Citation: Labaran, M.M. (2024). Nazarin Ɗan Waƙa Da Nau’o’insa a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 389-402. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.055.
Nazarin Ɗan Waƙa Da Nau’o’insa a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Muhammad Musa Labaran
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano
muhammadmusalabaran@gmail.com
08161747863
Tsakure
Ɗan waƙa shi ne ruhin duk
wata waƙar baka ta Hausa. Ashe kan ɗan waƙa ya zama tamkar wata
ma’ajiyar saƙonni ne, manya da ƙanana waɗanda suke fita daga
zuƙatan makaɗan baka na Hausa, su
kuma zuba su, tare da shirya su a cikin ɗan waƙa domin isarwa ga waɗanda abin ya shafi,
wato su sadar da su ta hanyar rerawa da gwamawa da amon kiɗa. Manufar wannan
bincike ita ce yin tarken tsarin ɗan waƙa da nau’o’insa a
cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru.
Takardar ta yi nazari bisa matakan ƙulla ɗan waƙa na + Jagora + ’Y/Amshi
+ tunani + rauji + gaɓa +kalma + saɗara + G/waƙa + ɗa + ɗiya + kiɗa da Makaɗa Sa’idu Faru yake bi
ya ƙulla nau’o’in ɗan waƙa guda uku. Wato
gajeren ɗan waƙa mai ƙunsar kammalalliyar
ma’ana da matsakaicin ɗan waƙa mai ƙunsar gutsire ko
kammalalliyar ma’ana da kuma dogon ɗan waƙa mai kammalalliyar
ma’ana. Kuma takardar ta ƙalailaice tsarin
ma’ana ta duban sassauƙan A1 A2
A3-A4 da kuma tsattsauran ɗan waƙa A1-B1,
C1, D1, E1, F1 G1-Z10
a cikin ɗaiɗaikun ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. An yi
amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya (WBB) na Gusau (1993.
2003, 2014 da 2023) a matsayin ra’in da aka ɗora wannan takarda a
kansa. A wannan takarda an yi amfani da dabarar bincike ta bi-bayani, wato
hanyar sharhantawa wajen yin sharhi da ƙalailaice ɗiyan waƙoƙin da aka zaɓa. Takardar ta gano
cewa, baya ga ɗa mai sauƙi da mai tsauri, za a
iya fitar da sabon rukunin ɗan waƙa, wato harɗaɗɗen ɗan waƙa. Haka kuma, ba sa
samun saukar ma’ana a gajeren ɗan da dogon ɗan waƙa ta ɗa da ɗa, sai dai a tsakanin
saɗaru. Amma ana samu a
cikin matsakaicin ɗan waƙa.
1.0 Gabatarwa
Waƙar baka wata aba ce
daɗaɗɗiya a ƙasar Hausa. Sannan
ana zaton kirare-kiraren farauta da na yaƙi su ne suka fara ba
da haske wajen faruwar waƙar baka. Waƙoƙin baka na Hausa sun
biyo zanguna aƙalla guda huɗu. Zango na farko shi ne zaman farko na
Hausawa (lokacin Maguzanci) zango na biyu bayan zuwan addinin Musulunci da
zango na uku zuwan Turawa musamman na mulkin mallaka da kuma zango na huɗu zamanin siyasa da
na sojoji. Duk a waɗannan zanguna, waƙoƙin na tafiya ne bisa
al’adu da hikimomi da fasahohin al’ummar Hausawa ta fuskar aiwatarwa da rerawa
da sadarwa. Haka kuma waƙar baka tana tafiya ne da sauye-sauyen al’adu a rayuwar
Hausawa. Masana da manazarta, baƙi da ‘yan gida sun yi
wa waƙar baka ribata wajen samar da ayyuka masu tarin yawa a
kan waƙoƙin baka na Hausa tun ma ba damar da suka samu ba ta fito
da hikimomi da falsafofin rayuwar Hausawa da suke tattare a cikinsu.
Bisa bincike, mawaƙa ko makaɗan baka na Hausa sun
kasu kashi uku; wato makaɗan bege da makaɗan fada da makaɗan game-gari. Akan
kira makaɗan fada da makaɗan sarauta ko iko a ƙasar Hausa. Sannan
sun samu ne bayan gama yaƙe-yaƙe a ƙasar Hausa tun a
wajejen shekara ta 1903, bayan da Turawa suka ci Ƙasar Hausa da yaƙi. Makaɗa Sa’idu Faru yana
cikin rukunin makaɗan fada.
Wannan
takarda ta mai da hankali ne a kan nazartar tsarin ɗan waƙa mai sauƙi da mai tsauri da
nau’o’in ɗan waƙa kamar gajeren ɗan waƙa da matsakaici da
kuma dogon ɗan waƙa. Wato takardar za
ta nazarci zahirin matanin ɗan waƙa ne a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin a
fito da yadda yake shisshirya saɗarunsa da kuma yanayin yadda yake sassarƙa saƙonninsa a cikin saɗarun ɗan waƙa.
A
wannan bincike, an yi amfani da ra’in Waƙar Baka Bahaushiya
(WBB) ne wajen ƙalailaice ɗiyan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru masu ƙunshe da ƙananan saƙonni da tsari na rera
ɗan waƙa. Wani ɓangare na wannan ra’i
yana magana ne a kan tsarin ɗan waƙa, wanda kuma tsarin ɗan waƙa ɗaya ne daga sigogin
awon baka da wannan Mazhaba ta raja’a wajen nazarta. Sannan an yi amfani da
sharhantaccen bincike wajen fito da irin tsari da ma’ana na ɗan waƙa da Makaɗa Sa’idu Faru yake
shirya ƙananan saƙonni a cikinsu. Sanna wannan bincike
zai taƙaita a kan nazarin waƙoƙi gua huɗu, wato waƙar kana shirye
baban ‘yanruwa da waƙar gwabron giwa uban Galadima da waƙar tsakin tama na
Abashe da kuma waƙar bajimin gidan Bello.
1.1 Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru A Taƙaice
An
haifi Makaɗa Sa’idu Faru a cikin
shekara ta 1932 a cikin garin Faru na cikin ƙasar Maradun, a Ƙaramar Hukumar
Maradun. Makaɗa Alu mai kurya[1]
shi ne ya haifi Makaɗa Abubakar Kusu ɗan Abdu, shi kuma shi
ne ya haifi Makaɗa Sa’idu Faru.
Asalinsu Gobirawa ne na cikin Sabon Birnin Gobir. Dukkanin waɗannan Makaɗa, Makaɗan iko ne, kuma an yi
su ne a garin Faru. Amma mahaifiyar Sa’idu Faru
mutuniyar Banga ce ta cikin Ƙasar Ƙaura-Namoda[2].
Idan aka dubi wannan bishiyar
salsala, za a ga Alu Maikurya waɗanda wasu suke yi masa laƙabi da Alu Maikotso, shi ne ya haifi mahaifin Makaɗa Sa’idu Faru, wato Makaɗa Abubakar ɗan Abdu. Shi kuma Abubakar ɗan Abdu ya haifi ‘ya’ya guda shida, cikinsu har da Makaɗa Sa’idu Faru. Shi kuma Makaɗa Sa’idu Faru ya haifi ‘ya’ya maza guda shida, wato
Ibrahim Abamu da Ibrahim Dage da Lawali da Haruna da Bello da kuma Salihu. Baya
ga ‘ya’ya maza kuma, yana da ‘yaya mata kamar haka, Hadija da Rabi’atu da
Lubabatu da Hadizatu da Rabi’atu ta biyu da kuma Faɗimatu.
Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure guda biyu: Zahra’u da Aminatu. Kuma yana da ‘ya’ya
maza da mata guda goma sha biyu (12). Mazan su ne ;
Ibrahim Abamu da Ibrahim Dage da Lawali da Haruna da Bello da Salihu. Matan
kuma su ne: Hadija da Rabi’atu da Lubabatu da Hadazatu da Rabi’atu ta biyu da
Faɗimatu. Zuwa yau, Makaɗa Sa’idu Faru yana da jikoki guda arba’in da biyu (42).
Makaɗa Sa’idu Faru Makaɗin shiri ne. Wato, yana zama da shi da yaransa su shirya waƙa kafin su sadar da ita
(Furniss 1996:177). Haka nan idan waƙa ta samu, yana yin ta a ko’ina ba tare da ya zauna ya
shirya ta ba (hira da Ibrahim Sa’idu Faru, 2020).
Ashe ke nan, Makaɗa Sa’idu Faru Makaɗin shiri ne kuma na ƙire. Daga cikin yaran Makaɗa Sa’idu Faru akwai Mu’azu da Muhammad Ɗandodo da Kwaɗo da Aliyu da Ɗandada da Bawa da kuma ‘ya’yansa guda biy, Ibrahim Abamu
da Ibrahim Dage.
1.1.1 Makaɗa Sa’idu Faru a Matsayin Turkakken Makaɗin Fada
Gusau (2023) ya raba
makaɗan fada zuwa gida
biyu; makaɗa turke a fada da
makaɗa sake a fada. Makaɗa Sa’idu Faru makaɗin fada ne a turke,
ta wata fuskar kuma sakakken makaɗin fada ne. Wannan bincike ya ayyana Makaɗa Sa’idu Faru a
matsayin turkakken makaɗin fada, saboda ba ya
yi wa malamai ko game-gari mutane waƙa. Duk wanda ya yi wa
waƙa
za a ga, ko dai Sarki ne ko kuma yana riƙe da wani muƙami na sarauta ko
kuma yana da jiɓi da sarauta. Ashe
kenan, ya taƙaita waƙoƙinsa ne ga iya waɗanda suke da sarauta.
Ta wata
fuskar kuma, za a iya ayyana Makaɗa Sa’idu Faru da sakakken makaɗin fada. Dalilin
hakan kuwa shi ne, ba ya ga iyeyen gidansa na waƙa, yakan tsallaka
wasu masarautun Ƙasar Hausa ya yi musu waƙa amma tare da izinin
iyayen gidan nasa. Misali, ya tsallako Ƙasar Kano ya yi wa
marigayi Alhaji Ado Bayero waƙa da marigayi Tijjani Hashim da kuma
marigayiya Hajiya Hasiya Bayero mahaifiyar marigayi Alhaji Ado Bayero. Haka
kuma, ya tsallaka masarautar Zazzau ya yi wa Alhaji Shehu Idris Sarkin Zazzau.
Haka kuma da sauran Sarakuna na gundumomi daban-daban. Misali, Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Alhaji
Abubakar da Alƙali Shehu da Sarkin Kaura Namoda Alhaji Abubakar Garba da
Ɗanmadamin
Sakkwato Usman Ɗangwaggo da Sarkin Kiyawa Ƙaura Namoda Ahmadu da
Sarkin Musulmi Abubakar na uku da Sarkin Zamfarar Zurmi da Sarkin Gabas na
Mafara Shehu da Sir. Ahmadu Bello da sauransu.
Wasu
mutanen kan iya cewa, an samu wasu waƙoƙinsa waɗanda ya yi su ba na
sarauta ba, kamar waƙar yaƙin basasa na Nijeriya da makamantansu.
Sai a bada amsa da cewa, ai daman makaɗan fada asalinsu makaɗan yaƙi ne, bayan gama yaƙi ne a shekara ta
1903 suka koma suna yi wa Sarakuna waƙa. Ashe kenan, idan
ya yi waƙar basasa ya yi ta a muhallinta.
1.1.2 Fasalin Kayan Kiɗan Makaɗa Sa’idu Faru
Sa’idu Faru Makaɗi ne na kotso, kuma yana haɗa amfani da icen tofanni. Gusau (2017) ya bayyana kotso da cewa, “ ana yin
kotso ne da itacen ƙirya ko gawo ko kaɗanya ko kolo. Da farko za a fafare cikin itacen, a daidaita tsayinsa
gwargwadon buƙata, a fitar da bakunansa biyu, na sama da na ƙasa. Daga nan, sai a sami fatar tayi ko
damo ko guza a rufa baki ɗaya na saman. A yi
masa ƙangu a ɗaure da tsarkiya ta yadda za a tsuke saman da ƙasan. Za a manna wa
saman fatar nake, sai kuma a ɗaura zaga wato zare mai ƙara amo da diri.
Akwai kuma huda wadda ake liƙonta da saƙar zuma. Kayan haɗa kotso sun ƙunshi itace na ƙirya ko gawo ko kaɗanya ko kolo da fata
ta tayi ko damo ko guza ko akuya ko gada da tsarkiya da zaga da nake da tsumma
da ƙusa
da ƙaro
da kibiya da daddawa da fari na Hausa da sauransu. Ana kaɗa kotsi ne da yatsun
hannu, ana yi ana matse shi a ƙarƙashin hammata. Haka
kuma ana yi wa kotso maratayi ta yadda za a iya rataya shi a kafaɗa.”. kotso iri biyu ne, akwai na Fulani da kuma na Hausawa. Ana amfani da kotso
ne wajen kiɗan sarauta da sauransu.
Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa ne a wurin mahaifinsa
Makaɗa Abubakar Kusu. Tun Sa’idu Faru na
da shekara goma (10), aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cim ma shekara goma sha shida
(16) ya fara soma tarɓi. Sa’idu Faru da ƙanensa Mu’azu da
Muhammad sun dubi tsufan mahaifinsu, wannan ya sa suka dakatar da shi a fagen
kiɗa, sai Sa’idu ya ci
gaba da jan ragamar gidan a fagen kiɗa da waƙa yana shekara ɗan shekara ashirin da
uku (23). Bayan mahaifinsu ya rasu a shekara ta 1952, sai Sa’idu
Faru ya ci gaba da jagorantar gidansu a fagen kiɗa da waƙa. Sa’idu Faru yana amfani da kotso wajen kiɗa. Sa’idu Faru ya fara cin gashin kansa ne a lokacin da
ya shirya wata waƙa wadda take ƙunshe da tarin hikimomi[3].
1.1.3 Iyayen Gidan Makaɗa Sa’idu Faru
Ɗanmadami (2018) yana cewa, “Makaɗan fada su ne waɗanda ke aiwatar da waƙoƙinsu ga wani Basarake guda a matsayin uban gidansu ba tare da sun haɗa shi da wani ba, in kuwa sun haɗa ɗin to sai da izininsa ko wani amininsa kuma da sharaɗinsa. A duk lokacin da wani Basarake ya riƙi wani makaɗi a matsayin mawaƙinsa na fada to fa cin wannan makaɗi da shansa da suturarsa da muhallinsa da ɗawainiyarsa duk sun rataya ne kan wannan uban gida nasa”.
Gusau (2023b) ya kawo cewa, “ Kalmar Ubangida tana da tsagi biyu Uba+ngida, an haɗa kalmomin biyu da alamar (–n) mai nuna wata dangantaka. An kuma ɗauki kalmomim su zama ɗaya a wata ƙa’ida ta rubutu na daidaitacciyar Hausa (Galadanci, MKM
1976).
Uba kalma ce ta suna wato Mahaifi ko
Shugaba ko Jagora. – n gida kuwa
wani haɗi ne mai nuna dangantaka (CNHN,
2006:461).
Ma’anar Kalmar Ubangida ta fuskar
fannin ilimi ko isɗilahi wato bisa ganowa ko ƙiyasin Malamai ko masana ko manazarta ita ce:
Shugaba ko Sarki ko wani jami’i ko attajiri ko masani ko ma’aikaci ko soja
ko ɗansiyasa ko sauransu, manya, masu
kamala, masu matsayi ko wata daraja, waɗanda kuma makaɗin baka ya yi wa wata waƙar baka ta Hausa bisa daidaitaccen shiri da rauji da
rerawa da sadarwa (Gusau, S.M. 2008:459)”.
A fagen kiɗa da waƙa, Makaɗa Sa’idu Faru yana da iyayen gida aƙalla guda huɗu, tun daga fara waƙarsa zuwa rasuwarsa. Ga dai jerin sunayen iyayen gidan
Makaɗa Sa’idu Faru daga na farko zuwa na ƙarshe, kamar haka:
1. Dagacin
Banga, Sarkin yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar. Ya yi Sarauta daga
1934-1960).
2.
Sarkin Kiyawan Ƙaura-Namoda, Alhaji Abubakar Garba. Ya yi Sarauta daga
1952-1960.
3.
Sarkin Zamfarar Zurmi, Alhaji Suleiman Muhammadu Sambo. Ya yi Sarauta daga
1991-1971/2
4.
Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo. Ya yi Hakimta daga 1956-1958. Daga
baya aka yi masa sarautar Sarkin Musulmi.
Makaɗa Sa’idu Faru ya ci
gaba da riƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a matsayin uban
gidansa har rasuwarsa. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Muhammadu Macciɗo waƙoƙi masu tarin yawa
kuma masu ma’ana.
Bayan
waɗannan iyayen gida na
Makaɗa Sa’idu Faru, ya
tsallaka wasu masarautu kamar Kano da Wurno da Kwantagora da Dutsin-Ma da
sauran ƙasashe ya yi musu kiɗa.
