Ticker

6/recent/ticker-posts

“Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”: Taliyon Dangantakar Adabi da Al'ada

Citation: Sani, A-U. and Bakura, A.R. (2024). Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto: Taliyon Dangantakar Adabi da Al'ada. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 319-327. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.040.

“Zamo Mini Tubali in Zam Miki Hoto”: Taliyon Dangantakar Adabi da Al'ada

Abu-Ubaida Sani
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
WhatsApp: +2348133529736

And

Dr. Adamu rabi’u bakura
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: arbakura62@gmail.com
Phone: 08064893336

Tsakure

Manufar wannan bincike shi ne gano nau’in alaƙar da ke tsakanin adabi da al’ada. An zaɓi yin amfani da tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano (stratified random sampling) domin tabbatar da cewa ba a ɗauki samfurin al’adu da ake kallo ko aka san da zamansu cikin adabi ba kawai. An ɗora aikin kan falsafar Hausawa da ke tunanin cewa hulɗa na kasancewa ne cikin tsarin cuɗe ni in cuɗe ka. A bisa wannan ne binciken ke hasashen cewa, adabi na da bazar takawa wajen bayyana hoton al’adu kamar yadda al’ada ke da rawar takawa wajen kasancewa tubalan gina adabi. Sakamakon binciken ya tabbatar da wannan hasashe inda ya kasance an samu dukkannin samfuran al’adu da aka ɗauka a cikin ɓangarorin adabin baka. Ta la’akari da wannan ne daga ƙarshe binciken ya ba da shawarar ƙara faɗaɗa bincike kan tasirin adabi a kan al’ada da kuma na al’ada a kan adabi.

Fitilun Kalmomi: al’ada, adabi, matakan rayuwa, bayyanannun al’adu, ɓoyayyun al’adu

1.0 Gabatarwa

“Al’ada” ba baƙuwar kalma ba ce ga kunnuwa da bakunan Hausawa. A kullum Hausawa na amfani da kalmar a bagire mabambanta bisa ma’anoni masu kama da juna waɗanda ba a rabe su da sababben al’amari ko sananniyar hanyar gudanar da lamura. Rubuce-rubuce masu tarin yawa da masana suka gudanar game da al’adun Hausawa na ƙara nuni ga kasancewar kalmar fitacciya da ba ta buƙatar wani dogon sharhi. Kalmar al’ada ta ratsa ayyukan masana da manazarta irin su Mustapha, (2003) da Najahu, (2018) da Bunza, (2019) da Abdullahi, (2021). Yayin da aka nazarci waɗannan rubuce-rubuce da makamantansu, za a tarar da cewa al’ada na nufin tsarin rayuwa ta gaba ɗaya wadda ta haɗa da sanannun sababbun al’amuran da ke gudana yau da kullu bisa wasu tsararrun ƙaidoji da matakai da kuma waɗanda aka saba da wanzuwarsu kara zube ba tare da ƙaida ta musamman ba.

A ɓangare guda kuwa, ayyukan da aka yi game da adabi sun fi shurin masaƙi. Wani abin burgewa shi ne, ba a samu saɓanin ra’ayi ba game da bayanin adabi a matsayin madubi ko hoton da ke bayyana rayuwar al’umma.[1] A farfajiyar Hausa da Hausawa, ana iya cewa adabi na nufin fasahohi da hikimomi na ƙirƙira da zalaƙa da ƙwarewar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha da ke kasancewa cikin salo-salo da siga-siga na labartawa ko rerawa ko ambatawa ko samar da sautin da ke isar da manufa da ba da ma’ana ta musamman, waɗanda ke nuna hoton zuci na rayuwar al’umma na gaba ɗaya, ciki har da bayyanannu da ɓoyayyun al’adunsu.

Wannan takarda ba ta kasance ta farko ba a wannan bagire na nazartar dangantakar al’ada da adabi. Sai dai mafi yawan ayyukan da aka gudanar a baya game da wannan batu suna da taƙaitattun kadada. Yawanci sukan ɗauki waɗansu keɓantattun al’adu ne domin nazartar yadda hotunansu suka bayyana cikin adabi, ko su ɗauki keɓantattun fannonin adabi domin nazarin wata al’ada ko wasu al’adun da suka ratsa cikinsu. Za a tarar da misalan hakan cikin ayyukan Yahya, (2001) da Mustapha, (2003) da Yahya, (2013) da  Sarkin Gulbi, (2014) da Buba, (2016) da Najahu, (2018) da Bunza, (2019) da Abdullahi, (2021) da makamantansu. Maƙasudin wannan bincike kuwa shi ne (i) gudanar da nazarin ƙwaƙƙwafi don gano ko aladu ne tubalan gina kowane nauin adabi, da (ii) gudanar da nazarin ƙwaƙƙafi don gano ko ana iya ƙyallaro dukkannin nauukan aladu daga cikin madubin adabi?

