TAMBAYA ❓
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatuhu
Barka da safiya Malam Allah ya qara rufa asiri ya biya mana buqatunmu na Alkhairi ya Saka maku da alkhairi bakidaya🙏🏻
Tambayata itace Dan Allah yaakeyiwa yaron da aka Haifa huduba da Saka suna da duk wata sunnah da ta kamata ayi lokacin da aka samu qaruwa ta haihuwa?
AMSA❗
Wa'alaikumus salamu waramatullah wabarakatuh
Salati
da aminci maras adadi sukara tabbata sugaban abin abin kaunar mu annabin rahma
(S. A. W).
KEBANTATTUN
SUNNONIN DA SHARI,AR MUSULINCI TA TANADA DA AKEYIWA JARIRI A YAYIN DA AKA HAIFE
SHI.
kamar
yadda suka zu daga manzun allah (S.A.W)
1-
naima masa tsarin allah
2-
yin godiya ga allah bayan an haife shi(ba tare da la,akari da namiji ne ko mace
ce ba)
3-yi
masa tahniik(fara ciyar da shi dabino) da kuma naima masa albarka
4-
sanya masa suna
5-
Yanka masa haqiqah
6-
Aske masa gashin kansa
7-
Yi masa kaciya
Bayanan
su daki-daki:-
1-
naimawa jariri tsarin allah daga shaidan kamar yarda mahaifiyar nana maryam
(A.S) (wato matar imrana)ta ce-: a yayin da ta haife ta
عليهما السلام -: ﴿ رَبِّ
إِنِّي وَضَعْتُهَا أُنْثَى وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا وَضَعَتْ وَلَيْسَ الذَّكَرُ
كَالْأُنْثَى وَإِنِّي سَمَّيْتُهَا مَرْيَمَ وَإِنِّي أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا
مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ﴾ [آل عمران: 36].
To
a yayin da ta haife ta sai ta ce:, ya ubangijina lalle ni na haife ta ya' mace,
kuma allah shine mafi sanin abin da ta haifa, kuma da na miji ba daidai ya ke
da ya' mace ba, kuma haqiqa ni na rada mata suna maryam, kuma haqiqa ni ina
nema mata tsarinka da zurriyar ta daga shaidan korarre(suratu al,imran 36)
Ya
kamata da zaran anhaifi jariri to yana da kyau mahaifiyar sa ta nema masa
tsarin allah daga babban maqiyin sa wato iblis domin addu,ar uwa ga ya'yan ta karbabbiya
ce in sha allah.
2-
yin godiya ga allah yayin da aka haife shi lafiya(ba tare da la,akari da namiji
ne ko mace ce ba)
Daga
kasiir dan ubaida (R.D) ya ce : "nana a,isha (allah ya kara yarda agare
ta) ta kasance idan akayi haihuwa acikin su- wato a ahalin ta - bata tambayar
namiji ne ko mace ce, tana cewa ne an haife shi lafiya? Idan akace ee an haife
shi lfy, sai ta ce:dukkan godiya ta tabbata ga allah ubangijin halittu"
[imam albani - allah yai masa rahama- ya hassana shi acikin sahihi adabul
muprad a shafi na 534 ].
3-
yi masa tahniik da kuma yima sa addu,ar samun albarka
Daga
nan aisha (R. d) tace: "annabin (S. A.w) ya kasan ce ana zuwam masa da
yaran da aka Haifa, yana musu addu,a ta samun albarka daga wajan allah da kuma
yi musu tahniik" [muslim ne ya rawaitu shi].
Menene tahniik?
Attahniil
shi ne sakawa jariri wani abu na dabino a bakin sa bayan an tattauna dabinun
sai ya kasan ce taunannan da binun shine farkon abin da zai fara shiga hanjin
sa bayan an haife shi.
1-
wanene zai yiwa jariri tahniik?
