye ba ne, ba su lamunci zaman banza ba, suna zuwa biɗar duk wani abu da zai inganta sana’arsu, kuma sukan yi tanadin duk wani abu da za su iya buƙata a gaba. Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen duba irin gudummuwar da mata suke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Mata sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar Hausa. Sana’o’in Hausawa ƙashin baya ne na ci gaban tattalin arzikin ƙasar Hausa, duk da cewa sana’o’in na gargajiya yanzu sun samu sauyi. Wannan sauyin bai hana samun gagarumar gudummuwa ga tattalin arziki ba. Buƙatar wannan maƙala ita ce, ta bayyana irin gudummuwar da mata suka bayar wajen buƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa.

    1.1 Manufar Bincike

    Babban manufar wannan bincike ita ce bayyana irin gagarumar gudummuwa da mata ke bayarwa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar Hausa. Kai tsaye maƙalar za ta mayar da hankali kan:

    i.                    Bayyana sana’o’i da kasuwanci da mata ke yi daga cikin gida da wajen gida har ma da wasu ƙasashe da ba na Hausa ba.

    ii.                  Fito da muhimmancin waɗannan sana’o’in da kasuwancin da matan suka tsunduma domin taimaka wa al’umma.

    iii.               Bayyana ta yadda waɗannan sana’o’i da kasuwanci suka taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar Hausa.

    1.2 Hanyoyin Gudanar da Bincike

    Wannan maƙalar ta kammala ne ta hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da muƙalu da masana da manazarta suka gabatar. An zaɓi a bi wannan hanya ne domin masana da manazarta sun gabatar da bincike a kan sana’o’i da kasuwanci. Kuma waɗannan sana’o’i da kasuwanci ba maza kaɗai ne ke aiwatar da su ba har da mata. Bin wannan hanya shi zai ba da damar:

    i.                    Gano waɗannan sana’o’i ne ko kasuwanci da mata suke yi, tare da warware manufar wannan maƙala.

    ii.                  Sanin irin muhimmancin da ke tattare ga sana’o’in da kasuwancin na mata, da yadda suke taimaka wa al’umm.

    iii.               Fito da bayanai da za su tabbatar da irin gudummuwar da mata suka bayar wajen bunƙasa tattalin arziki.

    2.0 Ma’anar Sana’a

    Sana’a ita ce samuwar hanya ta neman abinci da ɗan Adam zai yi domin neman halaliyarsa. Sana’a kan iya zama ta aikin ƙarfi, wato neman halaliya ta yin aikin mai wahala kamar su noma, gini, ƙira, jima, kaɗi, ɗinki da sauran su. Takan iya zama ta hanyar jiya, wato biyar ta koma goma wato a saye a sayar. Duk abin da mutum zai yi ya samu wani abin da zai gudanar da rayuwarsa da ta iyalinsa kuma jama’a suka san shi da ita wannan shi ake kira sana’a.

    Sana’a dai ita ce saye da sayarwa ko aikata wani aikin da zai samar wa mutum riba da zai iya ya kore wa bakinsa ƙuda. Idan mutum ya samu wata hanya ta samun kuɗi ko samun abinci ko biyan wasu buƙatu kuma jama’ar da ke kusa da shi suka sani cewa wannan abu da wane yake yi yana samar masa da abin da zai iya yin lalurorinsa wannan shi ne sana’a.

    Sana’a hanya ce ta sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomi da Allah ya yi wa ɗan’Adam kamar amfanin gona da dabbobi da tsirrai da kuma wasu albarkatu waɗanda suke ƙarƙashin ƙasa, ya Allah dutse ko kuma ruwa domin samun abin masarufi. Haka nan kuma za mu iya cewa sana’a hanya ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da sarrafa su ta hanyoyin kimiyya da ni’imomi da suke tattare da ɗan’Adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa. Sana’a ita ce mafi girman matsayi da Hausawa suke amfani da sunan don dogaro da kai. Sana’a na iya kasancewa wata abu ce wadda mutum yake koyo ya iya, wadda kuma sai da ita ce mutum yake iya zaman duniya mai amfani.