1.1 Dabarun gudanar da bincike

Wannan bincike ya shafi al’adun Hausawa ne a kadadar adabin baka. An bar kadadar wannan bincike a buɗe. Ba a taƙaita ta ta fuskar ayyana taƙamaimai nauukan aladu ko fannonin adabin baka da za a nazarta ba. Rashin taƙaita kadadar ne zai tabbatar da nazarin ya binciko abin aka ƙudurta tare da tabbatarwa, ko kuma kore hasashen da binciken ya yi.

A ƙoƙarin cimma maƙasudin wannan bincike, an duba samfurin aladun Hausawa a cikin adabin bakansu. Wannan ya shafi (i) bayyanannun aladu da (ii) ɓoyayyun al’adu da (iii) matakan rayuwa.[2] Kasancewar al’adun Hausawa suna da matuƙar yawa, an ware samfurin da ya wakilci saura. An yi amfani da tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano (stratified random sampling). An bi abajadi a matsayin ma’aunin rukunonin (strata) samfurin, inda aka ɗauki ɗaya daga (1) cikin kowane rukunin abajadi biyu (2), na farko da na ƙarshe. Bisa bin waɗannan matakai da alƙaluma ne aka samu samfuri kamar haka:

Jad. na 1: Samfurin bincike

Matakan Rayuwa

 

Zaɓaɓɓen Samfuri

Lamba

Matakan Rayuwa

 

Rukuni

Bayyanannun Al’adu

Ɓoyayyun Al’adu

1

Aure

A

Abinci

Amana

2

Haihuwa

Z

Zani

Zumunci

3

Mutuwa

 

Madogara: Tsararren salon zaɓar samfuri na wa-ta-gangano

Domin cimma hasashen binciken, ba a keɓance waɗansu rukunonin adabin baka ba domin gudanar da nazarin.[3] An yi ƙoƙarin taƙaita nazarin ta hanyar ɗaukar abubuwan da suka zo ƙarƙashin Jadawali na 1 da ke ƙasan 1.1 domin duba misalansu daga cikin fannonin adabin baka da hannu ya fara kaiwa gare su.

1.2 Ra’in bincike

Wannan nazari ya shafi adabi da al’adun Hausawa ne tsurarsu. Hakan ya sa ba a tafi neman na dawa ba alhali na hannu bai kai gida ba, kamar yadda Bunza, (2019 p. 721) ya yi wannan jan hankali. Ko ba komai, mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo. Hakan ya sa aka sakar wa waɗannan manyan fagage na adabi da al’ada mara domin su yi tuwona-maina ta fuskar zaƙulo hanyar ɗora aiki da ta dace da tunanin Hausawa kan batun da ake magana a kai.

An ɗora wannan nazari kan fahimtar Hausawa cewa “lamarin zaman duniya cuɗe ni ne, in cuɗe ka.” A bisa wannan tunani, ana sa ran duk wani abu ko wani lamari da ya cuɗanya da wani abu na daban, to wancan abin shi ma ya cuɗanya da shi ta waɗansu fuskoki, ko dai kai tsaye ko a kaikaice. A fahimtar wannan ra’ayi, binciken yana da hasashen cewa aladu su ne tubalen ginin kowane nauin adabi. A ɓangare guda kuwa, adabi madubi ne da cikinsa za a iya hango dukkannin nau’ukan al’adu.

2.0 Bitar dangantakar adabi da al’ada

Al’ada da adabi ɓangarorin rayuwa ne guda biyu da ke tafiya hannu da hannu. Suna zama ne irin na cuɗe ni, in cuɗe ka, ko na ba ni gishiri, in ba ka manda. Za a iya tabbatar da hakan cikin ayyuka daban-daban da suka gabata da ke nuna cuɗeɗeniyar waɗansu al’adu da ɓangarorin adabi. Daga ciki akwai ayyukan Abdullahi, (2000) da Muhammad, (2008) da Atuwo, (2009), Giwa, (2012), Bunza, (2013), da Musa, (2019) da Abdullahi, (2021) da waɗansu masu tarin yawa.

Babu wani nau’in adabi da al’adu ba su kasance tubalan gidan shi ba. Haka kuma, babu wata al’ada da ba ta da gurbi cikin adabi. An ga yadda Abdullahi, (2000) ya hasko hotunan magunguna da siddabarun Hausawa a cikin ƙagaggun labarai. Aikin Haliru, (2018) ya nuna yadda ake samun nason yaƙi cikin adabi.[4] Bunza, (2019) kuwa ya hasko yadda ƙwarya ta ratsa adabin bakan Bahaushe.  A aikin Abdullahi, (2021) kuwa, an ga yadda doki ya fito a nau’ukan adabin bakan Bahaushe, musamman labaru da karin magana. Waɗannan da makamantansu suna daga cikin dalilan da suka ƙarfafa hasashen wannan bincike na cewa alada da adabi na tafiya ne hannu da hannu.

3.1 Matakan rayuwar Hausawa a cikin adabin baka

Matakan rayuwa na nufin waɗansu muhamman gaɓoɓi ko zanguna da rayuwar ɗan’adam ke ratsawa ta cikinsu, waɗanda ke dabaibaiye da al’adu daban-daban masu sauyawa daga lokaci zuwa lokaci sakamakon yanayi da sauyin zamani da kuma tasirin baƙin alummu. Manyan matakan rayuwa su ne (i) aure da (ii) haihuwa da (iii) mutuwa. Wannan ɓangare na aikin ya mayar da hankali kan zawarcin matakan rayuwar Hausawa cikin adabin baka.

3.1.1 Aure

A tunanin Hausawan ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21), ana iya cewa aure na nufin wata yarjejeniya ta musamman da ake ƙullawa tsakanin namiji da mace, bisa wasu sharuɗa da ƙaidoji da suka fara tun daga nema har zuwa ɗaurawa da tarewa da abubuwan da ke biyo baya da suka shafi zamantakewa a matsayin miji da mata, bisa waɗansu ƙayyadaddun tanade-tanaden alada da addini. Wannan muhimmin mataki cikin matakan rayuwar Hausawa ya mamaye adabin baka.

Tatsuniyoyin[5] Hausa da dama an gina su kan wannan jigo na aure ko dai a matsayin babban jigo da ya mamaye tatsuniyar, ko kuma ƙaramin jigo a cikinta. A tatsuniyar ‘Yar Bora da ‘Yar Mowa, an ga yadda auren ɗan sarki ya kasance sakamako mai kyau ga ‘Yar Mowa. Mummunan aure kuwa ya kasance sakamako marar kyau ga ‘Yar Bowa. A tatsuniyar Icen Ƙosai ma, an ga yadda auren ɗan sarki ya kasance sakamako nagari ga ‘yar kishiyar da ta sha baƙar wuya a wurin kishiyar uwarta.[6]

A ɓangare guda kuwa, duniyar karin maganar Hausa na cike da batun aure. Waɗansu daga cikin karin maganganu da suka shafi aure da ake yawan ji a bakin Hausawa sun haɗa da:

a.      Aure ba ka da malam

b.      Ba haka aka so ba, ƙanin miji ya fi miji kyau

c.       Ƙarya ba ta sa amarya lalle.

d.     Ƙoshin takaba aure da mai ƙararren kwana

e.      Larura auren namiji da ‘ya’ya

f.        Matar na-gode, ba ta rasa mijin aure[7]

3.1.2 Haihuwa

Haihuwa na nufin fitar wani abu mai rai daga jikin wani abu mai rai bayan saduwa tsakanin mace da namiji, wanda yawanci abin da ya fita na kama da waɗanda suka samar da shi a bayyane kamar ta fuskar launi ko zubi da tsari, ko kuma a ɓoye kamar ta fuskar ƙwayoyin halitta da halayya da ɗabi’u. Haƙiƙa jigon haihuwa ya karaɗe adabin bakan Hausawa. Wannan ɓangaren nazarin ya kawo ‘yan misalai.

A cikin almarar Ɗan Zaki da Ɗan Mutum, an ga yadda tun farko aka gina ta kan mace mai ciki da ke shirin haihuwa. A ɓangare guda kuwa, sai aka koma kan zakanya da ita ma ke shirin haihuwa. Daga nan almarar ta ci gaba da ginuwa a kan Ɗan Mutum da Ɗan Zaki, har zuwa girmansu da gwagwarmayar rayuwarsu.[8]

A ɓangare guda kuwa, ɗaya daga cikin ƙissoshin[9] da suka kama bakin Hausawa shi ne na wani hukuncin hikima da Annabi Sulaiman ya yanke game da haihuwar wani jariri. Mata biyu sun kafa gardama inda kowa ta ƙeƙashe ƙasa cewa ita ta haifi jaririn. Duk ƙoƙarin duniyan nan da Annabi Sulaiman zai yi don gano asalin mahaifiyar ya faskara. Daga ƙarshe ya ce a samo zarto a raba jaririn gida biyu, kowace mata a ba ta rabi. Nan fa ɗaya daga cikin matan ta ce ita ta haƙura, a ba wa ɗaya matar jaririn ta tafi da shi. Bisa wannan ne kuma Annabi Sulaiman ya ce lallai jariri na wacce ta haƙura ɗin ne, domin sanin zafin haihuwarsa da soyayyar da take masa ya sa ba za ta bari a yi masa haka ba. Wannan na nuni ga matsayin haihuwa tare da dangantaka da shauƙi da tausayi da ke tsakanin abin da aka haifa da mahaifansa.

3.1.3 Mutuwa

Mutuwa na nufin gushewar rai daga ganganr jiki da ake iya tabbatarwa ta la’akari da manya da ƙananan alamomi da suka haɗa da daina motsi da sandarewar jiki da kafewar idanu da ɗaukewar numfashi da tsayawar bugun zuciya na tsawon lokacin da ya zarce suma a sababbiyar al’adar tsarin halittar ɗan’adam. Tsattsafin mutuwa ya ratsa ɓangarori daban-daban na adabin bakan Hausawa.

A ɓangaren labarai[10] ma, ana iya tsintar matakan rayuwar Hausawa, ciki har da lamarin mutuwa. A labarin Shehu Jaha da Wani Malami,[11] an ga yadda lamarin mutuwa ya bayyana. Babu abin da Shehu Jaha ya buƙata sai a sanar da shi ranar da zai mutu.

3.2 Bayyanannun al’adun Hausawa cikin adabin baka

Bayyananniyar al’ada ita ce duk wata nau’in al’adar da idanu ke iya gani ko hannu ke iya taɓawa. Ta fi shafar ƙere-ƙere da sauran sarrafe-sarrafen alumma da suka haɗa da abinci da gine-gine da sutura da zane-zane da duk sauran nau’ukan kayan al’ada da ba su ɓoye wa idanun ɗan’adam ba, ciki har da abubuwan da suke samammu ko wanzazzu a muhallan al’umma. Tsattsafin bayyanannun al’adun sun mamaye duniyar adabin bakan Hausawa. Wannan ɓangaren nazarin ya kawo misalai da ke tabbatar da hakan.

3.2.1 Abinci

Abinci shi ne duk wani abin da al’ada ta ɗauka a matsayin marar illatarwa da ake sa wa a baki, a tauna, a haɗiye domin kawar da yunwa ko marmari. Yayin da aka leƙa adabin bakan Hausawa, za a tarar da abinci ta kowane lungu. Misali, akwai nau’ukan salon magana[12] daban-daban da aka gina su ta amfani da tubalin abinci. Daga cikinsu akwai:

A - Misalin salon magana mai ma’anar abinci

i. Salon magana: Abin sawa a baki

Ma'ana: Abinci

B - Misalan salon magana da aka gina da tubalan abinci

ii. Salon magana: Ban ci nanin ba nanin ba ta ci ni ba

Ma'ana: Tun da ban amfana ba ba zan yi asara ba

iii. Salon magana: Ci kare ba babbaka

Ma'ana: Mutum ya yi yadda yake so ba tare da shakka ko fuskantar ƙalubale ba

iv. Salon magana: Cin tumbin kunkuru

Ma'ana: Yin haƙuri da wahalar da mutum ba shi da maganinta

v. Salon magana: Zaman doya da manja

Ma’ana: Ƙiyayya ko rashin jituwa

A ɓangaren yanken[13] Hausawa ma za a tarar da waɗanda aka yi amfani da abinci a matsayin tubalan gina su. Daga ciki akwai:

a.      Ana rige-rigen shiga aljanna ka tsaya wawan ɗanwake!

b.      Da ka ɓurka tusa sai da malmala ta yi nishi!

c.       Da wani hancinka kamar an kai alale/alala walda!

d.     Ka ci zogale ɗaya ka cika duniya da koren kashi!

e.      Ka ɗauko baki kamar ɓarnar wuƙa a kabewa!

f.        Kana ci ba ka ƙiba kamar ka ci matsefata!

3.2.2 Zani

Ɗuriyar zani a matsayin wani nau’in tufafin Hausawa ta mamaye duniyar adabin bakan Hausawa yadda har ta kai an samu sara[14] da yayi[15] game da shi. A ƙasa an kawo waɗansu misalan sara da yayi game da zani da suka ci zamaninsu a ƙasar Hausa. Daga ciki akwai:

Jad. na 2: Sara masu alaƙa da zannuwa

 

Sara

Tsokaci

1.

Kama ta kare! Ko

Wuh-wuh! Ko

Mai barewa!

A wajajen shekarar 2015 an yi wani nau’in zani mai hoton barewa a jahar Bauchi. Sai dai kash! Zanin ya yawaita sosai a cikin al’umma har ya zama abin aibantawa. Abin ya kai ga har yara da matasa na zolayar masu ɗaura shi. Yara sukan yi waƙa kamar haka:

Bayarwa: Mai barewa

Amshi: Wuh-wuh!

Bayarwa: Kama ta kare!

Amshi: Wuh-wuh![16]

Yayin ya karaɗe garuruwa sosai[17] yadda ko da ɗaya daga cikin kalmomin aka furta, ana dai nufin zolaya ga mai ɗaure da zanin.

2.

Mai ganyen rogo!

A wuraren 2006 an yi wani zane mai zanen ganyen rogo. Da zarar an ga mace da shi sai a fara zolayar ta da cewa: “Mai ganyen rogo!” Wannan dalilin ya sa kasuwar zanin ta mutu duk da kyawunsa.

3.

Karen miski!

