Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Zubar Da Cikin Da Na Tabbatar Sikila Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Slm mallam ni AS ce, mijinama ma AS ne thesame genotype muke da shi, yarana biyu babban AA karamar AS, duk sanda na sami ciki muna zuwa a duba mana genotype ɗin babyn dake cikin, likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a cire, amma bai kaiwa 4months muke cirewa, mallam meye hukunchin yin hakan ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, To 'yar'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.

Amma sun yi saɓani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta.

Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata huɗu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Sikcler ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata huɗu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.

Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil islamy na Umar Ganam.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments