Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Sallar Da Ta Fi Mutane Da Yawa Ta Fi Lada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya kara ma Dr. Ikhlasi, dan Allah dr. Akwai bambancin lada ne a sallar jam'i mai mutane da yawa da kuma yan kaɗan?

Domin muna da masallatai biyu a anguwar mu, to da yawa an fi raja'a a ɗaya, idan na yi ma mutane magana sai suce ai an fi cika a wancan ne shiyasa basa zuwa wannan.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Wannan magana haka take, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yana cewa: "Sallar mutane biyu tafi sallar mutum ɗaya, sallar mutum uku tafi sallar mutum biyu lada, duk sallar da tafi mutane da yawa tafi yawan lada" kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

Hadisin da ya gabata yana nuna babu laifi idan mutum ya tsallake Masallacin da yake da karancin Jama'a ya tafi Wanda ya fi yawa mutane saboda neman karin lada.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments