Sharudan Yin Layya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam Menene Sharuddan Yin Layya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Daga Ummu Salamah (R.A) cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace:" Idan kuka ga jinjirin watan Zhul hijjah kuma ɗayanku yana da nufin yayi layya, to ya kame daga aske gashinsa da kuma yanke ƙumbarsa. Muslim

    A wata riwayar: "Kar da ya cire gashinsa ko wani abu na fatan jikinsa.

    Sharuɗan layya guda shida ne

    1. Abunda za'ayi layyar dashi ya zama yana daka cikin dangin dabbobin ni'ima, Sune: raqumi da saniya da awaki, tunkiya da akuya, Saboda faɗin Allah maɗaukakin Sarki

    وَلِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنَا مَنسَكًا لِّيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّن بَهِيمَةِ الْأَنْعَامِ فَإِلَٰهُكُمْ إِلَٰهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ الْمُخْبِتِينَ

    Kuma ga kõwace al'umma Mun sanya ibãdar yanka, dõmin su ambaci sũnan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbõbin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushãra ga mãsu ƙanƙantar da kai. (Suratul Hajji aya ta 34).

    2. Abun layya ya zama yakai shekarun da aka iyakance ashari'a, ta kasance ta cika shekara ɗaya idan akuyace ko taure, ko tacika shekara biyu idan tunkiyace ko rago, saboda faɗin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam: (Kada kuyanka layya sai wacce ta cika shekara saidai idan kunsamu quncin tattalin arziki saiku yanka jaz'ah daka jinsin tumaki. Muslim.

    Idan raqumine wanda ya cika shekara biyar zuwa sama.

    Saniya wacce ta cika shekara biyu zuwa sama.

    Tumaki ko akuyoyi wanda ya cika shekara guda.

    3. Dabbar layya ta Kubuta daka Aibuka wanda suke hana ayi layya da ita, guda huɗu ne ga Sunan

    1. Harara garke wacce idonta ɗaya yake akwai matsala, ko wacce idonta zai fari fat wanda ke nuna makanta qarara atare da ita.

    2. Rashin lafiya bayyananniya, kamar zazzaɓi, wanda yake hana dabba kiwo, ko rauni qarara wanda yake lalata namanta, ko wanda yake da tasiri a lafiyarta, ko doguwar rashin lafiya da ta daɗe tanayi wanda yake mata tasiri a lafiyarta.

    3. Gurguntaka mabaiyyaniya,

    4. Wacce bata da Mai.

    Waɗannan Aibuka guda huɗu sune suke hana ayi layya da dabbar da take da ɗaya daka cikinsu.

    Akwai wasu waɗanda suke kamarsu koma suka fisu tsanani, layya bata halatta dasu

    1. Makauniya wacce bata gani sam.

    2. Wacce aka bata magani takecin Abunci sama da ikonta hartai qiba.

    3. Wacce bata iya haihuwa da kanta.

    4. Wacce ta faɗo daka saman wani abu ta samu illah.

    5. Wacce bata iya tafiya, saboda cuta.

    6. Wacce kafarta ta gaba ta guntule, ko ta baya.

    Idan ka haɗa waɗannan aibuka da guda huɗun da suka gabata zakaga aibukan da suke hana layya da dabba sunkai guda goma.

    Hakanan daka cikin sharuddan layya ta zama dabba mallakar mai layyace, ko kuma anyi masa izini yayi layya da ita,

    Layya bata halatta da Abunda mutum bai mallakaba, kamar dabbar da akayi fashinta ko qwacenta, ko wacce aka sato, ko wacce akai qarya aka sameta, ko wacce akaiwa wani kirari na qarya ya bayar da ita, da maka-mantansu, domin bai halatta neman kusanci zuwaga Allah da saɓo ba.

    Layyar wanda aka baiwa kula da maraya tayi, idan yayita da dukiyar marayan, idan Al'ada ta zamto haka, kuma zuciyar marayan zata karaya idan ba'ayi layyar ba.

    Haka layya ta hallata idan aka baiwa mutum wakilci, da dukiyar wakilin da izininsa.

    Kada Abun layya ya zama ya ta'allaqane da haqqin wani, layya bata halatta ga wanda akebi bashi, ya hana bashin yayi layya

    Dole mai layya yayi layya a lokacin da aka iyakance, shine bayan sallar idi izuwa faɗuwar ranar uku ga Sallah.

    Wanda ya yanka layyarsa kafin gama sallar idi, ko bayan faɗuwar ranar uku ga sallah, bashi da layya. Amma Idan Wani uzurine yasa Mutum bai Samu damar yanka dabbar layyarsa ba har bayan faɗuwar uku ga sallah, Kamar wanda dabbarsa ta gudu batare da sakacinsa ba, bai sameta ba har bayan uku ga sallah, ko wanda ya baiwa wani wakilcin yanka masa ya manta, babu laifi da wannan ɗan lokacin yin layyar ya wuce zaka yanka.

    Qiyasi akan wanda yai bacci baiyi sallah ba koya manta Sallar, zai sallaceta idan yafarka ko ya tuna.

    Ya Halatta yanka dabbar layyar cikin dare ko rana, yankawa da rana shine yafi, da kuma ranar idi bayan an sakko daka idin shine yafi falala. Saboda gaggawa wajan aikata Alkairi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.