𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum dafatan anwuni lafiya malam, dan Allah
malam ina neman shawara ina da aure 'ya'yana ukku, na farko yana da shekaru
bakwai (7 years) kuma yana da sikila na biyun yana da shekaru biyar (5 years)
sai ta ukkun nada Shekarau biyu (2 years) itama tanada sikila watanta biyar
yanzu da rasuwa, sai ɗayan
Wanda baida sikilar ya fara ceman kafarshi na ciwo ba ayi awaba kuma
hannunwanshi suma suka fara ciwo, sai duka jikin shima ya ɗauki ciwo, shima mai
sikilar sai ya fara ciwan, muna zuwa asibiti aka basu gado muka kwanta sun
tambaye mu Wanda bai da sikilar mun yi mashi awo ne mukace a'a, saboda tunda
akai haifeshi bai taɓa
ciwo ba sai mura da ɗan
zazzaɓi shima na rana ɗaya ne yawarke to sunyi
mana bayanin cewa wata sikilar na daɗewa
kafin ta bayyana to sai ya rasu, shima ɗayan
kwana ɗaya da rasuwar
wancen sai ya rasu kuma kanwarsu wata biyar tsakaninsu hankalina ya tashi yanzu
banda 'ya'ya kuma ni kaɗai
ce wajen mijina, shi ya kuma faɗi
mani dole yakara aure ni kuma ya ce sai nan da shekara goma yake san in haihu
ni kuma inasan 'ya'ya kuma ina san mijina amma ban san in haihu da shi saboda
na sha wahalar yara kuma jinin mune ɗaya
kaga dole tinani ya dame ni, shin zan iya cewa mijina ya sauwake mani inje
insamu wani Wanda zan iya haihuwa yara ba sikila ba?? dan ALLAH inasan Karin
bayani nagode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam, Tabbas Kina cikin damuwa da tashin
hankali, Tun da kin zama Mai wabi. Allah ya shar'anta saki ne Domin tunkuɗe cuta daga ɗaya daga cikin ma'aurata Ko
dukansu Kamar yadda ayar Suratun Nisa'i ta tabbatar da hakan. Mutukar kin ga a
cigaban zamanku akwai cutarwa kina iya neman rabuwa da shi Ko ta hanyar saki Ko
fansar kai. Yana daga cikin manufofin aure samun zuriyya waɗanda za su ɗebe kewa. Idan Kuka rabu
Allah zai iya azurta kowa daga falalarsa, ya ba ki miji ya kuma ba shi matar da
in sun haɗu ba za su
haifi Sikila ba.
Allah ne mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.