Ticker

6/recent/ticker-posts

Dimokuradiyya A Bamagujen Ma’auni

Abdullahi, I. S. S. (2013) “Dimokuraɗiyya a Bamagujen Ma’auni” in Yalwa, L.D. et al (eds) Studies in Hausa Language, Literature and Culture the First National Conference. Centre for the Study of Nigerian Languages Bayero University, Kano. Ahmadu Bello University Press. - Pages 754-763. ISBN: 978-125-426-2

Dimokraɗiyya A Bamagujen Ma’auni

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
Lambar Waya: 0803 6153 050

1.0             Gabatarwa

Ƙoƙarin gane inganci ko rashin ingancin al’amurran yau da kullum yana bukatar bin wata hanya don samun ainihin sakamakon da ya dace. Wannan ne ya sa mutane suka sami damar kallon al’amurra ta yadda za su iya fitar da inganci ko rashin ingancin abu. Wannan ne ya sa aka yi tunanin ɗaukar rayuwar da Hausawa suka gada tun fil-azal a matsayin mizanin gane sahihancin rayuwar da ake ciki a yanzu. A taƙaice, an yi amfani da rayuwar Maguzanci ne wajen auna yanayin tunani na dimokuraɗiyyar Hausawa a wannan zamani. Bamagujen ma’auni a nan yana nufin amfani da yanayin tunani da ma imanin Hausawa a Maguzance a matsayin ma’auni ga tunanin Hausawa na siyasar dimokuraɗiyya.

Maƙasudin wannan maƙala shi ne waiwayen rayuwar Hausawa a Maguzance domin fito da darussan da ’yan siyasar zamani za su amfana da su a kuma tabbatar da tun asali ba ɗabi’ar Hausawa ba ce na irin gurɓacewar halin rayuwa a yanzu wanda ake ikirarin dimokuraɗiyya ce. An bi tafarkin ɗora wannan nazari ne a kan rayuwar Maguzawa domin waiwayen halin ɗa’a da tarbiyyar da ’yanci da Bahaushe ya gada na rayuwa domin ya zama ƙalubale ga ’yan siyasar Hausawa na wannan zamani. Ba gurin wannan nazari ne ya koyar da halaye ko ɗabi’un Maguzawa masu takin saƙa da Musulunci ba. Tunani a nan shi ne mutane su san cewa, Bahaushe bai gaji fitsaranci da handama da ɓatancin da siyasar Hausawa ta zamani ta wayi gari a kansa ba. Wato a san cewa, baya ga kyawawan ɗabi’u da Musulunci ya koya wa Hausawa, hatta da rayuwar gargajiya ta Maguzanci ba ta aminta da wannan yanayi da ake ciki ba.

 

2.0             Fashin Baƙaƙen Tubalan Take

Wannan fasalin ya ƙunshi sharhi ne a kan tubalan taken wannan nazari. A taƙaice, haske fasalin zai bayar dangane da muhimmancin kalmomin da suka gina taken wannan nazari. Waɗannan kalmomi kuwa su ne Dimokuraɗiyyar da Bamaguje.

2.1      Dimokuraɗiyyar

Dimokuraɗiyyar wani tsari ne na shugabanci ko jagorancin jama’a ta hanyar ba su ’yancin zaɓen mutumin da ake ɗammahar an yarda ya yi jagoranci bisa wasu dalilai na musamman. Waɗannan dalilai a ƙumshiyar wannan nazarin sun haɗa da kasancewar mutum ya zama mai kirki, mai riƙon amana, mai kyakkyawar nasaba. Haka kuma akan bukaci ya kasance mai kyakkyawar hulɗa da mutane, kuma maras tabo na laifi ko abin kunya ko tarihin tsoro a rayuwarsa. Irin wannan tsari yana bukatar mutumin da ake tunanin zai yi jagoranci ya kasance yana da kishin mutane ko al’amurra da zai jagoranta. Haƙiƙa kowace al’uma ta duniya za ta yi alfahari da samun shugabannin da suka hau wannan matsayi na cancanta.

2.2             Bamaguje

Kalmar Bamaguje jinsi ne na namiji na kalmar Maguzawa wanda ke ɗaukar ma’anar Hausawan da ba musulmi ba, waɗanda al’adunsu da addinin su na gargajiya yake jagorancin rayuwarsu (Krusius 1915, Fletcher 1929, Ibrahim 1982, Yusuf 1986, Kado 1987, Safana 2001, Akodu 2001, Malumfashi 2002, ….) Bamagujen Ma’auni kamar yadda ya zo a taken wannan nazari, yana nufin rayuwar Maguzanci. Wannan rayuwa ta Maguzanci ta ƙunshi nau’in zamantakewar da Hausawa suka gada kaka da kakanni kafin zuwan musulunci. Rayuwa ce da ke da alaƙa da al’adun da mutanen suka fahimci suna da fa’ida a zahiri. Haka kuma ya ƙunshi rayuwa da yanayin tunanin su da abin da suka yi imani da shi. Wannan rayuwar ita ake son ta zama mizanin awon dimukraɗiyyar Bahaushe ta zamani a wannan nazari.

3.0             Dimokuraɗiyyar Hausawa ta Zamani

Duk da yake ana cewa, idan zamani ya yi riga dole a sa ta, amma Bahaushe ba ya da tunanin ɗaukar riga mai ƙaya da kwarkwata ya sa don kawai zamani ya zo da ita. Duk wanda ya yi haka sai al’uma ta ga wautarsa. Shi kuma ya rinƙa yi wa sauran jama’a kallon sakarkaru saboda ƙin yarda da abin da yake yi a matsayin salon burgewa.

Kawowa yanzu jama’a sun yi nisa da karatun matsalolin damokraɗiyyar Hausawa ta zamani. Wannan karatu ba lallai sai a makaranta ake yin sa ba. Hatta da lebura ko ’yan kasuwa ko ƙauyawa za su iya gaya maka irin matsalolin rashin mutuncin da ke tattare da yayin siyasar zamani.

3.1      Tsayar da Gurɓatattun ’Yan Takara

Wannan shi ne mataki na farko da ke haddasa gurɓatar tsarin Damokraɗiyyar Hausawa ta zamani. A halin da ake ciki, son rai da son ra’ayi su ke jagorantar jama’a wajen tsayar da ‘ɗan takara, ba ainihin abin da ya mallaka na kyakkyawar mu’amala ko halaye da ɗabi’u masu kyau ba. Ɗan takara a wannan zamani zai iya zama wani tsohon ɓarawo ko fasiƙi ko mara mutunci ko mai wata lam’a a rayuwa. Kasancewarsa ɗan wani ko yaron wani zai sa a tsayar da shi. Idan kuma shi ya tsayar da kansa, ba a binciken al’amurransa musamman hanyoyin da yake bi wajen mallakar kuɗaɗen da yake amfani da su wajen fafutikar nema ɗarewa a kujerar mulki. Muddin dai zai bayar, ya ci gaba da bayarwa, to ya tsira.

 

3.2      Aringizon Kuri’un Zaɓe

Wannan shi ma ya zama wani abin tiƙaho a yanayin siyasar Hausawa ta zamani. A koyaushe, ‘yan koren ‘yan siyasa dama suke nema ta kowace hanya su ƙara yawan alƙalumman kuru’u don kawai ‘yan takararsu su sami nasara. An wayi gari, wasu mutane na musamman sun yi ƙaurin suna wajen yin wannan mummunar aiki. Maganar a yi zaɓe a fito da ainihin sakamako na gaskiya ya kau. Hanyoyin da ake bi wajen aiwatar wa wannan nau’i na zalunci ba su da iyaka. A waɗansu wuraren ma ko zaɓen ba a gudanarwa, sai kawai a fitar da alƙalumman ƙarya waɗanda su za su ɗora wanda ake so ya yi dagoranci a kan mulki.

 

3.3      Ta’addanci da Tayar da Husuma a Lokacin Zaɓe

A wuraren da azzaluman ‘yan siyasar zamani suka fahimci jama’a ba za su zura musu ido su ga an yi maguɗi ba, sukan yi amfani da ƙarfin tuwo ko na hukuma wajen ƙoƙarin cin nasara. Ana amfani da matasa marasa mutunci a tayar da husuma, don a firgita jama’a, a yi abin da ake so. Ga talaka da ɗan takarar da ba ya da ƙarfi, ba abin da zai yi illa ya zura ido, daga ƙarshe ya ce Allah ya isa!

3.4      Rashin Dattako

A da idan dattawan unguwa ko na ƙauye ko na gari suka tsayar da magana, ko suka tsawata a kan lamari kowane iri, to akan sami nasarar tabbatar da abin da ya dace. Wannan kusan a ce ya ƙaranta a yau. Dattijai sun zama bakin ganga sai fa in ba a shafa musu mai a baki ba. Dattijo ya ce e yau, gobe ya ce a’a. Wannan ke sa idan irin waɗannan dattijan suka yi magana ba a ɗauka.

3.5             Munanan Ɗabi’un Shugabanni

Kamata ya yi a ce a lokacin da aka ɗora wa mutum nauyin jama’a, zai fara nesanta kansa da abin assha, don tsoron zubewar mutunci. A yanzu har alfahari zaɓaɓɓun shugabanni suke yi wajen ɓatanci ta amfani da wannan damar da aka ba su. Misali:

-                                  Su saci kuɗin hukuma su biya bukatun kansu da na iyalinsu.

-                                  Su yi wa jama’a ƙarya ƙiriƙiri ba a da ikon musantawa.

-                                  Su ɓata ’ya’yan mutane (maza da mata) ta hanyar fasiƙanci.

-                                  Su zalunci al’uma ta hanyar yin ayyuka marasa inganci.

-                                  A yi amfani da su a cuta wa jama’a.

-                                  Su taimaka wajen ɓata zumunci a tsakanin mutane.

-                                  Su taimaka wajen tayar da husuma don hankalin mutane su karkata ga abin da suke aikatawa marasa kyau.

-                                  Su shiga tsafe-tsafe don biyan bukatun rayuwa.

-                                  Su yi amfani da ƙarfin mulki wajen zaluntar talaka.

3.6             Mutuwar Zuciyar Talaka

A farko-farkon shigowar Damokraɗiyya ga Bahaushe, an san talaka ya fi kowa ’yanci. A yau, mutuwar zuciya ta sa ’yan siyasar zamani suka sami cin nasarar yarya wannan ’yanci na talakan da amincewarsa ta ɗora shugaba a kan mulki. Tarihin bore da tabbatar da ’yanci a sassa da yawa na duniya ya tabbatar da talaka ke assasa shi. A yanzu, talakan Bahaushe ya zama abin takawa da murƙushewa. Duk da yake talaka na sane da amanarsa da ake ci, da hakkinsa da ake tauyewa, amma mutuwar zuciya ta sa da zarar an kaɗa gangar siyasa, shi zai fara rawa har da rausayawa. Duk da fahimtar illolin wasu shugabannin siyasar zamani, talaka yana ganin martabar su ta hanyar:

- In sun yi magana ya gaskata.

- In sun yi ƙarya ya yi tafi yana murna.

- Ba a fara taro sai sun zo.

- Ba a gudanar da duk wani lamari sai an nemi su sa albarka.

- Talaka ba ya tunanin wanda zai auri kyakkyawar ’yarsa sai waɗannan mutanen.

- Ba a yin sallar janaza sai an jira su.

- Ba a tayar da iƙama sai an tabbatar da sun shiga sahu.

4.0      Ma’aunan Rayuwar Maguzawa

Duk da kasancewar rayuwar Maguzanci ba abin tinƙaho ba ce ga Hausawa musamman kasancewar akasarinsu Musulmi ne a yau, amma abin waiwaye ne idan ana juyayi da takaicin halin da suka shiga na gurɓataccen yanayi da sunan Dimokuraɗiyya. Wannan fasalin zai tabbatar muna da faɗar nan na Hausawa ke cewa, ‘albasa ba ta yi halin ruwa ba.” Fasalin zai yi ƙoƙarin duban wasu ɗaiɗaikun al’adu na Maguzawa waɗanda ake ganin sun yi takon saƙa da rayuwar dimokuraɗiyya ta Bahaushe ta zamani.

4.1      Shigowar Iyaye a Sha’anin Aure

 A al’adar auren Maguzawa, a daidai lokacin da saurayi ya fahimci budurwar da yake so ta kwanta masa a rai, zai yi ƙoƙarin sadar da iyayensa don su tuntuɓi iyayen budurwar. Waɗannan iyaye nasa ba kai tsaye za su tashi su tunkari iyayen budurwar ba. Za su ɗauki lokaci su tsananta binciken halaye da ɗabi’un wannan budurwar ta yadda za su tabbatar da dacewarta da zaman aure a wannnan gida. Haka kuma Maguzawa suna da ra’ayin cewa, ba kowa za a haɗa zuri’a da shi ba. Wasu gidajen suna da abin kunyar da duk mai tunani ba zai iya barin ɗansa ya auro ’yar gidan ba. A ɓangaren iyayen budurwar ma, akan tsananta wannan bincike a kan saurayin da iyayensa suka zo neman iri. Za su so saurayin da zai aure ‘yarsu ya kasance tarihin zuri’arsa da samartakarsa tsarkakkiya ce. Ya kasance namiji ne a cikin warinsa ta fuskar noma, kokawa da dai sauransu. Ya kasance yana da kyakkyawar sheda daga dattawan da ke kusa. Da zarar aka sami akasin haka, za a gaya wa bududrwar kai tsaye cewa, wannan ba mijin aure ba ne. Haka shi ma a ja hankalinsa cewa, ba gidan da ya cancanta ya nemi aure ba ne.

Idan muka ɗauki wannan a matsayin hanyar da ya kamata a bi wajen tace ‘yan takara a siyasar zamani sai mu ga kai tsaye an saɓa. Mutanen da suka kasance ba su da mutunci, marasa kyakkayawar nasaba su ake wankewa a ɗora su a kan mulki. Ina da za a ce a bi kwatankwacin wannan tsari na tantance ma’aurata na Maguzawa a siyasar zamani, da wani ko mafarkin tsayawa takara ba zai yi ba.

 

4.2      Tsarance

Tsarance wata al’adace a fafutukar neman auren Maguzawa. A taƙaice saurayi ne zai tafi gidan budurwar da yake nema da aure su kwana tare a shimfiɗa ɗaya. Haka ita ma tana iya bin sa zuwa gidan su daga dandali ta kwana a can tare da shi. A irin wannan yanayi ba a ɗammahar wani abu na ɓatanci ya shiga tsakanin waɗannan masoya. Idan har saurayin ya kuskura ya nemi wannan budurwar da ɓatanci a wannan daren, za ta tona masa asiri. Wannan ya ishe shi da ma duk zuri’ar gidansu abin kunya har abada. Dole ya bar wannan ƙauyen ya koma nesa saboda abin kunyar da ya aikata. Maganar ya ƙara dawowa cikin wannan al’ummar har ya saki jiki ya yi mu’amala da mutane babu ita.

Wannan haƙiƙa wani darasi ne ga siyasar Hauwasa ta zamani. An wayi gari mutum zai tafka abin kunya a al’umma ana ji ana gani ƙiri-ƙiri a tsayar da shi a matsayin ɗan takara har ma a sami dubban jama’a masu goyon bayansa da ta da jijiyar wuya idan an yi ƙoƙarin faɗar illolinsa. Idan da jam’iyu da masu zaɓe za su ɗauki wannan salo na Maguzawa, da ya tsarkake siyasar zamani.