An
tambayi samahatush shaikh dan baz - allah yai masa rahma:- game da daukar
jarirai a kai su wajan malamai domin su yi musu tahniik; sai ya hana hakan,
kuma ya ce: " mahaifin sa ko mahaifiyar sa suyi masa tahniikin, sannan ya
ce: da za,a bude kofar tahniik, ti da mutane sun zurfafa a cikin sa." (ma,
ana sunhuce gona da iri) [risalatu masaa,ili abii umarus sadhaani lil,imaami
binu baz shafi na 43].
(domin
a dauki jariri a kai shi wajan wani domin yayi masa tahnik ya kebanci annabi
(s.a.w.) Ne Shi ka dai bisa mafi ingancin maganar malamai)
An
rawaitu daga al,imam ahmad: "haqiqa shi an haifa masa yaro, sai ya cewa
mahaifiyar yaron ki yimasa tahniik"; [tuhfatul mauduud bi ahkamil mauluud safi
na 66]
**Lokacin
tahniik shi ne lokacin da aka haife shi
Shaikh
dan uthaimin - allah yaima sa rahma- ya ce:- " attahniik yana kasancewa
lokacin da akayi haihuwa har ya kasance shi ne farkon abun da za a fara ciyar
da jaririn da shi....."; [fatawaa nurun alaad darbi shafi na 14\2]
**Tahniik
yana kasancewa da dabinu
Daga
nana a,isha, (allah yakara yarda da ita)ta ce: "anzu da abdullahi dan
zubair wajan manzan allah (s.a.w)- domin yayi masa tahniik, sai muka naimi
dabinu, sai naiman sa yaimana huya"; [Muslim ne ya rawaitu shi.]
**To
Idan kuma ba a sami dabinu ba
Ahmad
dan anbal( rahimahullah) yace-: wani lokaci ya na lasawa yaron zuma"
[almugnii 2\497]
**
Idan ba a samu zuma ba, sai aimasa tahnik da dukkan wani abu mai zaqi
**
Tambaya: shin ya halatta ayiwa jajiri tahniik da zuma ko suga?
Amsa:
"ya halatta, sai dai asali shine ayi tahnik da dabinu, to amma idan ba a
sami dabinun ba sai aimasa tahnik da abin da ba shi ba daga abin da yake da
zaqi";[ashshaikh abdul muhsin al,abbaad, ya fadi hakan acikin sharyin
sunanu abii daahuud 1/158].
**Daga
cikin Fa,idar tahnik
Daga
cikin dabinu da annabiba (s.a.w)ya kasance yana yiwa jirirai: tahnik da shi,
lalli acikin dabinu akwai alkhairi da albarka, kuma yana da amfani ga ma,ajiyar
abinci (wato babban hanji) da ke ciki, to idan ya kasance shine farkon abin da
ya fara shiga zuwa ma,ajiyar abinci, Hakan sai ya zama alkhairi ga ma, jiyar
abincin"; [shaikh dan uthaimin acikin sharhin riyadus saliyiin, a babin
hakuri 1\269].
4-
sanya masa suna
**A-
sanya masa suna haqqi ne na mahaifin sa
Imam
dan qayyum ( rimahullah) yace-: wannn na daga cikin abin da babu jayayya acikin
sa a tsakanin mutane, kuma haqiqa idan iyaye suka yi jayayya wajan sanyawa yaro
suna, to haqqin samasa suna na mahaifi ne, kuma hadisan da suka gabata dukkan
su suna nuni akan haka"; [tuhfatul mauduud bi ahkaamil maluud shafi na
233].
**B-
sanya suna ga wanda ba mahaifi ba kuma ba mahaifiya ba ya halatta
Daga
baban musa yace: "yace an haifamin yaro,sai na kaiwa annabi (s. A.w) shi
sai ya sanya masa suna ibrahim yaimasa tahnik da dabinu, kuma yaimasa addu,ar
albarka, kuma ya miko min shi"; [bukhari ne ya rawaito shi].