    2.1 Nau’o’in Sana’a

    Nau’o’in sana’a wani abu ne mai mahimmanci domin yakan fitar da irin ressan da sana’a take ɗauke da su. Bisa ga irin abubuwan da ake amfani da su a lokacin da ake aiwatar da ita, muna iya cewa, sana’a tana da ressa masu tarin yawa da suka haɗa da: Noma, ƙira, Jima, kaɗi, ɗinki, saƙa, sassaƙa, fawa, sarkanci, wanzanci, da dai sauransu. Ba za a iya cewa ga iya adadin nau’o’in sana’a ba. Wasu suna saye da sayarwa, wasu bankwai suke yi wasu tireda, wasu dako, wasu lodi da saukale, wasu lebaranci sukai wasu kanikanci suke yi kai abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa.

    2.2 Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Mata

    Akwai sana’o’i da dama da suka shafi jinsin mata waɗanda mata ne kawai ke yinsu ba da maza ba. Wasu kuma idan ka ga maza na yinsu to lallai sai dai ‘yan daudu ko kuma wasu ɗai-ɗaiku. Waɗannan sana’o’in sun haɗa da: Sana’ar Kitso, Sana’ar Koda, Sana’ar Dafe-Dafe, Sana’ar Dawo da dai makamantansu. Yanzu bari mu ɗauki ɗaya daga ciki mu ɗan yi tsokaci saboda mu kafa hujja.

    2.2.1 Sana’ar Kitso

    Wannan sana’a ce da mata ke yi suna samun wani abu. Sukan tanadi wasu kayan aikin sana’ar su kamar mashaci, da tsinke wanda suke yi tsagar gashi da shi yayin da suke yin kitso.(Tcinke). Matar da take buƙatar a yi mata kitso takan kwance/banye gashin kanta ta wanke ta saka mai irin wanda ta fi son ta yi buƙata da shi sai ta sa a kanta sai ta nufi inda wadda take yin kitso take domin a yi mata wannan kitson irin wanda take buƙata, wasu suka ce a yi masu zanen yawo, wasu kuma sukan yi wibin ko kalaba ko shuku ko kwando, ko dai wani nau’in na daban.

    2.3 Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Maza

    Kamar dai abin da muka ambata cewa, akwai sana’o’in da suka shafi jinsin mata to, haka kuma akwai wasu sana’o’in jinsin maza ne suka fi aiwatar da su. Ba wai lallai sai maza ne kawai keyinsu ba, amma mafi yawan sana’o’in maza ne suka fi yinsu. Irin waɗannan sana’o’i sun haɗa da: Ƙira, Rini, Jima, Farauta, Noma, Dukanci, Tauri, Dambe, Kokawa, Wanzanci, Sarkanci, Ƙwadago, Sassaƙa, Sodori, Bashirwanci, da dai makamantansu.

    Dukkan waɗannan sana’o’i maza ne suka fi yinsu, mata ba su cika yinsu ba. Domin samun kafa hujja bari mu ɗan yi bayani taƙaitacce a kan sana’a ɗaya daga cikin waɗannan.

    2.3.1 Sana’ar Fawa

    Sana’ar Fawa dai sana’a ce ta mahauta, wadda mafi yawan masu yin ta sun gada ne, waɗansu kuma ba su gada ba. (Calvic Y. Garba 1991)

    Sana’ar fawa wata sana’a ce ta Hausawa, ta gargajiya wadda ake sayen dabba a yanka ta a sayar da namanta, domin miya ko wata buƙata. Ana sarrafa naman ne ta yin balangu, ko a soya ko a yi kilishi ko a dafa ko a yi tsirai ko langaɓu ga jama’a masu buƙata.

    Don haka fawa sana’a ce ta rundanci, wadda ake yanka dabba don a sayar da namanta ga jama’a, haka kuma sana’ar fawa ta ƙunshi tun daga kawo dabbab zuwa mahauta, kayar da ita, yankawa da feɗewa da rarrabawar ƙashi da tsoka da sayar da naman ɗanye ko balangu don sayarwa tare da zimmar cin riba.

    2.4 Sana’o’in Da Aka Yi Tarayya Tsakanin Maza Da Mata.

    Su waɗannan sana’o’i dai kamar yadda aka ce na tarayya ne to dukkan jinsin biyu suna iya yinsu, kuma ba ya zama wani abu. A al’adar Hausawa wasu sana’o’i da suke na mata ne idan aka ga namiji ya shiga yinsu, to sai a kama kallonsa da wani abu daban marar kyau, saboda a ganin su ya saɓawa al’adun su. A wasu lokuta kuma har da tsarguwa tana shiga a ciki har ta kai a la’anci mai yin sana’ar ba don sana’ar ba ta yiwuwa ba. Haka abin yake ga sana’o’in da suke na maza ne idan mace ta shiga dumu-dumu a ciki sai ka ga mutane suna kyamarta ko ma su la’ance ta.

