𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum waramatullahi wabarakatuhu barka da safeya muna fatan antashe lafiya Allah yasa haka ne. Mallam tambayar mu da mutum da duniya da duwatsu wanne Allah ya fara haltta, Da ayar da Allah yayi magana akai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Farkon abin da Allah ya halitta daga cikin abubuwan da aka
sani shi ne Al’arshinsa, wanda ya tashi bayan ya halicci sammai, kamar yadda
Allah (تعالى) yake cewa
وَهُوَ
الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى
الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا
"Kuma Shi ne wanda Ya halicci sammai da kasa a cikin
kwanaki shida, kuma Al'arshinSa ya kasance a kan ruwa, domin Ya jarraba ku,
wane ne daga cikinku ya zama mafi alherin aiki" (suratul Huud Aya ta 7).
Wasu kuma su ka ce Ruwa shi ne farko, kamar yadda aka
tambayi Manzon Allah sallallahu alayhi wa sallam, yadda duniya ta fara, sai ya
ce
« كان الله ولم يكن شىء غيره وكان
عرشه على الماء وكتب في الذكر كل شىء ثم خلق السماوات والأرض
»
«Allah ya wanzu kuma babu wani abu a tare da shi. Ya halicci
Al'arshi [Ya sanya shi] a saman ruwa. Sa'an nan kuma (Ya umurci Alƙalami
ya rubuta) a cikin Alƙur'ani, dukan abin da zai auku. Sai Allah ya halicci sammai da
ƙasa.» [Bukhariy ya rawaito shi]
Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya amsa wannan
tambayar da fara bayyana cewa samuwar Allah ba ta da mafari, watau shi ne
madawwami. Babu wanda aka jingina shi da dawwama face Shi. Watau babu abin da
ya wanzu sai Allah, kuma Allah ne ya halicci komai, watau ya fitar da dukkan
halitta daga babu, subhanallahu wata ala.
Allah, bai halicci dukan halittu a lokaci guda ɗaya ba. Kuma da Ya so
wannan da ta auku. Amma sai ya yi hakan a cikin kwanaki shida, Ya halitta
sammai da ƙasa.
Kuma acikin Duniya Allah ya halicci koguna da duwatsu da kwaruruka. Wanda
hikimar wannan ita ce koya mana kada mu yi gaggawar acikin al'amuran mu. Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:
إِنَّ
اللهَ تَعَالَى خَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ مِنَ الْمَاءِ
«Allah ya halicci komai daga ruwa.» [Ibn Hibban ne ya
rawaito shi]
Wannan kuma yana nufin Allah ya halicci ruwa kafin ya
halicci haske, da duhu, da ƙasa, da sama, da Al'arshi, da Allo mai tsaro. Allah ya sanya
ruwa ya zama tushen sauran halittu. Ya halitta Al'arshi daga ruwa. Sa'an nan
kuma Ya halicci Alƙalami kudra, sa'an nan kuma littafin da ke ɗauke da ayyukan bayi. Bayan
waɗannan halittu, sai
Allah ya halicci sauran halittu: irin su kasa, sammai, dabbobi, duwatsu,
bishiyoyi, koguna. Adam, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya
kasance daga nau’in halittun Allah na karshe, karshe, wato mutane.
Akwai sauran bayanai da hujjoji na malamai da yawa, Kuma
Allah ne mafi Sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.