4.3             Ɗaurin Aure Maguzawa

Bayan an gudanar da duk matakan ɗaurin auren da aka tanada a al’adar Maguzawa, za a umurci wani daga cikin manya ya ɗaura auren. Shi kuma zai yi amfani da wata karɓaɓɓiyar siga ta cewa.

                        Ni wane na ɗaura auren wane da wance,

 in ga ɗan jar kazar uban da zai raba,

Daga cikin dangin ango ko dangin amaryar ana iya samun wanda zai fito ya ce shi ya raba. Dalilin yin hakan kuwa yana iya zama wata lam’a da ya hanga a rayuwa ko zuriyar ango ko amaryar da ba ya son ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa su haɗa zuriya da su. Wataƙila an taɓa samun wani gawartaccen ɓarawo, ko kwarto, ko raggo a dangin ɗaya daga cikin ango ko amaryar. Furucinsa a wannan muhallin zai sa a dakatar da ɗaurin auren a bincika. Idan an tabbatar da gaskiyar ikirarin nasa to ana iya fasa auren.

Wannan ko shakka babu wata dabara ce ta tsarkake al’umma da yanayin siyasar zamani zai amfana da shi wajen samar da shugabanni ko ‘yan takara. Rashin yin hakan shi ya taimaka wajen gurɓata siyasar zamani. Ya kasance ‘yan takara su fito har su lashe zaɓe ba tare da an ɗora tarihinsu a wani mizanin awon inganci ba.

4.4      Al’adun Kai Bante

Maguzawa sukan yi al’adar tabbatar da ɗiyauci ‘ya mace bayan an ɗaura mata aure kafin a kai ta gidan miji. Waɗannan al’adu sukan bambanta daga wuri- zuwa wuri.[1] Amma duk sun haɗu a kan cewa, za a aiwatar da wani tsafin da zai tabbatar da cewa amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba. Idan ba ta yi musu ba (ta nuna lallai ta taɓa sanin namiji), ko dai a fasa auren, ko a rage wa miji dukiyar auren, kuma dole ta tafi gidan miji da ɗan kuikuyon kare a matsayin ɗan zaman ɗaki, ko kuma hudajjiyar ƙwarya da za a rataye a tsakar ɗakin. Da zarar aka ga haka, to mutuncinta ya zube, kuma ya zama abin faɗe ga iyayenta da duk zuriyar gidansu. Idan kuwa ta bari aka aiwatar da tsafin to tana ma iya rasa ranta.

Ba a ganin bin irin wannan mataki wajen samar da shugabanci ta hanyar siyasa zai samar da nagartacciyar al’umma? Na san babu ɗan majalisa ko shugaban ƙaramar Hukumar da zai so ya ga kare na binsa ko an rataye masa kwarya a ofishinsa wanda zai nuna tarihi ya tabbatar da shi ɗan iska ne tun kafin ya yi takara. Idan kuma haka ne, to da sai mutum ya san kansa kafin ya fito ya ce yana son jagorancin jama’a. Su ma jama’a kai tsaye za su iya sanin wanda ya cancanta su zaɓa.

4.5      Ladubban Haramcin Sata

Maguzawa sun ɗauki sata abin ƙyama ƙwarai da gaske. Duk wanda aka tabbatar da ɓarawo ne to ba ya da gindin zama a wannan al’umma. A ƙoƙarin kafa wannan tarbiyyar a al’umma, an samar da dokoki musaman ga masu bautar tsafin Uwar gona. Uwar gona wadda suke nuna cewa, ita ce uwar baƙaƙen iskoki, takan kumbura wa ɓarawo ciki ya mutu idan ya saci misali hatsin wani. Bayan ɓarawon ya mutu, dole a walaƙantar da gawarsa kafin a bizne ta muddin ana so zuri’arsu da ya fito su zauna lafiya. Abin da ake yi shi ne, za a ɗaura igiya a ƙafar mamacin aja gawarsa ana bardaɗa toka a inda gawar ta ja ƙasa har zuwa wurin da za a bizne ta. Idan ba a yi hakan ba, aka bizne ta salim-alim to, duk mazan gidan baligai za su riƙa mutuwa ɗaya bayan ɗaya har su ƙare. Haka kuma ba wani buki da za a yi masu na mutuwa komai muƙaminsa a al’umma.

Wannan ƙalubale ne ga ‘yan siyasar zamani. Tunanin ‘yan siyasar zamani shi ne duk abin da lauje ya jawo ciyawa ne. Sata ta zama abin ado. Idan da ‘yan siyasa cikinsu zai rinƙa kumbura suna mutuwa idan sun saci dukiyar jama’a, da an wayi gari babu ɓarawo daga cikinsu. Haka kuma idan za a ja gawar duk ɗan siyayar da ya saci dukiyar jama’a ya mutu, to da sata ta zama abin ƙyama a siyasar Hausawa ta zamani. Idan da zuri’ar ‘yan siyasa maza za su mutu a sakamakon satar da ɗan’uwansu ya yi, da sun bar fafutukar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tsayar da ɗan takara don ya sato ya kawo gida.

4.6      Riƙe Alƙawari

Maguzawa mutane ne da a al’adance suka ladabtu da riƙe alƙawari kuma suka ba shi muhimmanci. Misalin da za a iya kawowa a nan shi ne na al’dar zaɓen suna a al’ummar Maguzawa “Kainafara” waɗanda ake yi wa kirari da ‘Arnan Birci.’[2] A al’adar waɗannan Maguzawa, idan mace ta haihu, ba za a yi suna ba sai jinjirin ya kai kwana goma sha huɗu da haihuwa. A taƙaice, za a sami tsofaffi maza kamar su goma su sami gindin wata bishiya su zauna a ƙofar gidan da aka yi haihuwar. Waɗannan tsofaffin za su sami gaɓoɓin kara su tsaga su, su yi wani zane a jikin kowane ɓari na kara. Sai a kira Ungozoma a ba ta waɗannan kararen a ce ta kai wa mai jegon ta zaɓi ɗaya. Idan ta zaɓa, Ungozoma za ta dawo wa waɗannan tsofaffin da karan. Sai su fassara sunan yaron ta la’akari da zanen da ke jikin karan. Za a gaya wa Ungozoma sunan jinjirin ta gaya wa uwar. Sai dai ba za a kira wannan jinjirin da wannan sunan ba sai ranar da za a yi masa ko mata aure. Waɗannan tsofaffin da Ungozoma da uwar jinjirin su kaɗai suka san sunan kuma ba a yarda su gaya wa kowa ba. Sai dai su bar shi a zuciyarsu har wannan ranar.

Rashin Riƙe alƙawari yana daga cikin matsalolin da ‘yan siyasar zamani suke fuskanta wadda ita ke ƙara zubar masu da mutunci a idan jama’a. Idan har Bamaguje zai iya riƙe alƙawarin ƙin faɗin sunan jariri na lokaci mai tsawo, me zai hana ɗan takara ya iya riƙe alƙawurran da aka yi da shi a lokacin da yake yaƙin neman wakilcin jama’a?