    Duk da cewa sana’a da ake yi tana da gurbin da ya dace ta faɗa dangane da jinsin al’umma. Wato kamar sana’o’in da suka danganci jinsin maza da kuma waɗanda suka danganci jinsin mata. Akwai kuma wasu sana’o’in da suke an yi tarayya a wajen yinsu wato maza na yi kuma mata na yi. Irin waɗannan sana’o’in sun haɗa da: Malanta, Kaɗi, Ɗinki, Saƙa, Kiyo, Dillanci da dai sauransu. Domin mu samun ɗaure akuyarmu a kan magarya za mu ɗauki ɗaya daga cikin waɗannan mu ɗan yi tsokaci a kai.

    2.4.1 Ma’anar Sana’ar Tela.

    Wasu daga cikin masana adabin Hausa sun yi tsokaci dangane da ma’anar sana’ar tela. Alhassan da wasu (1982) ya bayyana ma’anar sana’ar tela a cikin littafinsu mai suna “Zaman Hausawa” cewa suka yi, “Haɗa sawaye da wani abu saƙaƙƙe a mayar da shi tufa ko wani abin sawa a jiki da taimakon zare da allura shi ne ɗinki”. A zamanin yanzune muke kira da suna tela.

    3.5 Muhimmanci Sana’a Ga Al’umma.

    Sana’a kamar yadda aka sani tana da matuƙar muhimmanci ga al’umma amma yanzu bari mu kawo wasu bayanai da za su tabbatar da haka:

               i.Sana’a tana samar da aikin yi ga al’umma. Idan kana da sana’a to lallai ya zama wajibi kai ka ƙaru su kuma al’ummar da suka saya su samu biyan buƙatarsu.

             ii.Sana’a tana rage sace-sace ga al’umma.

          iii.Sana’a tana rage zaman Banza ga al’umma.

          iv.Sana’a tana rage dogaro ga gwamnati, da wasu ‘yan siyasa.

             v.Sana’a tana tare da albaka saboda annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa, albarka tana cikin sana’a.

          vi.Sana’a tana samar wa mai ita kuɗi da suna da girma.

    Idan muka yi la’akari da waɗannan muhimman abubuwa da muka zayyana za mu ga cewa, suna daga cikin muhimman abubuwan da rayuwa ta ƙunsa. Kuma dukkansu sana’a ce take samar da su.

    4.0 Kasuwanci

    A saya a sayar shi ne kasuwanci. Wato a nan mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi kadara sannan wani lokaci ya fitar da wannan kadarar ya sayar shi ne kasuwanci. Mai irin wannan harka shi ake kira ɗan kasuwa in mace ce akan kira ta da ‘yar kasuwa. Kasuwanci ba ya yiwuwa sai da jari. Jari shi ne ake amfani da shi wajen sayen kadarar da za sayar. Ɗan kasuwa dole ne ya riƙe jari domin ya riƙa jujjuya shi. Zarruk (1982:38). “Kasuwanci wata harka ce mai saurin samun kuɗi ko rasa su.(Madabo, 1979:23).

    A wannan zamani kasuwanci da sana’a suna da makusanciyar alaƙa, sai dai sana’a an fi ta’allaƙa ta ga abin da ya shafi sarrafa wani abu domin sayar da shi. Shi kuma kasuwanci an fi kallonsa ta fannin amfani da jari a saye wani abu a sayar.

    5.0 Mene ne Tattalin Arziki?

    Kalmomi guda biyu ne suka tayar da kalmar tattalin arziki, watau, “tattali” da “arziki (Mika’il, 2015: 3). A ra’ayin Auta (2006:194) kalmar “tattali” kalma ce mai nuna rainon wani abu har ya kai ga ya girma. “Arziki” a wannan wurin yana nufin samun “dukiya” ko wani abin mallaka. Haka kuma a wata ma’anar an bayyana “tattali” da tanadi ko kula ko ririta ko adana wani abu ko ajiye wani abu don yin amfani da shi nan gaba. Ita kuwa kalmar “arziki” na nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko kuɗi ko wadata ko sukuni ko daula ko abin hannu ko hannu-da-shuni (C.N.H.N, 2006:432;19).

