Don Allah Yakubu Musa idan ana kwatancin mawaƙan Hausa, a bar auna Shata da Rarara, hanyar jirgin daban, ta mota daban.
Yin haka ina ga "daƙile" muhibba da zalaƙa da gwaninta da ɗaukaka da kuma mutuncin da Shata yake da shi a duniyar waƙar Hausa ne. Rarara ba ajin Shata yake ba, ba ma makarantarsu guda ba kamar yadda na sha faɗa, manta ma da zamani, domin ba a taɓa yin wani irin Shata ba, bare wani ya ce ya kai abin kwantancen sa!
Rarara
mawaƙin siyasa ne, ko kuma jam’iyyar siyasa da ke iya biya da riƙe shi na wani
lokaci, bai da gida ko uban gida ko masoyi ko abokin adawa, ba haka tsarin
waƙarsa yake ba, tsarin waƙarsa shi ne inda masu-gidan-rana ke wullawa, shi ya
sa Makka a wurin Rarara ita ce maiƙon da zai biyo bayan basirarsa.
Duk wani
kwatanci da za a yi wa Rarara da irin su Shata ko Ɗanƙwairo ko Narambaɗa ko
Jankiɗi, kuskure ne, haka ma in aka kwatanta shi da mawaƙan siyasa irin ta da,
musamman a zangon farko na kafuwar siyasa, irin su Sa'adu Zungur ko Gambo
Hawaja da yake kwaikwayo, za a ga bai dace ba a sa musu riga iri ɗaya ba. Su ba
kawai aƙida (principle) kaɗai suke da ita ba, ma'aikatan jam'iyya ne, albashi
ake biyan su, ba su taɓa yin 'ridda' ba a rayuwar ginuwar adabinsu.
Haka ba za ka
kwatanta Rarara da ko irin su Awwalu Bunguɗu ko Haruna Aliyu Ningi ba, domin
Awwalu aƙidarsa ta jam’iyya ɗaya ce, shi kuwa Ningi aƙidarsa ta jam’iyya ce,
amma wani yanki na jam’iyyar, shi ya sa za a ga ya yabi jam’iyyar daga baya
kuma ya bahallatse ta da ba ta yi wa sashen da yake goyon baya daɗi ba.
Saboda haka
muna iya cewa ko waɗannan ma ba tsarrarakin Rarara ba ne, ba a gwada su bare a
gwara su ko kuma a ce suna bisa turba ɗaya.
Idan kuna
muka koma ga waɗanda Rarara ke cin kasuwar siyasar wannan zamani da su, irin su
Naziru Sarkin Waƙa da Sani Liya-Liya ko Tijjani Gandu nan ma bambancin a fili
yake, shi ya sa ƙila ake ganin wallen Rarara, musamman da yake shi ɗan
tsilla-tsilla ne, ba kamar Naziru ba da ke da alamun ‘aƙida’ da ba ta cika
bayyana ba, idan aka ɗauke shi a matsayin mawaƙin siyasa. Shi kuwa Sani
Liya-Liya tsalle ɗaya ya yi wa rijiyar waƙar siyasa bai kuma fito ba har yanzu,
ƙila a ce Atiku ya so ya bi, tafiyar ba ta yi armashi ba. Tijjani Gandu kuwa ai
shi ma ba tsarar Rarara ba ne, domin da ka dubi saman kansa ko hular da yake sa
wa ka san aƙidarsa, ke nan yana da matsaya, har kafin ƙila wani abin ya
bayyana.
Saboda haka,
ina ga ya dace a dinga fahimtar kowane tsarin siyasa da yadda mawaƙan siyasa ke
gudanar da rayuwarsu. Ina jin in an yi haka za a fahimci me ya sa Rarara ke yin
abin da ya yi ko yake yi. Idan aka natsu sai a ga ba wani masakin da za a zuba
Rarara a ciki a halin yanzu; shi ba za a kira shi da ‘matar aure' ba, domin ba
ya zaman auren sunna a zahiri, kuma ba za a kira shi da ‘bazawara’ ba, domin da
aure yake yin abin da yake yi; shi kuma ba za a ce da shi ‘budurwa’ ba, domin
an riga an san dawan garin ko kuma a ce a kira shi da ‘kwartuwa’, domin wadda
ke aure ke yin kwartanci, shi ba kuma ‘Ɗan Daudu' ba ne, saboda shi mace ce a
zahiri, mace kuwa ba ta Daudu bare zama ɗa. Ƙila abin da ya fi dacewa da Rarara
bai wuce ‘kilaki’ ba, duk wanda ya biya shi ne nata!
To mene ne
laifin karuwa tun da kuwa kuɗi ake zubawa a kwashi awalajar daga hajarta!
Daga:
Prof. Ibrahim
Malunfashi
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.