Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Maganganun Falsafa (2024)

Waɗannan wasu maganganun falsafa ne da aka samar a shekarar 2024.
Falsafa
An halicci ɗan'adam da shauƙi wanda ke tasirantuwa daga abubuwa da yanaye-yanaye da suka cuɗanye shi. Wannan ne ya sa ba gangar jiki ba ce kaɗai ke tasirantuwa da muhallinta, har da zuciya da kurwa. (Sani, A-U. 2024)

Falsafa
An yi labarai babu adadi game da lamura da abubuwan da suke cikin duniya da har ya kai da wuya a samu wani lamari da tunani bai raya shi ba. Wannan ya sa labarai mafiya jan hankali a yau suka ƙetara iyakokin duniyar nan! (Sani, A-U. 2024)
Falsafa
"Babbar hanyar koyon rubutu ita ce koyon karatu." (Sani, A-U. 2024)
Falsafa
"Ko da ba ka da damar kyautata wa mutane, to lallai kana da damar kiyaye ƙuntata musu. Ka guji addu'ar wanda aka zalunta!" (Sani, A-U. 2024)

Post a Comment

0 Comments