    Idan muka lura da ma’anonin waɗannan kalmomi za mu fahimci cewa, in aka haɗa su za su gina kalmar “Tattalin Arziki”, wadda ita kuma wannan kalmar ta “tattalin arziki tana nufin “kula da abin da aka mallaka ko rainonsa ko ririta shi da ba shi kyakkyawar kulawa domin bunƙasa da cin gajiyar da ake samu tattare da wannan abin. Su kuwa masana da manazarta sun kalli wannan kalmar kamar haka:

    Ibrahim, (1981:5) ya bayyana ma’anar “tattalin arziki da cewa, “Tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗanAdam domin samar da muhimman abubuwan buƙatu da rarraba su ga jama’a masu buƙata”. Umar (1983:5) shi ma cewa ya yi, “Tattalin Arziki tsari ne na sarrafa wasu abubuwa domin samun abubuwan rayuwa”.

    A fagen nazari kuwa, tattalin arziki tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya hore wa mutum, domin samar da muhimman abubuwan da ɗan Adam yake buƙata a kuma rarraba su ga jama’a. Don haka wajibi ne ga ɗan Adam ya yi huɓɓasa ta yadda zai sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan waɗannan buƙatu. Sai dai mutum ƙashin kansa, ba zai iya wadatar da kansa da dukkan abubuwan da yake buƙata ba, don haka tilas ya dogara ga ‘yan uwansa wajen samun waɗannan buƙatu kamar yadda suma suke dogara da shi (Umar, 1983).

    Ana buƙasa tattalin arziki ta hanyar amfani da wasu dabaru wato “biɗa” da “tanadi”. Waɗannan hanyoyi sun kasance fitattu kuma masu taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar Hausa.

    5.1 Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa

    Al’ummar Hausawa sun kasance masu ƙoƙari da jajircewa wajen neman na kai, al’adar Hausawa ba ta yarda da zaman banza ba, wannan ya taimaka mata wajen ƙoƙarin dagewa da juriya da nacewa ga dukkan sana’ar da suka samu wadda za ta zama abin dogaro garesu. Za a fahimci cewa, idan Bahaushe ya samu sana’a tana zama ita ce dukkan zuriya za su mayar da hankali wajen yi. Don haka ita wannan sana’a za ta zame masu ta gado. Wato kowa a cikin zuri’ar zai gada ya samu abin dogaro. Sallau (2014:14) ya kalli tattalin arzikin ƙasar Hausa ta fuska biyu in da ya ce, “Tattalin arzikin ƙasar Hausa a yau yana da fuskoki guda biyu, wato “noma” da kuma “kiwo”. Sallau ya ƙara da cewa, “kamar kowace ƙasa, ƙasar Hausa tana da hanyoyi da suke taimaka wa tattalin arziki ya bunƙasa. Idan aka dubi waɗannan tattalin arziki za a ga cewa, akwai waɗanda aka gada tun daga iyaye da kakanni kamar noma, da kiwo, da fatauci, da sauran sana’o’in gargajiya.

    Sana’o’i su ne mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi domin samun abubuwan buƙata. Ta hanyar sana’a suke sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomi domin biyan buƙatunsu, kuma rarar abin da suka samu suke musanyawa su mallaki abubuwan da ba za su iya samar wa kansu ba. (Yakasai, 2012:35).

    Tsarin zaman Hausawa na gargajiya ya amince da zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Wato kowa da irin gudummuwar da yake bayarwa dangane da ci gaban rayuwa na yau da kullum. (Umar, 1987:14).

    Abdulƙadir, (2011:479) ya bayyana tattalin arzikin Hausawa na gargajiya da cewa, “abu ne da yake a tsare, ta yadda kowa yana bayar da gudummuwa gwarwagon ikonsa, kuma yana samun abubuwa gwargwadon ƙwazonsa da kuma sana’asa. Ita kuma hukuma tana sa idon don tsaron mutunci da dukiyar al’umma.

    Bisa ga bayanai da suka gabata idan aka lura za a ga cewa, kowa ya mayar da hankalinsa ga abin da ya shafi sana’o’i. Idan haka ne to sai mu lura cewa, sana’o’in nan su ne suka gina tattalin arziki. Shi kuwa tattalin arziki shi yake kawo walwala ga al’ummar da suka yi tsari mai kyau na bunƙasa tattalin arzikinsu.

    6.0 Sana’o’in Mata

    Duk da cewa wannan jinsi yana da rauni kuma al’ada ta ba jinsin damar ya zauna a kawo masa, amma saboda ƙarfin hali da zaman cuɗanni-in-cuɗe ka, wannan jinsi bai yarda ya zauna a yi masa komai ba. Don haka jinsin matan suka ƙallafa wa kansu shiga cikin harkokin biɗa na kare mutuncin kai da taimakon maigida da ‘ya’ya da gudanar da harkokin gabansu na bukukuwa da dai makamantansu. Mata kan biɗi jari komai ƙanƙantarsa ko wata sana’a ta hannu su riƙe suna gudanar da ita ana samun riba suna tara wa. Daga cikin sana’o’insu da suke yi akwai sana’ar tela, ko sana’ar sayar da ruwa, ko sana’ar ƙuli, ko sana’ar sayar da kayan miya, ko sana’ar sayar da kayan gyaran jiki, ko sayar da lalle, ko sana’ar kitso, ko yin lallen zamani, ko sayar da kayan sanyi da ake sakawa a firiza kamar ƙanƙara, da, kunun aya, da soɓo, da kunun zaƙi da dai makamantansu. Idan mace ta kasance tana yin sana’a makamantan waɗannan sana’o’i to ana iya kiranta da “mace mai biɗar na kai”. A nan kena sana’a ta koma biɗa.

    Akwai kuma wasu sana’o’i da suka a ƙasar Hausa. Waɗannan sana’o’i bincike ya nuna mata suna bayar da gagarumar gudummuwa a cikin waɗannan sana’o’i da kasuwanci. Sana’o’in da suka tsira a ƙasar Hausa a yau suna da yawa. Kuma sun samu ne a sakamakon zamani da sauyawarsa. A yau, biyan buƙatun al’umma yana daga cikin muhimmin abin da suka sa ma gaba. Kuma yau in ba ka da abin yi to wajibinka ne ka gani ga wani. Buƙatar abin yi ya sa al’ummar Hausawa suka shiga neman harkar yi har suka samu wasu sana’o’i suka riƙa yi domin su samu abin kore wa bakinsu ƙuda. Hausawa sun yi la’akari da abubuwan da suke cuɗanya da su a yau, kuma sun lura da cewa buƙatar waɗannan abubuwa na cikin ran wasu don haka suka riƙi wasu hanyoyi na koyon sana’o’in domin samun abin yi.

    Galibin sana’o’in da suka tsira ba gadonsu ake yi ba. Sai dai ana koyonsu kuma a iya. Da zamani ya zo yanzu har da wasu cibiyoyi aka buɗa domin koyon sana’o’in zamani. La’akari da irin ci gaban da aka samu ya sa Hausawa suke ganin samun wata sana’a da ta jiɓinci buƙatun al’umma yana da alfanu, don haka suka ɗauki sana’o’i daga cikin sana’o’in da suka tsira suka yi ta aiwatarwa suna samun amfani. Daga cikin sana’o’in da suka tsira akwai:

    ·                     Ci-maka

    ·                     Kwalliyar Hannu

    ·                     Magungunan Mata

    ·                     Aikatau

    ·                     Ɗinkunan Zamani

    ·                     Lalle

    ·                     Yanka salatib

    ·                     Ƙwalama

    ·                     Hakin maye

    ·                     Saƙar zamani

    ·                     Ƙulla suɓo

    ·                     Kunun aya

    ·                     Masu sayar da masa/waina

    ·                     Tuwo-tuwo

    ·                     Sayar da ruwan leda/pure water

    ·                     Tireda

    ·                     Hayar baro

    ·                     Kabu-kabu

    ·                     Hayar littattafain karatu na adabin kasuwar Kano

    ·                     Hayar kasusuwan kallo

    ·                     Sayar da sutura atamfa leshi da sauransu

    ·                     Sayar da katin waya

    ·                     Koyon sana’ar hannu ta zamani da ta haɗa da sabulu/man shafi

    ·                     Man wanke-wanke/ car wash

    ·                     Girke-girke

    ·                     Soye-soye

    Ba waɗannan kaɗai ba ne domin ɗan binciken da na gudanar na maƙala ne kuma zai yi wuya in iya tantance adadin yawan sana’o’in. Amma dai na san da waɗannan sana’o’in sababbi ne.