A shekarar 2017 an yi wani zane na mata mai laushi da gashi-gashi a jikinsa. An yi yayin sa ne a lokacin bikin salla. Da zarar mace ta sanya sai a ce mata: “Karen miski!”[18]

 

Jad. na 3: Yayi masu alaƙa da zannuwa

 

Yayi

Tsokaci

1.

Kamfala

Kamfala da soso da koken da siliki duk nau’ukan zannuwa ne da aka yi yayinsu a ƙasar Hausa. S. Habiba, (keɓantacciyar tataunawa, 21 ga watan Ogusta 2023) ta bayyana cewa, a shekarar da aka yi yayin waɗannan zannuwa, ko’ina mutum ya waiga ranar salla ‘yan mata zai gani ɗaure da su.

2.

Soso

3.

Koken

4.

Silikin

 

Yana da kyau a lura da alaƙar da ke tsakanin sara da yayi a wannan gaɓar. Haƙiƙa su ma sun yi canjaras da falsafar Hausawa game da cuɗe ni in cuɗe ka da ke aukuwa tsakanin lamuran da suka shafi rayuwar duniya. Misalai uku (3) da aka bayar a jadawali na 1 duk sara ne da suka samu a sanadiyyar yayi. Ko misalai huɗu (4) da aka bayar a ƙarƙashin jadawali na 3, S. Habiba, (keɓantacciyar tataunawa, 21 ga watan Ogusta 2023) ta bayyana waɗansu nau’ukan sara da suka tsiro a sanadiyyarsu. Misali, yawaitarsu ya sa yayin wata waƙa ya karaɗe gari inda yara ke rerawa kamar haka:

Mai silikin silellukan babanta!

Mai kamfala kamfanin babanta!

Mai koken uwarta ba ta salla!

Mai Jamila da Jamilu shegiyar ‘yar banza!

3.3 Ɓoyayyun al’adun Hausawa cikin adabin baka

Ɓoyayyun al’adu su ne nau’ukan al’adun da ido ba ya ganin su sannan hannu ba ya iya taɓa su. Sun shafi tadoji da tunane-tunane da ra’ayoyi da falsafofin al’umma, kamar gaskiya da amana da kawaici da kunya da tarbiyya da tausayi da zumunci da makamantansu. Wannan ɓangare na nazarin ya kawo misalan gurabun da ɓoyayyun al’adun Hausawa suka fito cikin adabin bakansu.

3.3.1 Amana

Amana ita ce riƙo da gaskiya a zamantakewa da hulɗa tare da karewa da alkinta dukiya da mutunci da sirrin abokin hulɗa a gaban idonsa da bayan idonsa. Amana tana da babban gurbi a cikin kirarin[19] Hausawa. Sau da dama mai yin kirari na amfani da kalmar amana wajen nuna dangantakarsa da ubangidansa, ko wajen nuna wurin da ya gaji jarumta da hatsabibanci. Misali:

a.      Wayyeeeehoho! Ni Abu amanar Lamara!

b.      Ni Abu na Abu mai amanar daji! An ba ni amana na karɓa!

A misalin “a” da ke ƙarƙashin “3.3.1,” za ga a cewa mai kirarin yana danganta kansa da wanda ake yi wa laƙabi da Lamara. Lamara ya kasance Ciroman Aska a garin Misau da ke Jahar Bauchi.[20] A ƙarƙashin “b” kuwa, a bayyane take mai kirarin na ishara ne kan cewa shi ɗan gado ne ba ɗan haye ba. Sannan ya gaji laƙanin da suka shafi daji, kuma ya ƙware kan harkar.

Ko bayan ire-iren waɗannan, akwai maganganun kirari na yau da kullum da ke ƙunshe da kalmar amana. Misalansu sun haɗa da:

c.       Ni kububuwa amanar mutuwa.

d.     Ni mahaukacin kare amanar yaƙi.

Idan aka leƙa duniyar waƙoƙin gargajiya ma za a tarar da hotun al’adu, ciki har da amana. A waƙar roƙon ruwa ta Allah Mun Tuba,[21] za a ga yadda masu waƙar ke bayyana cewa ba za su sake cin amana ba, don dai jaddada tubansu ga Allah domin ya tausaya musu ya ba su ruwa. Kamar yadda suke cewa:

...

Bayarwa: Gero a dawa ya bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

Bayarwa: Masara a dawa ta bushe,

Amshi: Allah mun tuba.

...

Bayarwa: Ba mu cin amanar ɗan kowa,

Amshi: Allah mun tuba.

3.3.2 Zumunci

A farfajiyar al’ada, zumunci kalma ce mai rassan ma’ana da ke da dangantaka da nau’in hulɗa da jin kusanci ga juna tare da jiɓintar lamuran juna da ke samuwa a sanadiyyar nasaba ko alaƙa ta jini ko maƙwabtaka ko kasuwanci da makamantan cuɗanya na dogo ko gajeren zango tsakanin mutane biyu ko fiye. Zumunci tubali ne da akan yi amfani da shi wajen gina adabin bakan Hausa.

Babban misali game da wannan shi ne barkwanci, wanda nau’in adabin baka ne da aka gina shi kacokan kan zumunci. Tun daga ma’anar da Ɗangambo ya bayar a cikin Muhammad, (2008) za a iya ganin hakan. Ya bayyana barkwanci da cewar: “...zantuttuka ne na raha da wasu mutane waɗanda Allah ya hore wa iya magana da ban dariya ke wa mutane. Akwai wasanni tsakanin ƙabilu iri-iri, su irin waɗannan wasanni (yawanci da baki ake yi), suna ƙara danƙon zumunci, misali akwai wasa tsakanin Fulani da Barebari, Kanawa da Zage-Zagi, Katsinawa da Gobirawa da Haɗejawa da sauransu.”

Bugu da ƙari kuma, maganganu da labaran barkwanci da dama suna ɗauke da ƙunshiyar amana. Daga ciki akwai kalamai irin su:

a.      “Ina kwana, tun da ka ƙi gai da uban gidanka.”

b.      “Ka san mu ba ma mantawa da yaranmu.”

A ire-iren waɗannan kalamai da ke gudana tsakanin masu wasan barkwanci, za a ga nason zumunci. A misali na “a” da ke ƙarƙashin “3.3.2”, za a ga cewa mai maganar na ƙoƙarin nuna cewa ya yi riƙo da zumunci. Hakan ne ya sa ya fara gaishe da wanda yake maganar da shi, duk da ya fi shi matsayi, don dai kada zumunci ya yanke. A ƙarƙashin misali na “b” kuwa, ƙarara mai maganar ya nuna cewa ba za su yanke zumunci ba ta hanyar mantawa da yaransu.

Idan aka leƙa kacici-kacicin Hausawa ma za a tarar da tsattsafin zumunci. Misalan kacici-kacici da ke ɗauke da nason zumunci sun haɗa da:

i. Kacici-Kacici: Bishiyar gidanmu, inuwar gidan waɗansu.

Amsa: Budurwa[22]

ii. Kacici-Kacici: Daga nesa na ga layun ƙawata.

Amsa: Bishiyar ɗorawa[23]

iii. Kacici-Kacici: Ki shiga, ki fita, ɗakin na uwarki ne?

Amsa: Moɗa/guga[24]

iv. Kacici-Kacici: Malam ya faɗi almajirai sun taru

Amsa: Kashi da ƙuda[25]

4.0 Sakamakon bincike

Lallai ya tabbata ƙarara cewa adabi da al’ada suna wanzuwa ne bisa tsarin cuɗe ni in cuɗe ka. Tsarin tattara bayanai da zaɓar samfurin bincike da aka bi na ƙara tabbatar da hakan. An ga yadda matakan rayuwa suka bayyana cikin fannonin adabi mabambanta. Misali, an ga yadda aure ya fito a cikin tatsuniya da karin magana (3.1.1). An ga lamarin haihuwa kuwa a cikin almara da ƙissa (3.1.2). Lamarin mutuwa kuwa, an hasko shi cikin labari (3.1.3).

ɓangaren bayyanannun al’adu kuwa, an kawo yadda samfuran al’adu da aka ɗauka suka bayyana cikin nau’ukan adabi. Misali, abinci ya fito cikin salon magana da yanke (3.2.1). Zani kuwa ya fito cikin sara da yayi (3.2.2). Samfuran al’adu da aka ɗauka a ƙarƙashin rukunin ɓoyayyun al’adu kuwa su ne amana da zumunci. An leƙo amana a madubin adabi na kirari da waƙoƙin gargajiya (3.3.1). Zumunci kuwa aka hango shi cikin barkwanci da kacici-kacici (3.3.2).

Wani abin lura shi ne, yawanci tubalan al’ada sama da guda ne ke haɗuwa domin gina wani nau’in adabi. A misalin waƙar roƙon ruwa da aka bayar a ƙarƙashin “3.3.1” da ke sama, an mayar da hankali ne kan ɓoyayyiyar al’ada (amana) da ta fito a cikin waƙar. An yi hakan ne ba don ɗangwayen sun taƙaita ga ƙunshiyar amana kaɗai a matsayin al’ada ba, sai don taƙaitawa kan abin da ake magana kansa a wannan bagiren. Akwai ɗangwayen da suka ambaci “gero” da “masara” waɗanda dukkanninsu suna daga cikin bayyanannun al’adu. A falsafance, ana iya cewa adabi guda na iya haska nau’ukan al’adu daban-daban a madubinsa.

