Ticker

6/recent/ticker-posts

Dabbobin Da Za A Nisanta Wajan Yin Layya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

wanne aibu ne wanda ba'asan samunsu a dabbar layya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sunyi ittifaqi akan waɗannan aibuka

1. Makanta, bayyananniya.

2. Rashin lafiya bayyananne, kamar zazzaɓi wanda yake hanata ci kosha ko kuzarin jiki wanda kana ganin dabba zaka gane batada lafiya. ko rauni wanda yakeda tasiri ga namanta, ko raunin dayake babba wanda yakeda tasiri a lafiyarta.

3. Gurguntaka shine rauni akafa ko karaya wanda yake hana dabba lafiyayyar tafiya.

4. Yamushashshiya bushashshiya wacce batada karfi batada maiko, saboda abunda ya tabbata acikin muwadda lokacinda aka tamabayi Annabi sallallahu Alaihi wasallam waɗanne dabbobine za'a nisanta wajan yin layya dasu? ( Sai yayi Nuni da hannunsa yace huɗu ne:

1. Wacce take da matsala akafarta bata tafiya normal.

2. Mai ido ɗaya wanda yabayyana.

3. Mara lafiyar da rashin lafiyar yabayyana.

4. Wacce take ramammiya mara nama.

Imamu malik yaruwaitoshi acikin muwadda daka hadisin bara'u bin azib.

Awata ruwayar datazo acikin sunan daka bara'u bin Azib yardar Allah takara tabbata agareshi yace: ( Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yamike acikinmu yace dabbobi huɗu basa halatta yin layya dasu.

Malamai sunyi saɓani akan dabba mai yankakken kunne komai yankakkiyar jela, magana ingantacciya ya halatta yin layya da ita, domin naman kunne ko jela baya tauye naman dabba kuma dabba bata cutuwa da rashinsa, itace maganar Abdullahi Ɗan Umar da ibnu musayyeeb da sauransu.

Ya halatta yin layya da ragonda aka ɗandakeshi, Annabi sallallahu Alaihi wasallam yayi layya da raguna manya manya dandaqaqqu, saboda naman layyar yafi daɗi, shine maganar jamhurɗin malamai, ibnu qudama yace: Bamusan wani saɓani akaiba.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments