TAMBAYA ❓
Dan
Allah tambaya nake akan sallar kasaru
Yar
garin kano ce ni
Tambayar shine yanxu idan naje garinda kasaru tah kamani kamar dustan jigawa sai laasar tah riskeni a garin amma banyi bah sai bayan nah dawo Kano
Toh xanyi raka biu ne koh hudin xanyi
AMSA❗
BISMILLAH
WASSALATU WASSALAMU ALA RASULlLLAH
An
yiwa samahatush sheikh bn baz (rimahullah) irin wannan tambayar A cikin
[fataawa nurun alad darbi]
Sai
ya bada amsa da cewa shi matafiyi idan ya riski ahlin sa (wato yayin da ya koma gidan
sa) zai biya abin da yake kansa na sallar da biyiba a halin tafiya to zai yita
ne cikakkiya (wato raka,a hudu) ba zaiyi qasru ba, ka dai dai zaiyi qasru ne a
halin kasancewar sa a cikin tafiya, to amma idan ya jirkinta sallar la,asar ko
azahar ko sallar isha,i har sanda ya koma gida to haqiqa shi zai sallace ta
raka,a hudu ne, domin tafiyar ta gushe kuma saukin ma ya gushe.
Allah
shi ne mafi sani
Amsawa
(abu abdullah)
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ
ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
[8:46
pm, 24/07/2024] +234 703 538 7476: SANARWA❗
Assalamu
alaikum, warahmatullahi, wabarakatuhu
Biyo
bayan amsar da na fitar kwanaki 10 da suka gabata gameda bincikawa wata baiwar
Allah Rajalis Salih wato Miji Nagari, an samu yan uwa da dama daga cikin wannan
group mai albarka da suka turo buqatu makamanta wannan Kuma ana sa ran za'a
dace domin kuwa an tsara program dinne bisa tsari mai kyau
Alhamdulillah,
sakamakon hakan, akan gaba, an samu dan uwa shugaban "DBK MARRIAGE &
ORPHANS FOUNDATION", wanda aikinsu shine qulla alaqar aure don raya sunnah
tsakanin maza da mata wadanda suka fahimci juna, tun tsawon sama da shekaru 3
ba su da wani aiki sama da wannan
A
tsawon shekarun nan an samu nasarar aurar da yan mata da Zaurawa sama da goma
sha [Wadanda muka Sani kenan]. A hakan ma Allah ne kadai yasan wadanda suka
daidaita har Kuma suka yi auren. Alhamdulillah. Wannan Nasara ce babba haka
Kuma dama ce ga duk wanda yake neman abokin zaman aure.
Allah
Subhanahu wata'ala yace
(
الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ
وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ ۖ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ
لِلطَّيِّبَاتِ ۚ
النور (26)
An-Noor
Miyãgun
mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma
tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan
mãtã suke.
Bayan
tattaro bayanai da Kuma jin tsare tsaren na ga dacewar a bude kofar SANARWA ga
duk wanda yake buqatar neman abokin zama, Wanda kuma ana sa ran ya zamo nagari
laakari da kusan duk Wanda ka gan shi a wannan group to dalilin gyara addinin
sa ne ya shigo domin kuwa wasu basu damu da neman ilimi ba ballantana Kuma aiki
dashi. Kwanakin baya wata mata tacemin Allah ya biyamu da Aljannah domin kuwa
suna daga gidajensu amman suna amfanar ilimin da ko masu zuwa Makaranta sai
Haka
A
karshe duk Wanda yake da raayin shiga sannan kuma ya shirya aure [ba soyayya
ba] bisa wannan tsarin zai cike wadannan bayanai kamar Haka
Send
your details using this format
1.First
Name
2.Gender
3.Tribe
4.Location
5.State
of Origin
6.Age
7.Blood
Group
8.Genotype
9.Health
status:
10.Marital
status:
11.
No. of kids
12.Height:
13.
Body size
14.Complexion:
15.Educational
Status
16.Occupation:
17.Religious
ideology- Muslim
/Aƙida
18.Interested
in
19.
Pictures
Sannan
kuma inda baa gane ba sai ayi tambaya
Muna
roqon Allah ya duba manufarmu ya shiga al'amarin. Sannan Nima a matsayina na
wanda lokacin sa bai zo ba, a tayani da adduar samun mace tagari: MAR'ATUS
SALIHA wadda zamu Sha ZANJABEEL daga tafkin SALSABEEL da yake a cikin ALJANNAH
(
وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا
كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا )
الإنسان (17)
Al-Insaan
Ana
shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance
zanjabil ne.
(
عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ
سَلْسَبِيلًا )
الإنسان (18)
Al-Insaan
Wani
marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka
Sanarwa
Usman
Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.