**C-
yaushene ake sanya masa suna
1-
a ranar da aka haife shi
Daga
baban musa yace: "yace an haifamin yaro,sai na kaiwa annabi (s. A.w) shi
sai ya sanya masa suna ibrahim yaimasa tahnik da dabinu"; [bukhari ne ya
rawaito shi 5467].
**2-
a rana ta uku
Khallaal
ya ce acikin jami,i nasa-rahimahullah - :(a babin ambatun sanyawa yaro suna).
Abdul
malik dan abdul hamid ya bani labari ya ce: mun tattauna gami da a kwana nawa
ne ake sawa yaro suna? Sai abu abdullahi- ahmad dan hambal ya ce mana-: amma
abin da ya tabbata, an rawaito daga anas (allah ya qara yadda da shi) haqiqa
shi yana sanyawa yaro suna a rana ta uku, amma shi kuma samura - allah ya qara
yarda da shi - yana sawa yaro suna a rana ta bakwaic";[tuhfatul maudud fi
ahkamil maulud shafi na 167].
**3-
a rana ta bakwai
Daga
samura (r. d) ya ce: annabi( s. A. W.) yace: ((yaro ana tare shi daga alkhairi
idan ba a yimasa haqiqa ba, za,a yanka masa haqiqa a rana ta bakwai da haihuwar
sa, kuma asa masa suna
a
rana ta bakwai, kuma a aske masa kansa)) [ imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma
albani ya inganta shi acikin mushkaatil masaabiih].
**D-
sunaye mafiya daraja da ake so a sanya su kuma suka halatta
An
so asanya wadannan sunayan
Daga
anas (R. D) yace: annabi (s. A. W) ya ce- (( mafiya soyiwar sunaye awajan allah
sune: abdullahi da abdurrahman da kuma haris)) [ albani ya inganta shi acikin
sahihil jaami,i shafi na 162].
Fadakarwa
**
anso a sanya sunaye da suka fara da (abdu) da aka rabasu da kowane sunan daga
cikin sunayen allah.
**Kuma
anso asanya sunayen annabawa da manzanni (amincin allah ya kara tabbata a gare
su).
**
kuma anso a sanya sunayan sahabbai (allah ya kara yarda da su) da kuma sunayan
salihan bayi daga cikin musulmai.
5=
yankawa dan jariri haqiqa(abin yanka irin su rago ko akuya ko tunkiya)
Ma,anar
haqiqah: "ita ce mutum ya yankawa jaririn sa abin yanka:
yanka
abin yanka a rana ta bakwai, (alhaqiqah): ita ce abin yankan da ake yankawa ga
jariri arana ta bakwai a yayin da ake aske gashin kansa" ; [alwajiz shafi
428].
**HUKUNCEN
TA: Shaiku dan uthaimin (rahimahullah) ya ce-: ita haqiqah sunnace mai qarfi ya
dace ga wanda yake da ikon yinta to ya tsayar da ita (ya aikata haqiqar), kuma
ita an shar,antata ga mahaifi ne kadai, ana yankata a rana ta bakwai daga
haihuwar jaririn"; [majmu,ul fatawa wa rasa,ilul uthaimin 25\203].
LOKACIN
DA AKE YIN HAQIQAH: Sunnah shine a yanka abin yankan a rana ta bakwai daga
haihuwa, idan ba asamu damar yankawa ba a rana ta bakwai sai a yanka a rana ta
goma sha hudu idan ba a samu damaba sai a yanka a ra rana ta ashirin da daya;
Daga
buraida (r.d) daga annabi (S. A. W) ya ce: ((haqiqah ana yankata a rana ta
bakwai da haihuwa ko kuma rana ta sha hudu, ko rana ta ashirin da daya))
[baihaqi ne ya rawaitu shi, kuma albani ya inganta shi acikin sahihul jami,i
4132].
