Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Beli Muhammad Inuwa, Sarkin Mafi Dadewa A Karagar Mulki A Tarihin Najeriya

Sarkin Ya Cika Shekaru 92 bisa karagar mulki, ya kuma yi shekaru 115 a Duniya.

Sarkin Beli Muhammad Inuwa, An Haifeshi A Shekara Ta 1908, Kuma An Naɗa Shi Sarautar A Shekara Ta 1933 A

Matsayin Sarkin Beli Dake ƙaramar Hukumar Shira A Jihar Bauchi.

Ya yi Zamani Da Sarkin Katagum Abdulƙadir 1933 Wanda Ya yi Shekara 12 Karkashin Mulkinsa

Sannan Kuma Ya yi Zamani Da Marigayi Sarkin Katagum Umaru Farouk I Wanda Ya yi Shekara 35 Yana Sarauta.

Sannan Kuma Ya yi Zamani Da Sarkin Katagum Muhammad Kabir Umar Wanda Ya yi Shekara 37 Yana Sarauta.

Sannan Ya yi Zamani Da Sarkin Katagum Na Yanzu Mai martaba Sarki Umaru farouk II shekara 6 yanzu.

A Kanon Dabo kuwa Ya yi Zamani Da Sarakuna 7.

Ya yi Zamani Da Sarkin kano Abdullahi Bayero Wanda Yai Shekara 20 Yana Sarauta.

Sannan Ya yi Zamani Da sarkin Kano Muhammad sunusi na I Shekara 9 yana sarauta.

Sannan Ya yi Zamani Da Sarkin kano Muhammad Inuwa Wanda Ya yi Wata 4 Bisa Karaga.

Sannan Ya yi Zamani Da Sarkin kano Ado bayero Wanda Ya Share Shekaru 52 Yana Sarautar Kano.

Sannan Ya yi Zamani Da Sarkin Kano Sunusi II Wanda Ya yi Shekara 6 Yana Sarauta.

Sai Sarkin Kano Na Yanzu Aminu Ado Bayero Shekara 3.

A Katsina kuwa Ya yi Zamani Da Sarakuna 4.

Ya yi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Wanda Ya yi Shekara 38 Yana Sarauta.

Sannan Ya yi Zamani Da Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo Wanda Ya Shekara 37 Yana Sarauta.

Sannan Ya yi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman 26 Yana sarauta.

Sai Har Yanzu Yana zamani Da Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman Wanda Ya keda Shekaru 15 Bisa Karagar Mulkin Katsina.

Kuma Har Yanzu Sarkin Beli Yana Nan Da Ransa Da Kuma Lafiya.

A Shekarun Baya Bayan Nan, An Samu labarin Mutuwar Sarauniyar England Queen Elizabeth Da Ta Kai Shekaru 70 Bisa Gadon Sarauta, Mutane Da Yawa Suna Ganin Sarauniyar Ta Daɗe Bisa Mulki.

Idan Aka lissafa Tana Shan jinjirarta Sarkin Beli Ya Fara Sarauta, Domin Shekarunta 92 Ta Mutu

Daga:

Ashiru Musa
Karamar Hukumar Shira
Jahar Bauchi, Wakilin AID Multimedia Hausa

Fada

Post a Comment

0 Comments