5.0 Kammalawa

Babu wani nau’in al’adar Hausawa face sai an tarar da ita cikin madubin adabi. Haka kuma, babu wani nau’in adabin Hausa face sai an tsinci tsattsafin al’ada a cikinsa. Ke nan ana iya cewa, al’adu ne tubalan gina kowane nau’in adabi. A ɓangare guda kuwa, adabi madubi ne ko hoto da ke ɗauke da kowace nau’in al’ada. Tun da kuwa haka ne, akwai buƙatar zurfafa bincike a fuskar nau’ukan tasiri da al’ada ke da shi kan adabi, da kuma musamman tasirin adabi a kan al’ada. Ta irin waɗannan nazarce-nazarce ne za a iya gano shin tasirin al’ada kan adabi ke samar da sababbin nau’ukan adabi da sauye-sauye cikin waɗanda ake da su? Ko kuma adabi ne ke yin tasiri kan al’ada da har yake samar da sababbin al’adu? Ko wannan tasiri ana samun sa ne ta dukkannin fuskokin guda biyu? Nazarce-nazarcen da za su amsa ire-iren waɗannan tambayoyi za su taimaka wajen ƙara fahimtar fagagen biyu wato adabi da al’ada. Za kuma su yi ƙarin haske kan muhawarar nan da ke ci gaba da gudana ta tasirin zamani kan al’adun Hausawa.

Manazarta

Abdullahi, A. (2021). Doki a tunanin adabin bakan Bahaushe: Nazari daga labarun baka da karin magana [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Abdullahi, I. S. S. (2000). Magani da siddabaru cikin rubutattun ƙagaggun labarun Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Atuwo, A. A. (2009). Ta’addanci a idon Bahaushe: Yaɗurwarsa da tasirinsa a wasu ƙagaggun labarai na Hausa [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Buba, M. (2016). Adon harshe a adabin baka: Nazari a kan amfani da tsuntsaye a waɗansu waƙoƙin Ɗanƙwairo [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Bunza, A. M. (2006). Gadon feɗe al’ada. Tiwal Nigerian Limited.

Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a Farfajiyar Adabi da Al’adun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720–727.

Bunza, A. M. (2013). Wani ra’ayi dangane da yadda aka fitar da rayuwar Hausawa a cikin littafin Shehu Umar [Takardar da aka gabatar]. Taron Ƙara wa Juna Sani, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Giwa, A. A. (2012). Gurbin tarbiyya a cikin tatsuniyoyin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2021). Waƙoƙin Hausa na gargajiya. Amal Printing and Publishing.

Haliru, A. R. (2018). Yaƙe-Yaƙe a wasu rubutattun littattafan ƙagaggun labarai na Hausa na gasa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Muhammad, M. S. (2008). Hauka a idon Bahaushe [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Musa, M. Y. (2019). Tarken tarbiyya a cikin waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Mustapha, S. (2003). Gurbin gaskiya cikin adabin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Najahu, I. K. (2018). Adabi madubin al’ada: Tsokaci a kan al’adar baƙunci a adabin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Sarkin Gulbi, A. (2014). Magani a ma’aunin karin magana [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Yahya, A. B. (2001). Dangantakar waƙa da tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa. Harsunan Nijeriya, XIX, 94–109.

Yahya, A. B. (2004). Tattalin zaɓen rubutattun waƙoƙin Hausa domin yara. FAIS Journal of Humanities, 3(1), 217–232.

Yahya, A. B. (2013). Tsattsafin raha cikin waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno. Mujallar Nazarin Waƙoƙin Hausa, 1(1).

Yahya, A. B. (2016). Salo asirin waƙa (sabon bugu). FISBAS.

Yahya, A. B., & Aliyah, A. A. (2020). Kukan kurciya cikin waƙoƙin Korona biyu. Amadu Bello University Press.

 [1] Rubuce-rubuce da aka gudanar a fannin adabin Hausa sun haɗa da ayyukan Yahya, (2004) da Bunza, (2006) da Yahya, (2016) da Bunza, (2019) da Yahya & Aliyah, (2020) da Abdullahi, (2021) da makamantansu.

[2] An keɓance matakan rayuwa ne (aure da haihuwa da mutuwa) ba don ba su da muhalli cikin rabon farko na bayyanannu da ɓoyayyun al’adu ba, sai don a ba su gurbi na musamman kasancewar suna ba babban matsayi a fannin nazarin rayuwa. Samun dukkanninsu cikin madubin rayuwa wani mataki ne na fara samun tabbacin ana iya kallon dukkannin al’adun Hausawa cikin wannan madubi.

[3] Keɓancewar zai tabbatar da iƙirarin binciken na cewa kowanne rukunin adabin baka na ƙunshe da al’ada a matsayin tubalan gina shi.

[4] A shafi na 54 ya nuna cewa: “Yaƙi wata muamula ce ta gwadi da nuna fifikon ƙarfi tsakanin mutanen ƙasashe ko ƙungiyoyi fiye da ɗaya, masu gaba da juna, domin neman biyan wasu buƙatu na rayuwa waɗanda ba a iya samu sai ta hanyar tilastawa.”