5.0      Kammalawa

A wannan maƙalar, an yi bayanin abin da aka fahimta da dimokuraɗiyya, da kuma ƙoƙari gano mutanen da ake kira Maguzawa. Nazarin ya waiwayi yadda Hausawa ke gudanar da dimokuraɗiyya a wannan zamanin da kuma amfani da ma’aunin Maguzanci wajen yanke hukuncin rashin ingancin wannan lamari. Sakamakon wannan nazari ya tabbatar muna da irin takin saƙar da ake samu tsakanin kyawawan ɗabi’un Maguzawa da kuma yanayin tunanin Hausawa a kan dimokuraɗiyya musamman a wannan zamanin. Duk da yake ba ƙudirin wannan maƙala ba ne ya ja hankalin mutane zuwa ga rayuwar Maguzanci, misalai ne kawai aka zaƙulo waɗanda za su tabbatar da cewa Bahaushe bai gaji wasu ɗabi’u marasa kyau da aka maƙala ya siyasarsu ta dimokuraɗiyya ba.

 Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Abdullahi, I. S. S. (2008). “Fitattun Ɗabi’un Maguzawa” Maiduguri Journal of

Linguistics and Literary Studies (MAJOLLS) Vol. X Department of Languages and Linguistics, University of Maiduguri.

Abdullahi, I. S. S. (2009). “Bukin Hawan Sadaka na Maguzawa” Journal of

Contemporary Hausa Studies, Vol. 1 No. 1, Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ’Yar’adua University, Katsina.

Abdullahi, I. S. S. (2010). “Tsafe-tsafen Maguzawa na Aure da Haihuwa” Zuba

Journal of Hausa Studies (ZUJOHAS) Vol. 1 No. 1 Department of Hausa, F. C. T. College of Education Zuba, Abuja – Nigeria.

Abdullahi, I. S. S. (2012). “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa” Maƙalar da Aka Gabatar

a taron Ƙara wa Juna Sani, cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, 19 ga Satumba.

Akodu, A. (2001). Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Gaskiya Corporation Limited. Zariya – Nigeria.

Anchau, M. D. (1986). “Tasirin Zamani Da Illolinsu Kan Al’adun Auren Hausawa A Lardin Zazzau, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

Fletcher, D. C. (1929). “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment Report on ’Yanɗaka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833 National Archives and Monuments, Kaduna.

Gennep, A. V. (1960). The Rites of Passage The University of Chicago Press, USA.

Gwarjo, Y. T. da wasu (2005). Aure a Jihar Katsina Hukumar BincikenTarihi Da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina, Hausa Vocabulary, Oxford University press, London

Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci, Cyclostyled Edition – Hausa Publications Centre – Zaria.

Kado, A. A. (1987). “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

Krusius, P. (1915). “Maguzawa” in: Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

Maikano, M. M. (2002). “Maguzawan Yari Bori: Tarihinsu Da Al’adunsu”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Malumfashi, A. A. (1987). “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study of Maguzawa Society in Malumfashi Area” (B. A. Hausa Project), Bayero University, Kano.

Mashi, B. U. (2001). “Maguzanci Da Zamananci: Nazari A Kan Al’adun Maguzawan Ɓula A Gundumar Mashi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Nyamwaya, D. and Parkin, D. (1987). Transformation of African Marriage.

Manchester University Press, United Kingdom.

 

Ottenberg, P. and Simon (Ed.) (1960). Cultures and Ethics of Africa, H. Wolff Book Mfg.Co., Inc. U.S.A.

Safana, Y. B. (2001). “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Sufi, A. H. (2001). “Hanyar Kiran Maguzawa Zuwa Ga Addinin Musulunci.” Maƙalar da aka gabatar a taron Kwamitin Yaɗa Addinin Musulunci na Jihar Kano.

Tremearne, A. J. N. (1913). Hausa Superstitions And Customs. John Bale, Sons and Danielsson, LTD Oxford. University Press United Kingdom.

Yusuf, A. B. (1986). “Wasannin Maguzawan Ƙasar Katsina”, Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.


[1] Don ganin waɗannan al’adun a dubi Muhammadu Sani Ibrahim, “Dangantakar Al’ada Da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa.” Kundin digiri na biyu, Jami’ar Bayero Kano, 1982

[2] Birci wani ƙauye ne a cikin ƙaramar hukumar Kurfi ta jihar Katsina.

Jejin Maguzawa

Post a Comment

0 Comments