Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Hadisan Manzon Allah (SAW) Da Aka Rubuta Domin Gaisuwar Juma'a

Waɗannan wasu hadisan Manzon Allah (SAW) ne waɗanda aka tsara a kan hotuna na musamman domin turawa a matsayin gaisuwar Juma'a. Wannan hanya ce babba ta tunasar da 'yan uwa da abokan arziki.
Hadisi
Juma@t Mubarak🕊️⛈️

Duk lokacin da Manzon Allah (SAW) ya ga za a yi ruwan sama, yakan ce: "ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI-AN" 
Ma'ana: "Ya Allah ka ba mu ruwa mai albarka.” (Sahih Al-Bukhari: 1032, Littafi: Book 15, Hadith 27)

Hadisi
Barka da Juma'a🕊️

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutane za su kasance kamar fari, masu ƙarfi suna cin masu rauni (babu tausayi), har dai ƙiyama ta tsaya a kansu." (Silsilatus Sahiha: 1953)
Hadisi
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne idan aka jinkirta maka mutuwa, sai kuma ka samu yin aikin ƙwarai domin Allah, to za ka samu ƙarin ɗaukaka. (Sahih Abi Dawud: 2864)
Hadisi

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne ita sa'a (ƙarshen duniya) ba za ta tsaya ba har sai an daina rabon gado (na dukiyar matattu) tukun. (Sahuh Muslim: 2899)
Hadisi
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Da dai kun san ladar da kuke samu a wajen Allah a dalilin damuwa, da kuwa kun so a ƙara muku damuwa da talauci." (Silsilatus Sahiha: 2169)
Hadisi
Amru Ibn Hazmin Al-Ansari ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya gan ni na jingina da wani ƙabari, sai ya ce:" "Kada ka cutar da mai ƙabarin."" (Silsilatus Sahiha: 2960)
Hadisi
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne talauci ya fi saurin isa ga mai so na (don jarabawa), fiye da ambaliyar ruwa daga saman dutse zuwa ƙasa." (Silsilatus Sahiha: 2828)
Hadisi
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne bala'o'i sun fi saurin isa ga mai so na (don jarabawa) fiye da isar ambaliyar ruwa zuwa ga ƙarshensa." (Silsilatus Sahiha: 1586)
Hadisi
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne na gani ana yi muku jarabawa a cikin ƙaburbura. Tsananinta yana kama da na fitinar Ad-Dajjal." (Muslim: 903; Nasa'i: 1475)
Hadisi
Barka da Juma'a 🕌💐

Manzon Allah (SAW) ya ce: "An yi min wahayin cewa za a muku jarabawa a ƙaburbura. Tsananinta yana kusa da na fitinar Ad-Dajjal!" (Al-Bukhari: 7287; Muslim: 903)
Hadisi
Barka da Juma'a 💐

Jabir Ibn Abdullahi ya ce: "Manzon Allah ya hana a yi fenti a ƙaburbura, ya hana yin gini a kansu, kuma ya hana wani ya zauna a kansu." (Sahihun Nasa'i: 2027)
Hadisi
Juma@t Mubarak 💐🕌

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Mutanen da idan mutumin ƙwarai ya rasu suke gina masallaci a kan ƙabarinsa, su ne mafi sharrin halittu ga Allah a ƙiyama." (Al-Bukhari: 427)

Post a Comment

0 Comments