1.1.4 Rasuwar Makaɗa Sa’idu Faru
Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a shekara ta
1987. Idan aka yi la’akari da shekarar haihuwarsa, wanda shi Sa’idu Faru ya
ayyana da kansa a 1976, wato an haife shi ne a 1937. Ya rasu ke nan yana da
shekara 50. Idan kuma aka yi la’akari da cewa an haife shi ne shekarar 1932,
kamar yadda Dutsin-Ma 1981 da Gusau (1988 da 2011) da Furniss (1996) suka kawo,
to Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu
yana da shekara 55 ke nan a duniya. Idan kuma aka yi la’akari da abin da
Ibrahim Ɗanmadami ya faɗa a 2019 da Ibrahim Sa’idu Faru a 2020 da
Jaridar Leadership Hausa 2020 cewa an haifi Sa’idu Faru ne a shekara ta
1915/16, ya rasu ke nan yana da shekera 71/72 a duniya. Allah shi ne Masani.
Bayan rasuwar Makaɗa Sa’idu Faru, ya
samu magada a fagen kiɗa da waƙa guda biyu.An samu ƙanensa Mu’azu, kuma
bayan rasuwar Mu’azu, sai Ibrahim ɗan Sa’idu Faru ya ci gaba da jan ragamar
gidan a fagen kiɗa da waƙa har zuwa yau.
1.2 Ɗan Waƙa A Waƙar Baka Ta Hausa
Ɗan waƙa wani mazubi ne da
Makaɗan baka na Hausa suke
zubawa, su kuma shirya manya da ƙananan saƙonni a cikinsa.
Wannan ya sa ɗan waƙa ya zama babban
ma’auni da masana da manazarta suke auna hikima da fasaha da kuma ƙwarewar makaɗi ta kallon yadda
yake ɗan shirya waƙa. Ɗan waƙa shi ne ruhin duk
wata waƙar baka ta Hausa. Ashe ke nan ɗan waƙa ya zama tamkar wata
ma’ajiyar saƙonni ne, manya da da ƙanana waɗanda suke fita daga
zuƙatan
Makaɗan baka na Hausa su
kuma zuba su, tare da shirya su a cikin ɗan waƙa domin isarwa ga waɗanda abin ya shafa,
ta hanyar rerawa da gwamawa da amon kiɗa.
Ɗa
(tilo), ɗiya (jam’i), zubi ne
da ake yi a shirya saɗara ko saɗaru da za su iya ƙunsar ƙaramin saƙo ɗaya ko biyu ko fiye
da haka. Ɗa yakan ƙunshi furucin jagora + furucin ‘yan
amshi (+ƙulli +ƙari) ko furucin jagora kawai ba tare
da furucin ‘yan amshi ba (+ƙulli−ƙari), haɗe da gindin waƙa (+ƙulli+/−ƙari+G/waƙa), ko ba haɗe da gindin waƙa ba (+ƙulli−ƙari−G/waƙa) (Gusau, 2014:16).
Gusau (2003) ya nuna cewa, “ Ta fuskar
zubin ɗiyan waƙa ne mai nazari zai
kula da yadda makaɗi yake ƙulla carbin tuninsa
da kuma yadda yake saƙa kalmomi da ƙananan saƙonni a cikin jimloli
na ɗiya. Za a lura ko
zubin ɗiyan ya ƙunshi saƙar zana ne ko kuwa saƙa ce mai sauƙi, sannan kuma a
bayyana yadda makaɗi yake ƙulla dangantaka a
makamantan waɗannan abubuwa”.
Ashe ke nan, ɗa a waƙar baka shi ne tarin
saɗaru waɗanda aka samar da su
ta hanyar furucin jagora da na ‘yan amshi, bisa tsari da ƙa’idar daidaita rauji
da karin-murya da amsa-amon kari, waɗanda kuma suke da manya da ƙananan saƙonni a ƙwansonsu. Ɗan waƙa ba shi da ƙayyadaddun saɗaru. Saɗarun ɗan waƙa suna iya kasancewa
gajeru ko dogaye, kaɗan ko masu yawa. Ana
rabe tsakanin ɗa da ɗa ta rera gindin waƙa ko ta sautin kiɗa.
1.3 Ma’ana A Ɗan Waƙar Baka
Ta Hausa
Ma’ana (tilo)
ma’anoni (jam’i) saƙonni ne da makaɗan baka na Hausa suke ƙullawa a cikin
kalmomi ko saɗaru domin su samar da
gundarin ɗan waƙa, kuma su rera shi
tare da sadar da shi ga wanda abin ya shafa. Akan samu furucin ma’ana a ɓangaren jagora ko
‘yan amshi.
A waƙar baka ta Hausa, duk
wata kalma ko saɗara da makaɗi ya yi amfani da ita
a waƙarsa, tana ɗauke da wata ma’ana ta daban, ƙarama ko babbar
ma’ana. Wannan ya sa Gusau (2003 da 2023) ya tsara hanyoyin da mai nazari zai
yi amfani da su wajen yin nazarin ɗan waƙa ta fuskar ma’ana da
tsari. Wato a tantance yawan saƙonnin da ke cikin ɗan waƙa ta hanyar ƙirgan ma’ana.
1.3.1 Matakan Bayyana Ɗan Waƙa
A wajen nazarin ɗan waƙa, ana bayyana ɗan waƙa ne ta amfani da waɗannan kalmomin fannu
na hawa da sauka da ajewa da saukar sauka da Gusau (2003 da 2023) ya
tsara domin a tantance furucin ma’ana ta jagora da kuma ta ‘yan amshi a
cikinsa.
i- Hawa
Hawa furucin da aka
fara yi ne wajen gabatar da ma’ana a cikin saɗara ɗaya ko fiye da haka (Gusau, 2023:40).
Hawa furuci ne na kalma ko saɗara ɗaya ko fiye da ɗaya a ɗan waƙa. Wato duk wani
furucin ma’ana da jagora ya yi a cikin ɗan waƙa shi ake kira da
hawa. Mafi yawan waƙoƙin baka na Hausa, furucin jagora (hawa) shi yake zama
furucin ma’ana na farko a ɗan waƙa.
ii- Sauka
Gusau (2003 da 2023)
yana cewa “sauka furuci ne wanda ake iyar da ƙarasa ma’ana da shi.
Shi ma furucin sauka ana yin sa a cikin saɗara ɗaya ko fiye da ɗaya ba tare da ƙayyade yawansu ba”.
Ashe kenan, sauka na nufin furucin da ‘yan amshi suka yi a cikin ɗan waƙa. Furucin ‘yan amshi
(sauka) yakan zo ne a matsayin wani ɓangaren ma’ana wadda jagora ya faro ta ɓangarensa, kuma suka ƙarasa iyar masa da
ita. Furucin ‘yan amshi na ma’ana (sauka) yana zuwa ne bayan furucin ma’ana ta
jagora.
iii- Ajewa
Ajewa wuri ne inda
ma’ana take numfasawa (Gusau, 2023:41). Ajewa na nufin furucin jagora ko na
‘yan amshi da yake jan ma’ana kuma ya ƙara mata tsayi domin
ta ƙara
numfasawa yayin da ta zo gangarar ƙarewa. Idan jagora ko
‘yan amshi suka faro wani furucin ma’ana daki-daki har ya zo inda za ta ƙare, to kafin ta ƙare ɗin, sai su ƙara ƙulla wata ma’anar a
cikinta a matsayin gini a kan waccar ma’ana ta farko. Wannan ita ce ajewa a taƙaice.
iv- Saukar Sauka
Saukar sauka wuri ne
inda ma’ana ta ƙare kwata-kwata, wato wurin da aka gama sauke ma’ana,
musamman bayan ‘takidi’ ko ‘ajewa’ (Gusau, 2023:41).
1.3.2 Ƙididdigar Ma’ana a Ɗan Waƙa
Ƙididdigar ma’ana na
nufin ƙirgan ma’ana da ɗan waƙa ya ƙunsa ta yin amfani da
wasu alamomi. Ɗan waƙa yakan ƙunshi ma’ana ɗaya ko fiye da ɗaya. A cikin mafiya
yawan ɗan waƙa, kowace ma’ana tana
da rukunoninta. Gusau (2023) yana cwa “Ta ma’aunin ƙididdiga kuma ana
amfani da waɗannan alamu ne na ƙwayoyin sauti don
fitar da shi a ɗan waƙa kamar haka; [A]-
[Z], amma banda [Ɗ]= ana ƙirga yawan ma’ana wato ƙaramin saƙo ne da su”. Haka
kuma, ana ƙirga rukunonin ma’ana ta amfani da lambobi kamar haka; A1
A2 A3 (wannan zubin rukunonin ma’ana ne a ɗan waƙa mai ma’ana ɗaya). Haka kuma, ɗan waƙa mai ma’ana biyu,
ana ƙirga rukunoninta ne da A1 A2 A3
B1 B2 B3. Wato kawace ma’ana tana rukunoni uku
kenan. Haka abin zai ci gaba da kasancewa gwargwadon yadda makaɗi ya tsara yawan saƙonni a ɗan waƙa. Za a iya yin ƙididdigar ma’ana ta
zahirin da kuma baɗinin matani. Wannan
takarda ta yi amfani da ƙididdigar ma’ana ta zahirin matani domin taƙaitawa.
2.1 Matakan Ƙulla Ɗan Waƙa
Yawancin
makaɗan baka na Hausa,
sukan ƙulla waƙoƙinsu ne ta hanyar ƙire ko shiryawa.
Gusau (2014) ya nuna cewa, waƙoƙi na ƙire, waƙoƙin baka ne waɗanda ake gudanar da
su kai tsaye kuma a nan take. A tsari na ƙire, ana so kawai a
fahimci wanda ko abin da za a tsara wa waƙa, daga nan, sai a bi
ta waɗannan matakai na
aiwatar da matani nata a rera ta:
a. Tunani
na nan take a ƙwaƙwalwa;
b. Zaɓen kalmomi kai tsaye
a ƙwaƙwalwa;
c. Samar
da rauji da karin murya;
d. Kiɗa da daidaita shi da
rauji;
e. Gina
gindin waƙa da ɗiyan waƙa;
f.
Gina ɗiyan waƙa babu gindin waƙa (Gusau, 2014:16).
Haka kuma, Gusau (2014) ya ƙara ayyana yadda ake
samar da waƙoƙin baka na Hausa ta hanyar shiri. Yana cewa, waƙoƙi na shiri su ne waƙoƙin baka waɗanda ake tsayawa a keɓe, kuma a natse a
tsattsara su ta yadda za a zaɓo musu kalmomi da jumloli a ka ko a rubuce, a samar da
murya bisa rauji mai nagarta, sannan a ɗora kiɗa a kuma bi ta da rerawa. Su waɗannan waƙoƙi na shiri suna da
halaye kamar haka:
a. Za
a fara tunaninsu a ƙwaƙwalwa;
b. Sannan
a zaɓo kalmomi da jumloli;
c. A
ɗora rauji ta la’akari
da karin murya ko gurbin murya da hawa da sauka da faɗuwar muryoyi (Gusau,
2014:15).
Makaɗa Sa’idu Faru yakan
yi hangen nesa, ko kuma ya samu bijirowar tunani a dalilin wasu abubuwa da suke
kewaye da shi, kuma su yi tasiri a zuciyarsa. Haka kuma, yakan shirya waƙa ne a take ko a
shirye ta hanyar zuzzurfan tunani ta kalmomi da gaɓoɓin da zai samar,
domin ya samar da ingatattun saɗaru da ɗa ko ɗiyan waƙa ta hanyar tunanin[4]
kalmomin da za su dace da waƙar da zai samar. Daga bisani kuma sai
ya samar da gangar jikin waƙar ta bin wasu matakai na samar da gaɓoɓin kalma da kalmomi da saɗaru da ɗan waƙa da kuma sauran ɗiyan waƙa,
sannan ya ta da cikakkiyar waƙa.
Ga
matakan ƙulla ɗan waƙa na Makaɗa Sa’idu Faru bisa
bishiyar tarke ta Gusau (2019) a ƙasa:
2.1.1 Nau’o’in Ɗan Waƙa
Akwai wasu matakai waɗanda Makaɗa Sa’idu Faru yake bi
domin ya shirya ɗiyan waƙoƙinsa bamabanta.
Mataki na farko shi ne, yana samar da gajeren ɗan waƙa mai ƙunshe da ma’ana tasa
ta kansa. Mataki na biyu kuma, yana samar da matsakaicin ɗan waƙa mai ɗauke da cikakkiyar
ma’ana ko gutsiren ma’ana. Mataki na uku kuma, yana samar da dogon ɗan waƙa wanda yake ɗauke da cikakkiyar
ma’ana. Wato yana gina ɗiyan waƙoƙinsa bisa mabambantan
ma’anoni. Wani ɗan waƙar ba ya dogara da
wani ɗan waƙar domin cikar
ma’anarsa. Sai dai a matsakaicin ɗan waƙa akan iya samun
wanda ma’anarsa ba ta cika har sai ta sauka
zuwa ga wani ɗan. Makaɗa Sa’idu Faru yana
tsara mabambatan ɗiya dangane da saɗaru da kuma ma’ana.
Amma ana samun saukar ma’ana tsakanin saɗaru. Sannan ba ya yin
kwangaba-kwan-baya wajen shirya ma’anonin da ɗiyan waƙoƙinsa ke ƙunshe da su. Misali;
idan aka duba waƙar ‘Kana Shirye
Baban ‘Yanruwa’, ta Muhammadu Macciɗo, za a ga cewa tana da ɗiya ashirin da tara
(29), kuma ya tsara ta ne bisa gajeren ɗan waƙa da matsakaici da
kuma dogon ɗan waƙa. Amma kowane ɗa zaman kansa yake
wajen cikar ma’ana, idan ban da ɗa na goma sha uku zuwa na goma sha huɗu (13-14) da ɗa na ashirin zuwa na
ashirin da ɗaya (20-21) waɗanda aka samu saukar ma’ana.
2.1.1.1 Gajeren Ɗan Waƙa
Gajeren
ɗan waƙa shi ne ɗan waƙar da yake ƙunshe da saɗaru biyu, (2) ko uku
(3) kacal a cikinsa, dogaye ko gajeru, masu alaƙa da juna ko akasin
hakan ta fuskar ma’ana. Haka kuma, yakan ƙunshi gajeruwar
ma’ana mai faffaɗan saƙo, cikin gajerun
kalmomi masu kaifafa tunani da sanya zauƙi ga masu sauraro.
A mafi
yawan lokuta, Makaɗa Sa’idu Faru yakan
shirya gajeren ɗan waƙa mai cin gashin
kansa wajen ƙunsar ma’ana. A gajeren ɗan waƙa ana samun alaƙar ma’ana a tsakanin
saɗarunsa, amma ba a
samun saukar ma’ana a tsakanin ɗa da ɗa a cikinsa. Ga wasu misalan gajerun ɗiya a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru:
a-
Ƙulli: Baba yau da kai kuma gobe da kai,
Ƙari: Ko jibi ma gogarma da kai.
Waƙar ‘Bajimin gidan Abdullahi’ ta
Alhaji Ado Bayero, ɗa na 8)
Idan aka kalli
misalin da aka kawo a sama, za a ga ɗan waƙar saɗaru biyu ke gare shi.
Amma kuma suna ƙunshe da kalmomi masu kaifafa tunani da sanya shauƙi da zuga. Alal
misali, a farko ya yi amfani da kalmomi sauƙaƙa kuma na ilhama, waɗanda suke na zuga da
yabo tare da nuni ga jimawar Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a kan karagar mulki.
Kuma kafin ɗan waƙar ko bayansa, babu
wata ma’ana da yake jira da za a haɗa ta da shi kafin cikar ma’anarsa. Ma’ana,
duk saƙon da Makaɗa Sa’idu Faru yake son isarwa, ya isar da shi
a cikin saɗaru biyu kacal. Kamar
yadda aka yi bayani, a cikin ɗan waƙar ya yi yabo da zuga da kirari da
isharar jimawa ga marigayi Alhaji Ado Bayero a kan karagar mulki. Za a ga kuma
hakan idan aka dubi tsakanin rasuwarsa da rasuwar Alhaji Ado Bayero, an samu
shekaru aƙalla ashirin da bakwai (27).
Ga wani ƙarin misalin kamar
haka;
b.
Ƙulli: Na Sarkin Gobir Ahmadu,
Ƙari: Ci fansa gagon Sarkin Ƙaya.
(Waƙar ‘Kana Shirye Baban ‘Yanruwa’ ta Muhammadu
Macciɗo da na 2)
Haka nan, shi ma
wannan ɗan waƙa mai saɗaru guda biyu a
cikinsa Makaɗa Sa’idu Faru ya fito
da saƙonsa na kirarin nasaba da yabo da kuma zuga. Haka kuma, a
ɗan waƙar da yake biye da
shi za a ga wata ma’anar ta daban yake magana a kanta. Wannan ya sa Makaɗa Sa’idu Faru, ya
gina wannan gajeren ɗan waƙa mai faffaɗar ma’ana da ma
zurfi.
2.1.1.2 Matsakaicin Ɗan Waƙa
Matsakaicin ɗan waƙa, ɗa ne wanda makaɗan baka na Hausa suke
shirya shi bisa tsari da ƙa’ida ta daidaita rauji da amsa-amon kari, wanda kuma
yake ƙunshe da saɗaru huɗu (4) zuwa goma (10). Matsakaicin ɗan waka, yana iya
zama mai kammalalliyar ma’ana ko mai gustiren ma’ana. Haka kuma, ɗa ne wanda ya ƙarfafa ma’ana da
haifar da alaƙar ma’ana tsakanin saɗaru da kuma saukar ma’ana a wani lokacin. Ga
wasu misalai na matsakaicin ɗan waƙa a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Ƙulli: Laifi yaro shi yi ƙwiya,
: Laifin babba shi yi rowa,
: Ina ƙaunarka Muhammadu,
: Na tabbata ƙamna ta
kakai,
: In ka niyyab ba mu dawakuna,
: Sabnan bafade sara yakai,
: Ya ce ko ka ba mu dawakuna,
Ƙari: Ran da salla ka tashi ƙaura mukai.
(Waƙar ‘kana shirye
baban ‘yanruwa’ ta Muhammadu Macciɗo, ɗa na 28).
Wannan ɗan waƙa, ɗa ne mai kammalalliyar
ma’ana wanda bai dogara da wani ɗan waƙar ba wajen cikar
ma’ana. Tun a saɗara ta ɗaya zuwa ta biyu, Makaɗa Sa’idu Faru ya fara
soma furta ƙwayar ma’anar ɗan waƙar. A saɗara ta biyar da bakwai
kuma, ya ci gaba da saƙa ma’anar ɗan waƙar, sai a saɗara ta takwas ma’anar ɗan waƙar ta cika kuma daga nan ta ƙare. Ashe ke
nan, idan aka dubi wannan ɗan waƙa ta fuskar yawan saɗaru, za a ga cewa
matsakaicin ɗa ne, ta
fuskar ƙunsar ma’anar kuma, ɗan waƙa ne kammalalle, wato ɗa ne mai dogara da kansa
wajen cikar ma’ana.
Amma akan iya samun matsakaicin ɗan waƙa wanda yake mai saukar ma’ana[5]. Misali, ga wani ɗan waƙa mai gutsiren ma’ana a ƙasa:
Ƙulli: Baba na Shamaki mai hana noma,
Ƙari: Baba ganɗon gabas raba kaya,
Ƙulli: In ga na Shamaki mai hana noma,
Ƙari: Baba ganɗon gabas raba kaya.
(Waƙar “Kana Shirye Baban ‘Yanruwa’, ɗa na 11)
Wannan
shi ma matsakaicin ɗan waƙa ne wanda Makaɗa Sa’idu Faru ya ƙulla shi, amma bai
cikasa iyar da ma’anarsa ba sai da ya haura zuwa wani ɗan daban. Idan aka yi
duba na tsanaki za a ga Makaɗa Sa’idu Faru, ya fara ɗan waƙar ne da koro kirari
da yabo da zuga a matsayin shimfiɗa, domin janyo hankalin masu sauraro ga abin
da zai faɗa. Ga cikon ma’anar
wancan ɗan waƙar da aka kawo a
sama:
Ƙulli:
Hwatad da nikai gun Rabbana,
Ƙari:
Ka gaji gidan Sarki Abu,
: Don
darajjar Halifad Ɗanhodiyo,
Ƙulli:
Ka gaji gidan Sarki Abu,
Ƙari:
Don darajam muƙaman Mamman Tukur.
(Waƙar ‘Kana Shirye Baban ‘Yanruwa’, ɗa na 11-12)
Idan aka yi la’akari
da yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya
rarraba saƙon da yake son isarwa a wannan muhalli a cikin ɗiya guda biyu, za a
gane ashe wannan ɗan waƙa na farko da aka
kawo ɗan waƙa ne mai gutsiren
ma’ana. Dalili kuwa shi ne, makaɗin ya fara ƙulla saƙonsa ne a ɗan waƙa na 11, saɗara ta farko, amma
bai cika shi ba har sai da saƙon ya sauka ya gangara zuwa ɗan waƙar da yake biye da
shi, wato ɗa na 12, saɗara ta ɗaya zuwa ta biyu.
Wannan ya sa za a iya kiran wannan nau’in ɗan waƙa, ɗan waƙa mai gutsiren ma’ana,
saboda an samu saukar ma’ana a cikinsa.
2.1.1.3 Dogon Ɗan Waƙa
Dogon ɗan waƙa, ɗa ne wanda Makaɗan baka na Hausa suke
sakin linzamin tunaninsu wajen shirya saɗarorinsa da saƙa saƙonni masu yawa a
cikinsa, ba tare da sun numfasa ba har zuwa wani ɗan lokaci. Wannan ya sa dogon ɗan waƙa yake iya ƙunsar saɗaru goma sha ɗaya (11) zuwa hamsin
(50) har ma zuwa ɗari biyu (200). Haka
kuma, ɗan waƙa ne wanda yake ƙunsar dunƙulallun ma’anoni a
cikinsa. Ma’ana, ba a samun saukar ma’ana ta tsakanin ɗa da ɗa, sai dai a tsakanin
saɗaru. Ga misalin wani
dogon ɗan waƙa a ƙasa:
|
Ƙulli |
: Za ni gidan
rediyo na Sakkwato, |
|
Ƙari |
: In yabon Jihab
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Za ni gidan
rediyo na Kaduna, |
|
Ƙari |
: In yabon Jihab
birnin Kano |
|
Ƙulli |
: Za ni gidan rediyo na Ikko, |
|
Ƙari |
: In yabon Jihab
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Za ni gidan rediyo na Niger, |
|
Ƙari |
: In yabon Jihab
birnin Kano, : Nijeriya ta Arewa
babu Jiha irin birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: In, |
|
Ƙari |
: Nijeriya ta Arewa
babu Jiha irin birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Lallai shina
birnin Kano, |
|
Ƙari |
: Yadi shina birnin
Kano, |
|
Ƙulli |
: Kuɗi shina birnin
Kano, |
|
Ƙari |
: Ilimi shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Kyauta tana
birnin Kano, |
|
Ƙari |
: Mulki shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
motoci, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin jirgin ƙasa, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
mashin hawa, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin famfan ruwa, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
motoci, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin keken
hawa, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin kwaɗon ɗaki, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin ƙera
makamai, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano. |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
tasoshi, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
kwanoni, |
|
Ƙari |
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Injimin yin
shirya agogo, |
|
Ƙari
|
: An ce shina
birnin Kano, |
|
Ƙulli |
: Babban abincin
Arewa, |
Ƙulli
|
: Babban abincin
Arewa, |
|
Ƙari |
: Gero shina birnin
Kano, |
|
|
: Gero yana birnin
Kano, |
|
Ƙari |
: Dawa tana birnin
Kano, |
|
Ƙulli
|
: Dawo tana birnin
Kano. (Waƙar
‘Tsakin Tama na Abashe’ ta Tijjani
Hashim, ɗa na 7) |
|
Ta fuskar saɗarun ɗiya, wannan ɗan waƙa yana da saɗaru guda arba’in da
biyar (45). Ashe ke nan dogon ɗan waƙa ne, idan aka yi duba da yadda aka
kasa nau’o’in ɗiyan waƙa ta baka. Idan aka
yi wa wannan ɗan waƙa duba na tsanaki, za
a ga ya ƙunshi babban saƙo guda ɗaya a cikinsa, wato,
yabon Jihar Kano, duk da dai yana da rukunonin ma’ana da wasu ƙananan saƙonni aƙalla guda uku. Wato,
rukunin yabo ta fuskar dukiya da ta fuskar kayayyakin kimiyya da fasaha da kuma
ta fuskar albarkatun kayan noma.
Kamar
yadda bayanai suka gabata, dogon ɗan waƙa yana iya ƙunsar ma’ana ɗaya ko fiye. Saboda
haka, wannan ɗan waƙa ma Makaɗa Sa’idu Faru ya ƙulla ma’anarsa ne a
saɗara ta ɗaya, kuma ya ƙare ta kwata-kwata a
saɗara ta ƙarshe, wato ta
arba’in da biyar (45). Idan kuma aka dubi ɗan waƙar da yake biye da
shi, za a ga sabuwar ma’ana ta daban makaɗin ya ƙulla a cikinsa. Ashe
ke nan ɗan waƙa ne mai
kammalalliyar ma’ana, wato ba a samun saukar ma’ana a cikinsa kamar dai yadda
bayanai suka gabata a baya.
3.1 Tsarin Ɗan Waƙa[6]
Tsarin ɗiyan waƙa na Hausa na nufin
yadda makaɗan baka na Hausa suke
ƙulla
carbin tunaninsu, ta hanyar zaɓen kalmomi da jimloli domin sassaka ƙananan saƙonni a cikinsu ta
yanayi mai tafiyar kura ko mai sauƙi. Haka kuma, ya
danganci irin yadda makaɗa ke ƙulla alaƙa tsakanin saɗarun ɗan waƙa ko ta ‘ɗa’ da ‘ɗa’ ta fuskar saƙonni da suke ƙunshe a cikinsu.
A
tsarin ɗan waƙa na awon baka, ana
samun hawa da sauka da saukar sauka da ajewa.
Ta haka ne ake bambancewa tsakanin furucin jagora da na ‘yan amshi. Akan samu
ma’ana ɗaya ko sama da ɗaya a cikin ɗan waƙa, kuma ya danganta
da yadda makaɗi ya sassaƙa saƙonni a cikinsa.