**
GWARGWADON ABIN DA ZA, A YANKA: ana yanka akoyoyi biyu ga yaro, yarinya kuma
ana yanka mata akoya daya; sabo da abin da ya tabbata daga hadisin ummuna
a,isha (r.d) ta ce: annabi (s.a.w) ya umarce mu muyankawa yaro akuya biyu, ita
kuma yarinya akuya daya" [dan maja ne ya rawaitu shi, kuma albani ya
inganta shi acikin sahihu bn majah 2561]
**
HALACCIN YANKA NAMIJI KO MACAN DABBA A CIKIN HAQIQA
saboda
hadisin ummu kurzun (r.d) ta ba shi labari haqiqa ita taji mazan allah. -
s.a.w- yana cewa -: ((ga yaro ayanka masa akuya biyu ga yarinya kuma a yanka
mata akuya daya, ba zai cutar da ku ba idan abin yankan ya kasance namiji ne ko
mace ce)) [ abu dahud ne ya rawaitu shi kuma albani ya inganta shi acikin
sahihil jami,us sagir 4106]
**
IDAN ZA, A YANKAWA YARO AKUYA BIYU TO SU KASANCE SA,ANNI (TSARAN JUNA)
daga
ummu kurzin. (R. D) ta ce: na ji mazan allah. (s.a.w) yana cewa: ga yaron da
aka haifa ayanka masa akuyuyi biyu tsarannin juna, ita kuma mace a yanka mata
akuya daya; [ baihaqi ne ya rawaitu shi, kuma imam alvani ya inganta shi a
cikin al, irwaa,a 1166.]
**
Shin ya halatta a yanka akuya daya ga da namiji?
Shaikh
bn uthaimin (allah yaimasa rahama) ya ce : idan mutum bai sami akuya biyu ba
sai daya to ta, isar masa, kuma an samu da ake nufi da ita, sai dai idan allah
ya kasance ya azurta shi, to biyun sune sukafi falala" [ ashsharhul
mumta,a 7/492]
**
cin bashi domin yin haqiqa
Kuma
an tambayi abu abdullah: akan mutumin da aka haifa masa da (yaro), kuma bashi
da abin da zai yanka masa, shin yafi soyiwa agare ka ya ci bashi ya yi masa
haqiqa, ko ya jinkir ta har sai allah ya hori masa? Sai ya ce: mafi tsananin
abin da na ji gami da haqiqa abin da alhasanu, ya rawaitu daga samurah (r.d)
daga annabi(s.a.w)-: ((ko wani ya a natare shi da ga alkhairi idan ba a yanka
masa haqiqa ba)) kuma haqiqa ni ina fatan idan yaci bashin allah zai gaggauta bashi
abin da zai biya bashin, domin ya raya wata sunnah da ga cikin sunnar annabi
(s.a.w) kuma ya bi abin da ya zo daga gare shi; [ masa,ilu imam ahmad riwayatu
ibnahu masaa,ilun fiil aqiqah juzu,i 2 shapi 208]
**
abin da ake cewa ayayin yakan aqiqah
عن عائشة - رضي الله عنها
- أنها قالت: "عق رسول الله - صلى الله عليه وسلم - عن الحسن والحسين، وقال:
((قولوا: بسم الله، والله أكبر، اللهم لك وإليك، هذه عقيقة فلان))؛ [رواه البيهقي،
وقال النووي: إسناد حسن، في المجموع (8/428)].
Daga
ummuna a,isha (r.d) haqiqa ta ce: annabi (s.a.w) ya yankawa hasan da Hussain
aqiqah kuma ya ce: (Ku ce: da sunan allah kuma allah ne mafi girma ya allah
daga gare ka kuma zuwa gare ka, wannan ita ce aqiqar wani)
6-
aske gashin kan yaro arana ta bakwai da kuma yin sadaka da azurfar da ta kai
kwatan kwacin nauyin gashin kan sa (ko kuma sadaka da kudin da suka kai qimar
nauyin azurpar)
Daga
samura (r. d) ya ce: annabi( s. A. W.) yace: ((yaro ana tare shi daga alkhairi
idan ba a yimasa aqiqah ba, za,a yanka masa aqiqah a rana ta bakwai da haihuwar
sa, kuma asa masa suna
a
rana ta bakwai, kuma a aske masa kansa)) [ imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma
albani ya inganta shi acikin mushkaatil masaabiih].
