Daga Hausar Rukuni Zuwa Boyayyiyar Al’ada: Kebabben Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau

     Cite this article as: Sani, A-U. & Adamu, S. (2023). Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Al’ada: Keɓaɓɓen Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 115-123. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.013.

     Daga Hausar Rukuni Zuwa Ɓoyayyiyar Al’ada: Keɓaɓɓen Nazari A Kan Hausar Telolin Garin Gusau

    Abu-Ubaida Sani
    Department of Languages and Cultures
    Federal University, Gusau
    , Zamafara, Nigeria

    Sani Adamu

    Prince International Schools Gusau, Zamfara, Nigeria
    +2348135366284

    Tsakure

    Wannan bincike ya ta’allaƙa ne kan nazarin Hausar teloli. Manufar binciken shi ne nazartar ire-iren kalmomi da jimloli da teloli ke amfani da su ta hanyar ba su ma’anonin da suka bambanta da maganar yau da kullum. Kadadar binciken ta taƙaita a garin Gusau da ke jahar Zamfara. An yi amfani da tattaunawa a matsayin babbar hanyar tattara bayanai. A bisa haka ne aka yi hira da teloli daban-daban da ke garin Gusau. Binciken ya gano cewa, akwai kalmomi da jimloli daban-daban da telolin ke amfani da su waɗanda suka bai wa ma’anonin da suka bambanta da na gama-gari. Waɗansu kuwa sukan kasance ƙirƙira ce kai tsaye. Binciken ya kalli wannan a matsayin wani abinci a fagen nazarin harshe da alada. Kundace su da nazartar su mataki ne na bunƙasa harshe tare da taskacewa da daidaita alada musamman yayin fito da tasirin amfani da iren-iren waɗannan Hausar ta rukuni ga zamantakewa.

    Fitilun Kalmomi: Telololi, Hausar Rukuni, Harshe, Al’ada

    1.0 Gabatarwa

    Masu azancin magana sukan ce "tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela tana da farinta." Hausawa al'umma ce wadda tun tuni suke da tsarin tattalin arziki. Wannan ne ya sa sana'o'i suka yi tasiri a gidajen Hausawa. Da wuya a da can a samu wani gidan Hausawa a ƙasar Hausa da ba su da sana’a.[1] Duk da haka, sana’o’in sukan samu sauye-sauye musamman sakamakon tasirin zamani da shirye-shiryen game-duniya.

    ɓangare guda kuwa, sana'ar ɗinki sana'a ce wadda take tafiya tare da zamani. Tana samun sauye-sauye kamar yadda zamani yakan sauya. Akan samu sauyi dangane da kayayyakin da ake ɗinkawa ko kayan aiki da sauran abubuwa da suka shafi sana’ar kai tsaye ko a kaikaice. Wannan ne ma ya sa duk mai son ya yi dogon zamani a ɗinki, to dole ne sai ya tafi tare da zamani.[2]

    Tuni aka samu Hausar rukuni a tsakanin maɗinka biyo bayan buƙatu na aladar zamantakewa da hulɗayya. A waɗansu lokutan, Hausar teloli ta shafi aikin sana’ar ɗinki kai tsaye, wato tun daga kan kayan aikin ɗinki zuwa aiwatar da ɗinkin da kuma kayayyakin da ake ɗinkawa. A waɗansu lokutan kuwa, buƙatun sakayawa da sirrinta zance ne yakan samar da Hausar teloli. A bisa laakari da haka ne wannan takarda ta ɗora sana’ar ɗinki a faifan nazari musamman domin ƙwanƙwance abin da ke da akwai cikin Hausar teloli.

    Kai tsaye, tambayoyin da nazarin ke son amsawa su ne (i) Ga Bahaushen yau, me ake nufi da ɗinki kuma yaya ake aiwatar da shi? (ii) Waɗanne nau’ukan maɗinka ake da su a farfajiyar binciken? (iii) Yaya yanayi da misalan Hausar telolin farfajiyar binciken suke? (iv) Mene ne tasirin wannan Hausar a muhallin harshe da al’ada Bahaushiya?

    1.1 Dabarun gudanar da bincike

    Kasancewar kadadar binciken ba ta tsallake al’ada da harshen Bahaushe ba, bai zama dole a yi amfani da Baturen ra’i wajen gudanar da shi ba. A maimakon haka, an ɗora shi a kan hanyar gudanar da bincike da ta dace da Bahaushiyar al’ada.[3] Ya gudana ne a kan tunanin Bahaushe na “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” A fahimtar wannan ra’ayi, ba abin mamaki  ne ba idan aka samu waɗansu keɓaɓɓun al’adu da kuma harshe na musamman a wurin maɗinka. Ma’ana ke nan su ma za su yi “kukan gidansu” na sana’ar ɗinki.

    Dangane da farfajiyar bincike kuwa, yana da kyau a lura da cewa ko a cikin ƙasar Hausa, akan samu bambance-bambance game da yadda ake gudanar da waɗansu sana’o’i daga wuri zuwa wuri. Farfajiyar wannan bincike ta taƙaita ne a cikin ƙwaryar garin Gusau. Binciken ya mayar da hankali kan Hausar teloli a garin Gusau ta fuskar:

    i.                     Kayan aiki

    ii.                   Yanayin gudanar da ayyuka

    iii.                 Sunayen ayyuka

    iv.                 Sakaya zance (ɓad-da-bami)

    Domin samun sauƙin aikin, an kasa muhallin binciken zuwa sassa uku wato (i) Gusau ta Yamma da ta haɗa da Birnin Ruwa da Ƙofar Yarima (Bakin Silma) da Bakin Tsohuwar Kasuwa da yankin Sabon Fegi, (ii) Gusau ta Tsakiya da ta haɗa da Sabon Gari da Mutuwa Geji (Mortgage) da Bakin Total da Tashar Magami, (iii) Gusau ta Gabas da ta ƙunshi Tudun Wada da Unguwar Gwaza da Samaru da Hayin Malam Sani da Damɓa.[4] An tuntuɓi Teloli daban-daban daga waɗannan yankuna domin samun ingantattun bayanai daga tushe. Kasancewar daga cikin telolin akwai waɗanda ba su da ilimin karatu da rubutu na boko, an zaɓtattaunawa a matsayin hanyar tattara bayanai.

    2.0 Teloli a garin Gusau

    Kalmar tela ararriya ce daga harshen Ingilishi. A gadajjiyar al’ada, Bahaushe na kiran wanda ke sana’ar[5] ɗinki da suna “maɗinki.” A jam’i kuma sai ya ce “maɗinka.” A ƙasar Hausa a yau, ararriyar kalmar wato tela ta karaɗe ko’ina. Da zarar an ambace ta, hankalin mai sauraro zai koma kan ɗinki irin wanda ake aiwatarwa a zamanin yau.

    Ɗinki na ɗaya daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in Bahaushe gadaddu. Alhassan da wasu, (1982 p. 54-55) sun bayar da ma'anar ɗinki na gama-gari a matsayin hanyar "haɗa sawaye da wani abu saƙaƙƙe a mayar da shi tufa ko wani abin sawa a jiki da taimakon zare da allura ko ƙayar aduwa ko basilla."

    A cikin wannan bincike, an mayar da hankali ne kan ɗinkin tufafi a keɓance. Ta la'akari da ma’anar gama-gari da aka bayar tare da yin la’akari da zamananci, za a iya cewa ɗinki sana'a ce ta amfani da hikima wajen sarrafa yadi zuwa abin suturta jiki ko ƙawa, tare da taimakon keken ɗinki da sauran kayan aiki.

    ɓangare guda kuwa, teloli sun kasu zuwa rukunoni da dama. Akwai manyan abubuwa biyu da za a iya la’akari da su yayin tattauna rabe-raben teloli. Za a iya la’akari da nau’ukan kayan aikin da teloli ke amfani da su domin bayyana rabe-rabensu. Bayan haka, za a iya la’akari da muhallin gudanar da aiki.

    2.1 Rabe-Raben teloli ta la’akari da kayan aiki

    Teloli na amfani da kayayyakin aiki daban-daban yayin aiwatar da sana’arsu. Wannan ya kama tun daga kan keken ɗinki zuwa ƙananan kayan aiki irin su almakashi da zare da sauransu. Duk da haka, babban abin la’akari a wannan rukuni shi ne nau’ukan kekunan da maɗinkan sukan yi amfani da su. Yayin da aka yi la’akari da nau’ukan kayan aiki, ana iya raba maɗinka zuwa rukunoni kamar haka:

    A-     Telolin Taka-Taka: Waɗannan su ne waɗanda sukan yi amfani da keken ɗinki wanda ake takawa da ƙafa. Wani lokaci akan yi amfani da keken ɗinkin tare da taimakon wani ɗan injin idan akwai wutar lantarki ko janareta mai ba da hasken wutar lantarki. Akan samu maza da mata a cikin nau’in waɗannan teloliAn samu babban sauyi a wannan rukunin teloli bayan samuwar wani nau’in keken ɗinki mai suna indostura. Wannan keke ba ya aiki sai da wutar lantarki.

    B-      Telolin Barnina/Fonis: Waɗannan teloli ne masu aiki da wani keken ɗinki da ake kira fonis. Suna yi wa wuyan riga ko wani sashe na tufafi aiki. Suna yin aiki na mata da na maza. Wannan keken ba ya aiki sai da wutar lantarki ko na janareta.

    C-     Telolin Cunko: Waɗannan telolin suna yin amfani da wani keke wanda ya bambanta da fonis ta fuskar yanayin saƙar ɗinkinsu da kuma sifar keken. Keken cunko yana da wani sitiyari a ƙasa. Su ma suna aikin maza da mata.

    D-    Telolin Sama: Teloli ne masu kamance da na cunko amma zubin ɗinkin da suke yi ya bambanta da nasu. Aikin sama yana da kamance da ɗinkin hannu. Shi ma akan yi na maza da na mata. Tamkar dai keken cunko, shi ma ba ya aiki sai da wutar lantarki ko na janaretaSannan yana da sitiyari ƙasa kamar na keken cunko.