Ɗan
waƙa
a waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru ya kasu zuwa gidaje biyu: sassauƙan ɗan waƙa da tsattsauran ɗan waƙa.
3.1.1 Sassauƙan Ɗa
Ɗan waƙa mai sauƙi, na nufin ɗan waƙa wanda yake ƙunshe da hawa da
sauka kawai a cikinsa. Kuma ba ya ƙunsar ma’ana sama da
guda ɗaya. Ga misalin ɗan waƙa mai sauƙi a ƙasa:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
: Alhamdu Lillahi duk kun nuhi, |
Sauka |
A2 |
: Rabbul alamina ni nau nuhi, |
Hawa |
A3 |
: Ka san kiɗi ba karatu ba ne, |
Sauka |
A4 |
:Ballantana mui
istigifari in mun gama.[7] (Waƙar
‘Kana Shirye Baban ‘Yanruwa’, ɗa na 3)
|
Wannan ɗan waƙa shi ne ɗa na 3 a waƙar da aka ciro wannan
misali. Idan aka dubi wannan ɗan waƙa, za a ga yana ƙunshe da saɗaru guda huɗu. Sannan kuma, ɗa ne mai ƙunshe da ma’ana guda ɗaya tak, wato
habaici, ma’anar kuma tana da rukunoni guda huɗu. Wato rukuni na ɗaya yana magana a kan
nuni da yarda da Allah. Rukuni na biyu shi ma yana miƙa saƙo ga wasu mutane.
Haka nan rukuni na uku, yana bayyana kiɗa da cewa ba karatu ba ne. Sai kuma rukuni na
huɗu, shi kuma yana nuna
rashin illa idan ba a ambaci Allah ba bayan an gama waƙa. A wajen shirya
wannan ɗan waƙa, jagora ne ya fara
hawa wajen furta saƙo na ɗaya a saɗara ta ɗaya, ‘yan amshi kuma suka sauka a saɗara ta biyu. Haka abin ya kasance a saɗara ta uku da ta huɗu.
Idan aka lura da wannan ɗa, za a ga ɗan waƙa ne mai sauƙi saboda hawa da sauka kawai ya ƙunsa, kuma ma’ana ɗaya ce a cikinsa kawai.
Ga wani misalin ɗan waƙa mai sauƙi a ƙasa:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
: Zama kai a ginshiƙi, |
Sauka |
A2 |
: Zama kai a ginshiƙi, |
|
A3 |
: Ko da an
shekara ruwa. (Waƙar
“Gwabron giwa’, ɗa na 18)
|
Wannan ɗa, a tsarin ɗan waƙa, shi ma ɗa ne mai sauƙi. Ta fuskar ma’ana, ya ƙunshi hawa (masomin ma’na ta ɓangaren jagora) da sauka (ƙarashen iyar da ma’ana ta ɓangaren ‘yan amshi) ne kawai. Ta fuskar tsari kuma, ɗa ne mai ma’ana ɗaya da rukunoni uku.
Ga wani misalin a ƙasa na ɗan waƙa mai sauƙi:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
:Bajimi ɗan gagara gasa amalen
Sarakuna, |
Sauka |
A2 |
:Toron giwa ɗan Abdu ƙanen Ali ɗan Iya, |
Hawa |
A3 |
: Toron, |
Sauka |
A4 |
: Giwa ɗan Abdu ƙanen Ali ɗan Iya. (Waƙar
“Alhaji Macciɗo jikan Mamman,” ɗa na 2). |
Wannan shi ma ɗan waƙa ne mai sauƙi, saboda kasancewar hawa da sauka kawai ya ƙunsa. Kuma ma’ana ɗaya ce a cikin ɗan waƙar kawai, wato kirari. Sai rukunonin ma’ana guda huɗu, wato kirari ta amfani da jinsintarwa da kirarin nasaba
da dabbantarwa da kuma kirarin kambame. A ma’ana ta ɗaya, jagora ne ya fara hawa a gurbin furucin ma’ana ta ɗaya, sai ‘yan amshi suka sauka a furucin iyar da ma’ana a
rukunin ma’ana ta biyu. Sannna sai jagora ya ƙara yin furucin ma’ana a rukuni na
huɗu, ‘yan amshi kuma suka sauka a
rukuni na huɗu.
Ga wani ƙarin misalin a ƙasa kamar haka:
3.2 Tsattsauran Ɗan Waƙa
Ɗan waƙa mai tsauri, shi ne ɗan waƙa wanda yake ɗauke da furucin jagora da na ‘yan amshi na hawa da sauka da saukar sauka
da/ko kuma ajewa. Wato, wanda kuma yake ƙunshe da ma’ana sama da guda ɗaya bisa mabambantan rukunoni. Ga misalin ɗan waƙa mai tsauri:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
: Amadu cika ni aza ni ka ba ni kuɗi in tai Haji, |
Sauka |
A2 |
: In hawo bisa
marsadi ina rabkak kiɗi, |
|
A3 |
: In don kiɗin barkakka da kaya
ban zuwa ko Moriki, |
Hawa |
A4 |
: In
don, |
Sauka |
A5 |
: Kiɗin barkakka da kaya
ban zuwa ko Moriki, |
Ajewa |
B1 |
: Wasu sun yi gidan
rediyo na banza, |
|
B2 |
: Ko sisin kwabo
ba su ba kowa, |
|
B3 |
: Satan Moriki ɗai sukai, |
|
B4 |
: Zama wayo ba
ya fid da taba, |
Saukar Sauka |
B5 |
: In
dai ni sha ta babu daɗi watsawwa nikai, |
|
B6 |
: In tai in biɗo wata inda mai daɗi take. (Waƙar
‘Tsakin Tama na Abashe’ ta Tijjani
Hashim, ɗa na 5).
|
Wannan ɗan waƙa yana ƙunshe da ma’anoni
guda biyu. Ma’ana ta ɗaya na da rukunoni
guda biyar. Wato ma’ana ta ɗaya ita ce roƙo, da rukunin bayyana
son zuwa Hajji da son zuwa Kano da kore wa kai maula da nanata nuni. A wannan ɓangare, akwai furucin
ma’ana a ɓangaren jagora na
hawa guda biyu a saɗara ta 1 da ta 2, da
furucin ƙarasa iyar da ma’ana a ɓangaren ‘yan amshi guda uku a saɗara ta 2 da 3 da kuma
ta 5. Idan aka kalli ma’ana ta biyu kuma, za a ga tana da rukunonin ma’ana guda
shida (6). A nan, an samu nunfasawar ma’ana a saɗara ta shida, rukuni na ɗaya. Sannan sai ‘yan amshi suka sauka a saɗara ta 7-10 a rukuni na 2-4. Haka kuma, an samu ƙarewar ma’ana kwata-kwata ne a saɗara ta sha ɗaya, rukuni na shida.
Haka kuma, an sami wani ɗan waƙa mai tsauri kamar
haka:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
: Shehu gidan, |
Sauka |
A2 |
: Hassan ɗan Mu’azu katakoran
Mutawalle, |
Hawa |
B1 |
: Na gaishe ka da
aikin ilimi, |
Sauka |
B2 |
: Na gaishe ka da
aikin ilimi, |
|
B3 |
: Na kuma gaishe
ka da kyauta, |
|
B4 |
: Hanya ilimi
hanyar mulki, |
|
B5 |
: Hanyar ilimi
hanyar mulki, |
Ajewa |
B6 |
: Ko kyauta ko
sada zumunci, |
Saukar Sauka |
B7 |
: Kowace hanya
anka kasa uku, |
|
B8 |
: Shehu ya
kwashe kashi biyu. (Waƙar
‘ Bajimin Gidan Bello,’ ɗa na 12).
|
Shi ma wannan ɗan waƙa, yana da ma’anoni
guda biyu a cikin saɗaru guda goma, wato
kirari da yabo. Ma’ana ta ɗaya tana da rukunoni guda biyu, wato rukunin masomin saƙo da kuma na kirari.
Za a ga a ma’ana ta ɗayan, jagora ne ya
furta furucin ma’ana a ɓangarensa na hawa,
sai ‘yan amshi kuma suka sauka a saɗara ta biyu a ɓangarensu na sauka. Ma’ana ta biyu
kuma, tana da rukunoni guda takwas. Wato, rukunin yabo ta fuskar ilimi ( da ta
mulki da ta kyauta ) da ta mulki da ilimi da kuma ta kyauta da sada zumunci. A cikin ma’ana ta ɗaya, an samu hawa guda ɗaya a saɗara ta ɗaya da sauka a saɗara ta biyu. Sannan kuma a cikin ma’ana ta biyu, an samu hawa guda ɗaya a saɗara ta uku da sauka guda ɗaya a saɗara ta huɗu zuwa ta bakwas. Sannan sai kuma ajewa, wato nunfasawar
ma’ana a saɗara ta takwas da kuma saukar sauka,
wato inda ma’anar ɗan waƙar ta ƙare duka a saɗara ta tara zuwa ta goma.
Ga ƙarin wani misalin ɗan waƙa mai tsauri a ƙasa:
Ma’ana |
Tsari |
Ɗan Waƙa |
Hawa |
A1 |
:Rashin zuwa Haji
ya sha min kai, |
Sauka |
A2 |
: Baba Shehu ya
ba mu kujera, |
Hawa |
B1 |
: Shehun gidan
Hassan ɗan Mu’azu, |
Sauka |
B2 |
: Katakoran
Matawalle, |
Hawa |
C1 |
; Za a naɗin Sarkin Sudan
Wurno, |
|
C2 |
: Sai ka ga jirgi. |
|
C3 |
: Inda kad diba
sama Sakkwato, |
Sauka |
C4 |
:Kala-kala haw
waje ta hwara isowa, |
Hawa |
C3.1 |
: Sai ka ga jirgi
kala-kala sama, |
Sauka |
C5 |
: Haw waje ta
hwara isowa, |
Hawa |
C6 |
: Amerika ta tafo
naɗinnai, |
Sauka |
C7 |
: Ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C8 |
: Alƙahira, |
Sauka |
C9 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C10 |
: Ƙasar Midiwe, |
Sauka |
C9.1 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C11 |
: Ƙasar Canis, |
Sauka |
C9.2 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C12 |
: (Ivery Coast), Abirika |
Hawa |
C13 |
: Ƙasar Ghana, |
Sauka |
C9.4 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C14 |
: Ko ƙasar
Niger, |
Sauka |
C9.5 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C15 |
: Igala ma, |
Sauka |
C9.6 |
: Ta tafo naɗinnai, ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
C16 |
: Idoma ma, |
Sauka |
C9.7 |
: Ta tafo naɗinnai ga su suna bisa kujera, |
Hawa |
D1 |
: Ɗan manyan duniya uban mai-bariki, |
Sauka |
D2 |
: Ɗan
Bubakar da Amadu kai ka shirin riƙon, |
Hawa |
D3 |
: Sarki, |
Sauka |
D4 |
: Kai ka shirin
riƙon gidan ga, |
Hawa |
D5 |
: Sarkin Sudan na
Wurno zaki, |
Sauka |
D6 |
: Sarkin Sudan
na Wurno zaki, |
|
D6.1 |
: Sarkin Sudan
na Wurno zaki, |
|
D7 |
: Gogarman Shehu
Turaki, |
Hawa |
I1 |
: Kai aka tsoro
Shehu na Ummaru, |
Sauka |
I2 |
: Amma kai ba ka
da tsoro, |
Hawa |
I3 |
: Wanda gajeru suka
tsoro, |
Sauka |
I4 |
: Wanda gajeru
suka tsoro, |
|
I4.1 |
: Wanda gajeru
suka tsoro, |
Hawa |
F1 |
: Duniyar Allah
haka nan take |
Sauka |
F2 |
: Ga wani ya
kwan shina ta murna, |
|
F2.1 |
: Ga wani ya
kwan shina ta murna, |
|
F3 |
: Ga wani ya
kwan shina ta murna, |
Hawa |
F4 |
: Wanda gajeru suka
tsoro, |
Sauka |
F5 |
: Ya kwan yana
ta murna, |
|
F6 |
: Ga wani ya
kwan da hawaye, |
Hawa |
F7 |
: In Allah yay yo
ka maka samu, |
Sauka |
F7.1 |
: In Allah yay
yo maka samu, |
|
F8 |
: Ba mai maishe ka matsiyaci, |
Hawa |
F9 |
: In Allah yay yo
maka tsiya, |
|
F10 |
: Ko kana gidan
Mamudu Alasan, |
Sauka |
F11 |
: Cikin tsiya za ka gamawa, |
Hawa |
F10.1 |
: Ko kana gidan, |
Sauka |
F11.1 |
: Mamudu Alasa cikin tsiya za ka gamawa, |
Ajewa |
G1 |
: Kowa yan bisa
‘yan motatai, |
Sauka |
G2 |
: Kowa yan bisa
‘yan motatai, |
Saukar Sauka |
G3 |
: Allah ya sawwaƙa Mu’azu. (Waƙar ‘Muzakkarin Sarki, ɗa na 10) |
Wannan dogon ɗan waƙa ne, kuma ya ƙunshi ma’anoni guda bakwai bisa
mabambantan rukunonin ma’ana. Wato, ma’ana ta kokantawa da kirari da tarihi da
kirarin nasaba da kirarin jarumtaka da miƙa lamari ga Allah da kuma jirwaye da kamar wanka. Jagora
ya ƙulla saƙonninsa a cikin wannan ɗan waƙa a saɗara ta 1 da ta 3,4,5-7, 9, 11, 13,
15, 17, 18, 21, 23, 25, 27, 29, 31, 33, 37, 39, 42, 46, 49, 52, 53 da kuma saɗara ta 56. Haka nan ‘yan amshi sun yi furucin ƙarasa iyar da ma’ana a
saɗara ta 2, 4, 8, 10, 12, 14, 16, 18,
20, 22, 24, 26, 28, 30, 32, 34-36, 38-40 ,42-44, 46-47, 49-50, 53, 54, 55 da
kuma saɗara ta 57. Sannan a ɗan waƙar an samu furucin
hawa a ɓangaren jagora guda
ashirin da huɗu (24) a cikin saɗarorin guda ashirin
da bakwai (27). Haka kuma, akwai furucin sauka daga ɓangaren ‘yan amshi
guda ashirin da huɗu (24) a cikin saɗarori guda talatin
(30).
Ta fuskar ma’ana
kuwa, ma’ana ta ɗaya tana da rukunoni
guda biyu. Haka nan ita ma ma’ana ta biyu rukunoni biyu gare ta.
Ma’ana ta uku kuma, tana da rukunoni guda ashirin da huɗu (24). A cikinta an samu takidin rukunin ma’ana a rukuni
na biyar (5) a cikin saɗara ta tara (9) da rukuni na sha biyu (12) a cikin saɗara ta goma sha shida (16) da rukuni na sha huɗu a cikin saɗara ta sha takwas (18) da rukuni na sha shida (16) a cikin saɗara ta ashirin (20) da rukuni na ashirin (20) a cikin saɗara ta ashirin da biyu (24) da rukuni na ashirin da biyu
(22) a cikin saɗara ta ashirin da shida (26) da
rukuni na ashirin da huɗu (24) a cikin saɗara ta ashirin da takwas (28).
Haka kuma, ma’ana ta biyu ma tana da rukunoni guda biyar tare da takidin
rukunin ma’ana a rukuni na biyar (5) a cikin saɗara ta arba’in da uku (43). Sannan sai ma’ana ta shida,
ita ma ta ƙunshi rukunin ma’anoni guda goma sha biyar (15). A cikin waɗannan guda goma sha biyar ɗin, an samu takidi a rukuni na uku (3) a cikin saɗara ta arba’in da bakwai (47) da rukuni na tara (9) a
cikin saɗara ta hamsin da uku (53) da rukuni
na sha huɗu zuwa sha biyar (14-15) a cikin saɗara ta hamsin da biyar zuwa hamsin da shida (55-56). Sai
kuma ma’ana ta bakwai, inda aka samu numfasawar ma’ana a rukuni na ɗaya (1) da kuma saukar sauka a rukuni na uku (3) a cikin
saɗarar ƙarshe ta ɗan waƙar.
4.0 Kammalawa
A wannan takarda an nazarci nau’o’in ɗan waƙar baka guda uku: gajeren ɗan waƙa da matsakaici da kuma dogon ɗan waƙa. An yi bayanin yadda Makaɗa Sa’idu Faru yake ƙulla kowane nau’in ɗan waƙa, da ma yawan saɗarun da kowane ɗan waƙa yake ɗauke da su. An kawo cewa gajeren ɗan waƙa yana ƙunsar saɗaru biyu zuwa uku ne kawai, kuma ba a samun saukar ma’ana a cikinsa.
Matsakaicin ɗan waƙa kuma yana ɗauke da saɗaru huɗu zuwa goma, kuma ana iya samun
saukar ma’ana, wato kammalalliya ma’ana ko gutsiren ma’ana. Haka nan, dogon ɗan waƙa ɗan waƙa ne wanda yake ƙunsar saɗaru goma sha ɗaya zuwa hamsin, ko ma zuwa sama da haka. Amma ba a samun
saukar ma’ana ta tsakanin ɗa da ɗa, sai dai ta tsakanin saɗaru. Sannan an nazarci ɗan waƙa ta fuskar tsari da kuma ma’ana. An fitar da tsarin ɗan waƙa mai sauƙi da mai tsauri ta fuskar ƙunsar gundarin saƙo da kuma rukunonin
ma’anoni.
A ƙoƙarin rubuta wannan takarda an gano cewa a ƙarƙashin tsarin ɗan waƙa mai tsauri za a iya samar da wani rukunin ɗan waƙa na daban, mai suna harɗaɗɗen ɗan waƙa, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake samun ƙullin ɗan waƙa mai ɗauke da takidin rukunonin ma’ana da ma na ɗanin rukunonin ma’ana a cikinsa. Haka nan an fahimci cewa
akwai tababa a kan haƙiƙanin shekarar da aka haifi Makaɗa Sa’idu Faru. Gano hakan da wannan takarda ta yi zai sa a ƙara zuzzurfan bincike a
kan rayuwar Makaɗa Sa’idu Faru da ayyukansa na adabi
domin samun matsaya tabbatacciyar a kan shekarunsa na haihuwa da kuma shekarun
da ya kwashe a fagen ayyukan adabi.
Manazarta
1. Ammani, M. (2019). Nazarin Awon
Baka da Aiwatar da Harshe a Waƙoƙin Nafi’u Yakubu Katsina. Kundin Digiri na uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
2. Dunfawa,
A.A. (2004) Zuga a Cikin Waƙoƙin Fada A Cikin Algaita Journal of Current Reseaech In Hausa
Studies. (Vol. 1, sh. 223-235). Kano: Bayero Uniɓersity.
3. Dutsin-Ma,
U.L. (1981). Sa’idu Faru da Waƙoƙinsa. Kundin Digiri
na Ɗaya.
Zariya: Sashen Koyar da Harsuna da Al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello.
4. Funtua,
A.I, da Gusau, S.M. (2011). Waƙoƙin Baka
Na Hausa.
Katsina: Department of Hausa, Federal College of Education.
5. Funtua,
A.I. (2015). Nazari a kan Waƙoƙin Makaɗan Baka na Hausa a
Jihar Katsina. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
6. Furniss,
G. (1996). Peotry, Prose and Popular
Culture in Hausa. USA: Smithsonian Institution Press.
7. Gusau,
S.M. (1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-Yanayensu, Musamman a Ƙasar Sakkwato. Juzu’i
na Biyu. Diwanin Waƙoƙin Makaɗan Fada. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
8. Gusau,
S.M. (2002). Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Kaduna: Benchmark
Publishers Ltd.
9. Gusau,
S.M. (2003 da 2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark
Publishers Ltd.
10. Gusau,
S.M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa.
Kano: Benchmark Publishers Ltd.
11. Gusau,
S.M. (2011). Makaɗa da Mawaƙan
Hausa.
Kano: Usman Al-amin Publishing Company.
12. Gusau,
S.M. (2013). “Mizani Tsakanin Waƙoƙin Hausa na Baka da
Rubutattu”. Takardar da aka Gabatar a taron ƙara wa juna ilimi a
kan harshe da adabi da al’adun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
13. Gusau,
S.M. (2013). Tatsuniyoyi a Rubuce.
Kano: Century Research and Publishing Company.
14. Gusau,
S.M. (2014). Waƙar Baka
Bahaushiya. (The
Hausa Oral Songs). Kano: Bayero Uniɓersity, Inaugural Lecture Series. No: 14.
15. Gusau,
S.M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a
Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.
16. Gusau, S.M. (2019). “Aiwatarwa da Sadarwa a Waƙoƙin Baka na Hausa”.
Takardar da aka gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
17. Gusau, S.M. (2010/2014). “Makaɗan Hausa Jiya da
Yau”. A Cikin Garkuwan Adabin Hausa: A
Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Kano: Jami’ar Bayero ta Kano.
18. Gusau, S.M. (2021). “Ra’in Waƙar Baka Bahaushiya:
Asali da Wanzuwarsa Zuwa Yau 2021: Ra’in Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau”.
Takarda Wadda aka Gabatar. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero.
19. Gusau,
S.M. (2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka (Sabon Bugu). Kano:
WTP Press Printing and Publishing Limited.
20. Haruna,
M.A. (1988). Mawaƙi a Matsayin Mafalsafi”.Kundin Digiri na Ɗaya. Zariya:Sashen
Koyar da Harsuna da Al’adun Afrika,Jami’ar Ahmadu Bello.
21. Kulo,
F. Nalele (2018). Ɗani na ‘Yan Amshi da na Rauji: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa.
Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
22. Lawal,
A. (2017).“Nazarin Salo a Cikin Wasu Waƙoƙin Bara”. Kundin
Digiri na Biyu. Zariya: Sashen Koyar da Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar
Ahmadu Bello.
23. Labaran,
M.M, (2024). Tarken Awon Baka a Wasau Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Kundin
Digiri na Biyu. Kano. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
24. Muhammad,
A.S. (2012). Nazarin Ayyukan Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni (1938-2000).
Kundin Digiri na Biyu. Zariya: Sashen Koyar da Harsuna da Al’adun Afrika,
Jami’ar Ahamdu Bello.
[1] Alu mai kurya Makaɗin Sarakunan Gobir ne wanda ya yi musu kiɗan yaƙi
a lokacin da ake yaƙe-yaƙe. Bayan Turawa sun ci Arewa da yaƙi a shekara ta 1903, sai aka canja
yanayin kiɗan yaƙi da na noma, ya koma kiɗan
fada. Wannan ya sa kakan Makaɗa Sa’idu Faru da mahaifinsa, Abubakar
mai kotso, suka koma kiɗan kotso suna yi wa Sarakunan Maradun
da na Faru da sauran Sarakuna na wannan yanki nasu waƙa.
[2] A
garin Banga ne aka yi jegon cikin Makaɗa Sa’idu
Faru kuma a nan ne aka haife shi
[3] Wannan waƙa ta Sa’idu Faru ta
farko ita ce wadda ya yi wa Sarkin Yamman Faru Alhaji Ibrahim. Gindin waƙar shi ne:
G/Waƙa: Bi da maza Ɗanjoɗi na Iro,
: Iro magajin Shehu Bello.
[4] Tunani a
harshen waƙa wani muhimmin fage ne da ke warware fasalin zalaƙar mawaƙi ko makaɗi wajen
isar da maganganun waƙa ta sigar saƙo ƙarami ko babba
wand aka iya bunƙasa al’umma ta
zamto mai ƙarfi. (Gusau, 2018: sha.11).
Ta hanyar tunani
ne Hausawa suke harhaɗa ƙwaƙwalwa da zuciya da harshe su dinga aiwatar da maganganu
na hikima da na zube da na waƙoƙi… A shiryawa da zuba ƙwayoyin maganganu ko ƙananan saƙonni a ɗiya na waƙar baka, akan yi
tunani ne domin a samar da saƙonni da za su iya
raya al’umma wadda za ta zama mai ƙarfi, mai daraja.
Makaɗan baka na Hausa suna daga cikin rukunonin Hausawa masu yi da aiwatar da
ayyukan adabi waɗanda suke amfani da tunani da hankali da harshe a zubin
waƙoƙinsu.
Mafarin tunani a
wurin Makaɗa ana jin ya fara ne ta yi wa kai tambayoyi a kan
tambayoyi kan manufa da muradan shiryawa da ƙulla ɗiya a waƙar kamar. A kan me za a yi waƙa? Me za a yi wa waƙa ko abin da za a yi wa waƙa? Me ya sa z a a faɗi kaza? Idan aka ce kaza, za a iya ƙarawa da kaza? Haka dai Makaɗi mai tunani zai dinga tambayar kansa a kan matakan
rayuwar mutum da hidimominsa da wasu abubuwan da za a yi faɗakarwa a kansu na yi ko bari da zimmar a fahimci yadda za
a iya taimakawa da shawarwasi cikin maganganu na tunanin waƙa. (Gusau, 2018: sh. 15-16).
[5] Saukar ma’ana wani yanayi ne da makaɗi yake fara ƙulla
saƙo a cikin wani ɗan waƙa,
amma ba zai cika saƙon ba har sai
ya tsallaka izuwa wani ɗan waƙar (da yake ƙasansa)
daban, bayan rera gindin waƙa
ko amon kiɗa.
Saukar
ma’ana ta saɗara, ita ce makaɗi ya fara ƙulla
wata ma’ana a cikin saɗara ɗaya
amma ba zai cika ma’anar ba sai a saɗarar da ke biye da ita.
[6] Tsarin ɗan
waƙa tamkar rassa ne na itaciya wadda ake
fara hawowa daga gindi kuma a sauka ta kansa… (Gusau, 2003:33).
[7] A wajen nazarin tsarin ɗan waƙa,
ana ja wa furucin ‘yan amshi layi, amma ba a ja wa furucin jagora (Gusau, 2003
da 2023).
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.