[5] “Tatsuniya wani tsararren labari ne mai ɗan tsawo na hikima da nuna ƙwarewa da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da kuma cinye lokaci” Yahaya da wasu a cikin Buba (2016: 85).

[6] A duba (Gobir & Sani, 2021: 122) domin samun cikakkiyar tatsuniyar.

[7] Domin samun ƙarin misalai, ana iya duba https://www.amsoshi.com/2017/07/karin-magana-game-da-aure_5.html.

[8] Yahanya da wasu a cikin Buba, (2016 p. 85) sun bayyana cewa, almara “... labari ne shiryayye, ƙagagge cikin hikima da ake aiwatarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko don nishaɗi da nishaɗantarwa.”

[9] A mahangar addini, ƙissa labari ne na annabawa da sahabbai da mala’iku da waɗansu muhimman mutane ko halittu a cikin addini. A mahangar adabi da al’adun Hausawa kuwa, akan samu sauye-sauye da ƙirƙire-ƙirƙire a lamarin ƙissoshi domin fitar da waɗansu darusa tare da faɗakar da al’umma.

[10] Buba, (2016: 92) ya rawaito inda Zarruk da wasu suka ba da ma’anar labari da cewa: “... zance ne tsararre mai kai da gindi. Wato irin zance da ka iya cewa ga farkonsa. Sannan kuma idan an ƙare, kana iya sani. Irin wannan labari yana iya zuwa ko a magance ko kuma a rubuce, kuma wani lokaci akan same shi da ɗan tsawo.”

[11] Domin samun wannan labari a kammale, ana iya duba https://www.amsoshi.com/2023/08/labarin-shehu-jaha-da-wani-malami.html.

[12] Salon magana na nufin amfani da kalmomi biyu ko fiye waɗanda dunƙulalliyar maanarsu ta bambanta da maanoninsu yayin da suke a matsayin ɗaiɗaiku.

[13] Yanke tsararrun zantukan hikima ne na muzanci ko kushe ko soka baƙar magana ga wani mutum ko waɗansu mutane ta hanyar siffantawa ko kwatanta su ko wani ɓangare na jikinsu ko wani abu da ke da alaƙa da su ko halayya da ɗabi’unsu da wani abu ko wani lamari mai ƙasƙancin matsayi ko wanda zai ba da hoton zuci da ke bayyana su a matsayin nakasassu ko ƙasƙantattu ko koma-baya.

[14] Sara ƙirƙirarrun zantuka ne da kan yi tashe a wani lokaci, masu ba da ma’ana ta musamman ga wanda ya san su, waɗanda ake tsarawa game da wani mutum ko wasu mutane ko wani abu ko waɗansu abubuwa domin yabawa ko kushewa ko gorantawa ko zolaya ko ƙarfafawa, waɗanda kuma ke dusashewa ko ma su ɓace bayan sun ci zamaninsu.

[15] Yayi na nufin wani abin da ya yi fice a tsakanin mutane a wani taƙamaiman lokaci wanda mallakarsa ko samar da shi ko mu’amala da shi ko aiwatar da shi cikin wani ayyanannen salo da tsari shi ne burgewa, wanda kuma armashinsa ke dusashewa ko ma ya salwanta bayan ya ci zamaninsa.

[16] A wannan gaɓa ma za a tarar waƙa ta samu a sanadiyyar al’ada. Duk wannan na ƙara tabbatar da iƙirarin falsafar nan ta Hausawa game da “cuɗe ni in cuɗe ka.”

[17] Wannan bayani ya fito ne daga jahar Bauchi. Ba a samu tabbacin ko ya karaɗe garuruwan waɗansu jahohi na daban ba.

[18] I. Hamza, (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga watan Ogusta 2023)

[19] Kirari wasu gajerun zantukan hikima ne, tsararru da ake shiryawa domin yabo da jinjina da kambamawa ga mutum ko mutane ko wani abu ko waɗansu abubuwa, tare da kushewa ko ƙasƙantar da darajar kishiya ko kishiyoyinsa.

[20] An halarci taron janjanko (taron mafarauta da ƙauraye da wanzamai) a garin Misau, jahar Bauchi, a ƙofar Ciroman Aska da ke unguwar Mangari.

[21] Domin ƙarin bayani, ana iya duba Gobir da Sani, (2021 p. 134-135).

[22] Zumuntar aure ke sa budurwa tarewa wani gida.

[23] Idan har ƙawa na iya hango layun ƙawarta daga nesa sannan ta gane su, lallai zumunci ya yi zumunci.

[24] Da a ɗakin uwarta ta riƙa shige da fice, lallai ba za ta fiskanci tsangwama ba saboda ƙarfin zumuntar da ke tsakani.

[25] Da zarar wani abu ya faru da wani, zumai za su yi caa, har sai inda ƙarfinsu ya ƙare.

Download the article:

Post a Comment

0 Comments