Daga
baban rafi,i haqiqa annabi (s.a.w)ya ce wa fadima yayin da ta haifi alhussain:
(( ki aske masa gashin kansa, kuma ki yi sadaka da azurfa da ta kai nauyin
gashin kan sa ga miskinai [imam ahmad ne ya rawaitu shi, kuma albani ya hassana
shi a cikin al,irwa,i 1175]
**
na daga cikin sunnar da aka kaurace mata shafe kan yaron bayan an aske kansa da
za,afaran
Daga
buraidah (r.d)ya ce: mun kasance a jahiliyya idan aka haifarwa dayan mu yaro,
za, ayanka akuya kuma sai a shafe kan yaron da jinin ta, amma yayin da
musulunci ya zo mun kasance muna yanka akuya a rana ta bakwai kuma mu aske
kansa kuma mu shafe kan nasa da za,afaran"; [abu dahud ne ya rawaitu shi,
kuma albani ya inganta shi a cikin sahihi abi dahud 2843]
7-Yiwa
jariri kaciya a rana ta bakwai
Daga
jaabir (r.d) ya ce annabi (s.a.w) ya yankawa hasan da husain aqiqah, kuma yayi
musu kaciya arana ta bakwai. [baihaqi ne ya rawaitu shi]
Daga
dan abbas ya ce: " abubuwa bakwai suna da ga sunnar yaron da aka haifa
arana ta bakwai: sanya masa suna, da yi masa kaciya, da kauda masa qazanta, da
huda masa kunnan sa, da yanka masa aqiqah, da shafe kan yaron da jinin dabbar da
aka yanka masa, da kuma yin sadaka da azurfa ko zinari da suka kai nauyin
gashin kan sa da aka aske" [ baihaqi ne ya futar da shi acikin
al,ausad"(1\133\2)]
Sheikhul
albani (rahimahullah) ya ce: daya daga cikin wadannan hadisai biyu yana karfafa
daya duk da dai hanyar da suka futu ta bambanta, kuma babu tuhuma a cikin su,
kuma haqiqa shafi,iiyah sunyi roko da shi, sai suka so ayi kaciya arana ta
bakwai da haihuwa ; kamar yadda ya ke a cikin majmu,i1\307"; [tamamul
minnah fiit ta,aliiqi alaa fiqihus sunnah juzu,i na 1 shafi na 68].
**
kaciyar mace
An
tambayi sheikh bn baz- menene hukunxin kaciyar mace, shi ko akwai wata hujja
baiyananna da take nuni akan haka?
Sai
shaikh bn baz rahimahullah]) ya amsa da cewa: da sunan allah kuma dukkan godiya
ta tabbata ga allah
Kaciyar
mace sunnah, idan aka sami likitan da zai kautata hakan ko likitar da zata
kyautata hakan; saboda fadin sa (s.a.w)-:((dabi,o,i biyar suna daga cikin
dabi,o, in musulunci: yin kaciya, da da aske gashin mara, da rage gashin baki,
da yankan kunba (farce), da tsige gashin hammata (wato askewa) [bukhari da
muslim ne suka rawaitu shi] shi wannan hadisin ya game maza da mata bai
banbanta suba acikin hukuncin sai dai ban da aske gashin baki domin shi ya ke
banci maza ne kawai banda mata domin shi sufface ta maza" [majmu,ul
fatawa10/47].
Allah
shine mapi sani
Amsawa:
abu abdullah
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.