Ticker

6/recent/ticker-posts

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Kamar yadda tsare-tsaren gidauniyar adabi ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa ta shirya cewar, za a riƙa gudanar da gasa daga lokaci zuwa lokaci akan wasu muhimman lamura da suka shafi rayuwar al’umma, domin bayar da dama ga al’umma su fito da matsalolin su da kansu.

Maudu'in Gasa (Buri)

A wannan shekarar 2024, maudu'in gasar zai kasance ya taɓa batutwa da suka shafi hanyoyin cimma burika da kuma muradu da Ɗan’Adam kan buƙaci cimmawa a rayuwarsa, za a so marubutan su fito a batutuwa da suka shafi:

Burukan ko ƙudurorin da rayuwa kan buƙaci cimmawa na Ɗan’adam.

Ƙalubalen da akan haɗu da su a hanya, wanda wasu lokutta sukan hana cimma waɗannan buruka, ko su zama tarnaƙi ga Ɗan’adam na cimma burinsa na zama wani abu.

Yadda za  a iya gane mene ne burin mutum tun yana ƙarami da yadda za a taimake shi ya cimma wannan burin nasa, ko kuma a sauya mai shi idan ana ganin burin ba wanda ya dace da yanayin rayuwarsa ba ne.

Matsalolin da ke tattare da rashin cikar buri da abin da hakan kan haifar a rayuwar mai burin.

Tilas masu shiga gasa su yi anfani da salon ayyanawa na gajerun labaran zube na Hausa.

Taswirar Gasa

An bayar da dama ga marubutan Hausa maza da mata, su aiko da samfurin labarin da za su rubuta mai ɗauke da kalmomi da basu gaza 500 ba kuma kar su wuce 1000. A tabbata an turo da samfurin kai tsaye ga dangiwaliterary2020@gmail.com daga ranar 8/05/2024 zuwa ranar 15/06/2024. Za a tace da zabar 30 daga cikin samfurin labaran da aka aiko waɗanda suka fi burgewa a cikin kwanaki sha biyar (20/6/2024-5/7/2024). sDaga nan za a nemi masu waɗannan samfuran labaran guda talatin da su halarci bita domin samar masu da wani horo na musamman kan yadda ake son alabaran su kasance. Sannan su koma su rubuto labari cikakake wanda bai gaza kalma 4000 ba bai kuma wuce dubu biyar ba (5000) daga 1/8/2024 zuwa 1/09/2024. Za a bayyana sha ukun da suka yi nasara a cikin watan Satumbar 2024./

Za a tace da tsara da kuma buga labaran, a ƙaddamar da su a wani gaggarumin biki da za a shirya a Katsina da yardar Allah.

Dokokin Rubutun

Domin shiga wannan tsarin samar da gajerun labarai na Hausa wanda zai kasance mai ɗauke da kalmomi 5000, marubuta na da damar su yi bincike da nazari da tuntuɓa na tsawon wata ɗaya kafin aiko da labaran, bayan tantance su da aka yi.

1. Waɗanda suka yi na ɗaya zuwa na uku a gasar Muhalli, Sutura ta 2020 da gasar Ɗaukar Jinka ta 2022 ba za su shiga wannan gasar ba.

2. Ba a kuma buƙatar sai ana da wani kwali ko satifket na musamman kafin a kasance cikin wannan tsarin samar da labarai, illa iyaka gwaninta da fasahar tsara labaran Hausa. Ana kuma buƙatar rubutun ya dace da batutuwan da suka shafi burukan rayuwa da duk wani abu da ke da alaƙa da shi.

3. Dole ne ya kasance an yi amfani da ƙa'idojin rubutu bisa daidaitaciyar Hausa.

4. Dole ne a yi rubutun bisa tsarin haruffa masu ƙugiya, kuma rubutun ya kasance an aika shi bisa tsarin Microsoft word ko PDF. Zuwa ga wannan email ɗin dangiwaliterary2020@gmail.com

5. Wajibi ne labaran su kasance sabbi waɗanada ba a taba shiga wata gasa da su ba ko kuma buga su a wasu jaridu ko zauruka na kafafen sadarwa.

6. Mutum biyu za su iya haɗin guiwa domin samar da labari guda. 

7. Wannan gasar buɗe take ga duk marubuta da masu sha’awar farawa, matuƙar da zai iy kiyaye dokoki da ƙa'idojin da aka gindaya.

8. Wajibi ne a aiko da somun taɓi na kalmomi ɗari biyar zuwa dubu (500-1000) a cikin tsawon wata ɗaya.

9. Duk labarin da aka shiga gasar da shi mallakin gasa ne, ba a yarda a sake ɗaukar shi a shigar da shi wata gasa ba ko makamancin haka.

10. Hukuncin da alƙalan gasa suka yanke shi ne na ƙarshe ba za a sake tattaunawa ko duba hukuncin ba, bayan fitar sakamako.

Kyautukan Da Za A Bayar

Za a bada kyautuka ga waɗanda suka shiga gasar daga na ɗaya zuwa na goma sha uku (13) kuma a buga littafin, a ƙaddamar da shi a yayin bikin bayar da kyautukan.

Don karin bayani a tuntubi wadannan lambobin: 08060767379, 08036954354

Gasar Rubutattun Gajerun Labaran Hausa Ta ARC. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation

Post a Comment

0 Comments