Waɗannan zaɓaɓɓun barkwanci ne daga taskar www.amsoshi.com.
Wani malamin Agric ya ba wa yara assigment kowa ya zo da wake kwano biyu.
Wani ya kawo matarsa kemis. Aka yi mata allura sannan aka ba ta vitamin C. Mijin ya ƙwace ya zubar, ya ce: "Buɗa ciki suke yi."
Wane mataki za ki ɗauka idan kika zo kika tarar da mijinki yana dukan saurayinki😑 a gaban wanda za ki aura 🥺🚶?🙄
Yaro ya ga tsoho fa sanƙo, ya ce: "Baba wa ya yi maka aski?" Tsoho ya ce: "Duniya ce yaro!"
Amarya ta cinye taliya leda guda. Ango ya kalle ta ya ce: "Amma ba a haka za a rayu a nan ba ko?" 😟
Idan fa ka aure gajerar mace, ko ba password sai ka ajiye wayarka a saman pridge.
An ce kukan kurciya jawabi ne. Shi kuma kukan sauro fa? 😰
Turare na gani a status ɗin wata. Na tambaya: "Nawa?" Ta ce mini: "Dubu tamanin (80k)." Shi ne na tambaya: "A jarka yake ko a galan?"
Daga tambaya ta yi blocking ɗina.🤔🤷♂️😢
Status: "Idan na aure ki, ba zan bari albasa ta shiga gidana ba saboda ba zan taɓa yarda da duk wani abin da zai saka ki hawaye ba."
Comment: "Magana ake na mai ƙarya ɗan wuta."
Wata mata mijinta ya yi tafiya. Da dare sai ta kira shi a waya take cewa: "Sweet heart yau ba ka nan gidan ya yi duhu." Ba a jima ba sai ta ji an ƙwanƙwasa ƙofa. Da ta buɗe ɗan'uwanta ne da mai gyaran wuta.👨🚒 Suka ce: "Ya ce wutar gidan ta ɓaci."Hira tsakanin miji da mata.
Miji: Na ga ƙawarki sai ƙara kyau take yi.😊
Mata: Ka san haka maganin HIV yake idan ya karɓi mutum.🛌
Miliyan 7 aka ba ni da hannun hagu, na ƙi karɓa. 😏 Tarbiyya ai ba wasa ba ne.🤷♂️Duk daɗin soyayya ba ta kai shinkafa da wake ba.😋
Duk son cuwacuwan cefena na mata, yanzu sun fi son ka sayo da kanka. 🤭
Idan mace tana soyayya da mai kuɗi, za ka ga har so take yi ya kafa mata doka domin ta nuna tana jin maganarsa.Mun sauƙe farashi domin layya.
Rago babba = 3,000
Rago ƙarami = 2,000
Akuya babba = 1,000
Amma sai da dare muka kasuwanci saboda a unguwarmu akwai 'yan sa'ido da ba sa son cigabanmu.
Wata yarinya ce🧕 babanta ya mutu⚰️ ya bar mata Million 95💴Wllh tsabar tausayi😭 har na fara son ta. 💖😍🙈🏃Tun da aikin Hajji bai yiwu ba, sai mu duƙufa aikin hanji. 😎
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.