TAMBAYA (145)❓
Assalamu
Alaikum. Dan Allah malam inada tmby
Malam inajin kamar nakashe aurena saboda mijina bayabani duk wata kulawa dazata gusarmin da sha'awata daga kan duk wani da namiji shekararmu takwas da aure Yaya uku da cikin na hudu Kuma nice ta uku agurinshi Kuma Yana ciyar damu kamar yanda Allah yace Yana Kuma biyan kudin maganin duk wata lalura datasamu Yana mana dinki duk sallah Kuma Yana mu'amalantar Yan iyaye da yan uwanmu cikin martabawa, Babbar damuwar shine Dan kasuwa ne Yana fita kullum da kamar misalin karfe 7 ko 8 nasafe Sannan bazai dawoba sai karfe 12 ko 1 nadare
Kuma
idan yadawoma bazai iyayin fira damuba komunyimasa yakan nuna bayaso saidae
ayishiru yakunna kallo awayarsa yaci abinci yayi bacci ko kwalliya nayi Dan na
Burgesa zai nunakamar banyi komaiba tun inakorafi har nagaji nadaina babu wani
shauki ko burgewa da mace takeyiwa mijinta kwanciyar aurenma sai idan shi yake
da bukatarki idan bahaka ko kinaso shi bayada ra'ayi haka dasafe dayatashi yayi
sallah zaiyi wanka Yana gama shiryawa shikenan zaidamu Azo adebi abinci shi
sauriyakeyi kana gaidashi wallahi wani lokacin kamar Wanda yayi gudu haka yake
amsawa da haki
Sannan
tarbiyar yarana yasakarmana saidai mu mata wallahi malam agidan ko fashin
sallah zakai badalili babu maicewa danme haka yakemana duka matan nasa damuwar
tana damunmu saidae muzanta atsakaninmu duk wasu Abubuwa nasamun ladan aure
munrasashi. saidai nazaman gidan aure da girki idan yazo kanka kayi ko away
bashi da lokacin iyalinsa wani lokacin idan fitar gaggawa tasami mutum
yakirashi awaya wallahi kinkira yakeyi har takai wasu acikin matan sukan fita
unguwa say adadi da yawa batare da saninsaba saboda rashin lokacinsa Allah
yakarawa malam lafiya kaji dalilin kayi hakuri da yawan rubutu
AMSA❗
Waalaikumus
salam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu
Alhamdulillah
Da
farko dai Ina tayaki alhini saboda halin jarabawar rayuwa da kika shiga, Allah
yana jarraba ki ne Ya ga shin za ki koma gareShi ne don neman taimakon Sa bisa
wannan jarrabawar, Kamar yanda ya fada
(
الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ
وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْغَفُورُ )
الملك (2)
Al-Mulk
Shi
ne Wanda Ya halitta mutuwa da rãyuwa domin Ya jarraba ku, Ya nũna wãye daga
cikinku ya fi kyãwon aiki, Shi ne Mabuwãyi, Mai gafara.
Kuma
in Sha Allahu da akwai mafita domin kuwa dukkan tsanani yana tare da sauqi
kamar yanda Allah [Subhanahu wata'ala] ya fada
(
فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ
يُسْرًا )
الشرح (5)
Ash-Sharh
To,
lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
(
إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )
الشرح (6)
Ash-Sharh
Lalle
ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
Yawancin
mazaje musamman na yanzu sam sam basa yiwa matansu adalci
Indai
yanda kika fada haka zancen yake to haqiqa wannan Mijin naku baya muku adalci
Kuma abinda yake kawo irin wannan matsalar shine: rashin koyi da kyawawan
halayen Annabi Sallallahu alaihi wasallam da kuma jahiltar bin Sunnar sa
Annabi
tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya kasance abin koyi ga dukkan
al'umma kuma koyi da shi ne kadai mafita a garemu
Irin
wannan matsalar ce ta sa ake son a binciki halayen mutum da kuma kyakkyawar
mu'amalarsa da mutane kafin a yi zamantakewar auratayya da shi
Idan
kika duba cikin littafin "Shama'ilil Muhammadiyya" na Abu Isah
at-Tirmidhi zaki ga yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yake gudanar da
mu'amalarsa da iyalansa
A
cikin littafin sa mai suna "Adabul Mufrad", Imamul Bukhari ya kawo
ladubbai dayawa akan yanda mutum zai aiwatar da al'amarin rayuwar sa na yau da
gobe kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu
Haka
ma a cikin littafin "Seerah" zaki ga yanda Ma'aiki tsira da amincin
Allah su qara tabbata a gareshi yake nuna tsantsar love da kulawa ga matayensa.
Nana Aisha Radiyallahu anha tace duk sanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam
zai shigo gidansa Yana sumbata [kissing] dinsu, wanda tuni turawa suka kwace
wannan koyin. Alhalin mu musulmai ne yakamata mu dinga dabbaqa wannan Sunnar a
gidajenmu. Idan kuka karanta littafin "Guidelines To Intimacy In
Islam" wato "Shiriya akan tafiyar da rayuwar aure a musulunce"
zaku amfana matuqa da ilimin da littafin ya qunsa
Duk
rashin karanta irin wadannan littattafan da Kuma maida hankali a iya Kasuwanci
zalla ne yasa idan namiji yayi aure zai wahala ka ga yana bawa iyalansa
cikakken lokacin tattaunawa akan wata matsala ballantana Kuma ya ware lokacin
fira
Allah
Subhanahu wata'ala ya bawa mace wata irin baiwa ta musamman wadda zaka ga ta
iya sarrafa akalar mijin ta kamar yanda makiyayi zai iya sarrafa dabbar sa
Da
kisisina, iyayi, iya magana mai dadi, kallo mai sace zuciya da kuma shagwaba
kadai mace zata iya sarrafa mijinta, sai yanda kika so kiyi dashi
Rashin
sanin dabarun iya sarrafa miji ne yake saka wasu Matan suna fadawa tarkon
shaidan su fara bin tsinannun bokaye da yan tsibbu wanda a karshe kuma mace ta
je ta siyarda imaninta. Wal'iyazubillah
Duk
mijin da zai bar gida tun karfe 8 na safe har zuwa karfe 12 na dare wannan kam
ya zama bawan kudi. Bazai iya ware awa guda cur ya saurari maganar matarsa ba.
Kusan dukkan tunanin sa yana kasuwa. Kwanciyar shimfida zai yi ta ne domin
gusar da sha'awar kansa amman ba ta matarsa ba
Ta
gamsu ba ta gamsu ba, ba ruwansa indai shi ya gamsu. Wannan yana daga cikin
dalilan da suke sa indai mace ba mai tsoron Allah ba ce ba sai kaji an ce an
kamata tana lalata da wani a waje. Sai wadda Allah ya tseratar
Shawarar
da Zan baki anan itace
Ki
dinga tashi cikin tsakar dare kamar irin 2 ko 3 ki yi ta nafilfili kina fadawa
Allah buqatunki. Ki nunawa Allah da gaske kike, ki fada maSa buqatunki musamman
idan kikai sujjada. Ki roqi Allah da wadannan addu'o'in
Kiyi
salatil Ibrahimiyya
Sannan
sai kice: "La'ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minazzalimeen"
kamar yanda Annabi Yunus [Alaihis Salam] ya fada a cikin kifi
Ki
tuno da addu'ar da Annabi Ibrahim [Alaihis Salam] yayi a lokacin da aka jefa
shi cikin wuta: "Hasbunallahu wani'imal wakeel"
Ki
fadawa Allah buqatunki
Sannan
sai ki sake yin salati ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam
Kada
ki gaji da yin hakan ko da sau 1 ne a kowanne sati, In Sha Allahu zaki ga sauyi
a zaman ku
Haka
zalika, duk sanda mijinki ya dawo komin daren da zaiyi ki dinga tarbarsa cikin
girmamawa. Idan kin fahimci yana cikin walwala sai ki bijiro masa da tambaya:
"Nikam my Love me yasa kwana biyu ka sauya, ba ma fira akan yanda muke a
da, ko wanine yake bata mata rai a Kasuwa". Da irin wadannan tambayoyi
zaki iya jin dalilan da suka sa baya baku yalwataccen lokacin
Sannan
Kuma zata iya yiwuwa kin Bata masa rai ne alhalin ke ba ma ki sani ba, ta
hanyar janyo shi a jiki da yi masa shagwaba ne kadai zaki iya gano inda gizo ke
saqar
Sannan
Kuma idan bakya zuwa Islamiyyah to yakamata ki fara zuwa ki zama ustaziyar dole
ta yanda idan wata matsala ta taso shi kansa Mijin zai dinga tambayar ki me
addini yace gameda abu kaza da kaza domin kuwa babban abinda mata basu sani ba
shine majority maza ba sa son ace mace ta fi su ilimin addini
Shima
Kuma kamata yayi ace yana karanta littattafan addini, ya dinga ware lokaci yana
karatu don neman dacewa a duniyarsa da lahirarsa
Kinga
kenan duk sanda kema kika fara neman ilimi tuquru dole Mijin ki zai duba
darajar wannan ilimi naki ya dinga baki kulawa wadda a da can baya baki
Idan
Kuma duk da haka kika ga bai daina abinda yake ba Kuma hakan zai iya sa ki
sabawa Allah musamman ta bangaren rashin samun gamsuwa to sai ki sanar da
waliyyanki, a tara ku ga ki ga shi a tambaye shi dalilan da suka sa ba ya iya
biya Miki buqata
Idan
ba shi da lafiya ne to sai a bashi damar neman magani idan Kuma ya nuna shi
bazai sauya ba to idan zaki iya haquri da ci gaba da zama dashi hakan zaifi
Miki akasin haka Kuma zaki iya rabuwa dashi [Kul'i] indai za'a shiga haqqinki
Wallahu
ta'ala a'alam
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash hadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa'a'tubu ilayka
Amsawa
Usman
Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.