    A wasu jihohi da aka ci gaba har da cibiyoyi aka buɗe na koyon sana’o’i in da mutum zai je ya koyi wani abun amfanin al’umma kamar dai yadda ake girki, yadda ake ɗinkin zamani, da yadda ake yin man shafi, da yadda ake yin sabulun wanki, da yadda ake yin man wanke-wanke, da yadda ake yin soye-soye, da yadda ake yin wasu sana’o’in da suke da kusanci ga buƙatun al’umma.

    7.0 Gudummuwar Mata Wajen Haɓaka Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa

    Babu shakka idan aka dubi irin yadda mata suka shiga harkokin sana’o’i da kasuwanci za a ga cewa, an samu wasu sana’o’i da suka zo da zamani, haka kuma kasuwanci da aka sani na gargajiya yanzu an samu wasu hanyoyi na zamani. Mafi yawan sana’o’i da mata ke yi a yau da ma kasuwanci duk suna amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen saye da kuma tallata sana’o’insu da kasuwancinsu. Tattalin arzikin ƙasa kuwa ba ya samuwa sai in akwai zaman lafiya, aikin yi, wani abin dogaro, ababen buƙata na rayuwa, wadatar abinci kyakkyawan shugabanci da makamantansu. Waɗannan sana’o’i da kasuwanci sun taimaka wajen:

            i.Samar da ababen amfanin al’umma

          ii.Hana zaman banza

       iii.Rage raɗaɗin talauci

       iv.Yawaitar abubuwan amfanin al’umma

          v.Samun abin buƙata kusa da mutum ba sai an je nesa an wahala ba

       vi.Rage wa gwamnati yawan marasa aikin yi

     vii.Rashin dogaro ga abin wani

    viii.Magance matsalar rashin aikin yi

        ix.Kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali

    8.0 Kammalawa

    Wannan maƙala ta bayyana irin gudummuwar da mata suka bayar wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar Hausa. Ko shakka babu mata suna da rawar da suke takawa wajen ci gaban ƙasar Hausa. Akwai wasu sana’o’i da suka keɓanta ga mata kawai a al’adance duk kuwa da cewa zamani ya zo da yadda za a samu namiji ya shiga wannan sana’a. Wannan kuma ba zai yi wani tasiri ba musamman a wasu sassa na ƙasar Hausa da yake mata kawai aka sani da waɗannan sana’o’i kamar da kitso, koda, da makamantansu. Abin da ya shafi kasuwanci kuma, mata suna yi, wannan lamari ne na saye da sayarwa. Don haka mata suna da rawar da suke takawa wajen wannan kasuwanci musamman abin da ya shafi kayan sutura, ko kayan ado na mata da na yara, haka kayan abinci da na miya da na magungunnan mata da makamantansu. Duk wannan sana’o’i da kasuwanci da mata kan yi sun kasance wasu manyan ginshiƙai na haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

     Manazarta

    Abdulƙadir D. (2011) “Gyara Kayanka: Tasirin Al’adun Hausawa ga Ci Gaban Ƙasa” a cikin Studies In Hausa language, Literature and Culture. Kano: Jami’ar Bayero.

    Alhassan H. Da Wasu (1991), Zaman Hausawa, Islamic Publishes Bereau Lagos.

    Bunza A.M (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nig. Lmt Lagos

    CNHN (2006), Cibiyar Nazarin Al’adun Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

    Funtua da Gusau (2010), Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani El-Abbas Printers and Concepts Kaduna

    Faruk A (2017) “Nazarin Biɗau a Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa” Kundin MA Hausa Studies UDUS.

    Hassana (2003) “Sana’ar Fawa a garin Gusau” Kundin Bincike  na kammala karatun NCE a Kwalejin Ilmi da Ƙere-Ƙere ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Gusau Jihar Zamfara.

    Ibrahim M.S (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a Kan Rayuwar Hausawa” Kundin Digiri na Biyu. Kano: jami’ar  Bayero

    Madabo M.H (1979) Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa Annuri Printers and Publication D/Rimi.

    Sallau B.A (2010) Wanzanci da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. M.A. najiu Professional Printers. Sokoto.

    Yakasai, S.A (2012) Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services Limited. Sokoto.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.