     

    2.2 Rabe-Raben teloli ta la’akari da muhallin aiki

    Muhalli ko wurin gudanar da aiki wani abin la’akari ne yayin bayyana rabe-raben teloli. A ƙarƙashin wannan, za a iya samun manyan rukunonin teloli guda uku kamar haka:

    A-     Telolin Girke: Su ne telolin da suke zaune wuri guda. Idan mutum ya sayi yadi zai tafi ya same su wurin da suke. Sukan zauna a shago ko rumfa idan kasuwa ce, ko kuma a cikin gidaje.

    B-      Telolin Tafi-Da-Gidanka: Waɗannan teloli ne waɗanda ba su da tsayayyen wurin zama inda za a same su domin ba su aiki. Sukan zagaya da keken ɗinkinsu a kafaɗa ko a saman abin hawa. Sau da dama sukan kasance tafe suna shelanta "Ga tela ya zo!" Mafi akasarin ayyukansu sun keɓanta ga gyaran tufafin da suka yage ko kuma ɗinkin kalo (tamfol). Mafiya yawan waɗannan telolin maza ne.

    C-     Teloli 'Yan Ci-Rani: Su ne masu tashi daga garuruwansu zuwa wasu garuruwa ko ƙasashe domin neman ayyukan ɗinki. A irin wannan rukuni akan samu telolin tafi-da-gidanka da kuma na girke.[6]

    Ko bayan waɗannan rabe-rabe, akwai ta fuskokin da za iya kallon kashe-kashen maɗinka. Misali, ana iya dubawa ta fuskar jinsi. A nan za a samu (i) maɗinka maza da (ii) maɗinka mata. Ana kuma iya dubawa ta fuskar jinsin waɗanda ake yi wa ɗinki. A ƙarƙashin rukunin ana iya samun (i) maɗinkan mata da (ii) maɗinkan maza da kuma (iii) maɗinkan tarayya. Bayan haka, ana iya duba abin da maɗinkan ke samarwa domin bayar da rabe-rabensu. A nan ne za a iya samun (i) maɗinkan haɗi da (ii) maɗinkan aiki.

    1.3 Tarayyar teloli

    Duk da kasancewar teloli sun rabu zuwa rukunoni daban-daban, akwai ta fuskokin da suka yi tarayya. Daga ciki akwai:

    i.         Kowane tela ya ɗauki ɗinki a matsayin sana’a.

    ii.       Kowane tela yana yin ɗinki ne domin samun abin masarufi, don kawar da lalurorin yau da kullum da sukan bijiro.

    iii.     Duk suna mu'amula da yadi, don samar wa al'umma tufafi ko ingantawa ko gyara ko ƙawata tufafin.

    iv.     Duk suna amfani da keken ɗinki don ɗinki ko gyara ko yin kwalliya ga yadi ko wani ƙyalle da aka kawo masu aiki.

    v.       Sukan rufa wa juna asiri idan buƙatar hakan ta taso.

    vi.     Sukan yi aiki daidai da buƙatun mutane.

    vii.   Suna da Hausa ta musamman (sakayayyiyar hanyar sadarwa a tsakaninsu).[7]

    3.0 Hausar teloli

    A nan, Hausar teloli na nufin nau’in Hausa ta musamman da take bambanta da sananniyar Hausa ta fuskar kalmomi ko jimloli, wacce kuma ake samun ta a tsakanin teloli. Za a tattauna Hausar telolin garin Gusau ƙarƙashin muhimman rukunoni guda biyu wato (i) kalmomi da (ii) jimloli.

    3.1 Kalmomin Hausar teloli a garin Gusau

    Jadawali na 1 da ke ƙasa yana ɗauke da jerin waɗansu kalmomin da telolin garin Gusau sukan yi amfani da su.

    Jad 1: Kalmomin Hausar telolin Gusau da ma’anoninsu

    Kalma

    Ma’anar Asali

    Sabuwar Ma’ana

    Tsokaci

    Hassan/

    Hassan Bala

    Sunan Mutum

    Mutumin da ya cika son banza (mai son kansa) dangane da abubuwa.

    Ana amfani da wannan furuci domin a yi wa wani tela hannunka mai sanda. Da zarar tela ya fahimci cewa kwastoma Hassan Bala ne, to lallai ba zai sakankance da shi ba. Zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa haƙƙinsa ya fito.

    Raɓawo

    Zaurance ne (ɓarawo)

    Mutumin da ya cika son banza (mai son kansa) dangane da abubuwa.

    Ana amfani da wannan furuci domin a yi wa wani tela hannunka mai sanda. Da zarar tela ya fahimci cewa kwastoma Hassan Bala ne, to lallai ba zai sakankance da shi ba. Zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa haƙƙinsa ya fito.

    Badakuwa

    -

    Yanayi ne inda tela yake taya tela ɗan uwansa domin su tsuga tsada ga kwastoma.

    Yayin da tela ya ambaci kalmar, tela ɗan uwansa zai fahimci cewa wancan telan na buƙatar su haɗa baki domin kwastoma ya amince da abin da za su faɗa masa, ko da kuwa ba gaskiya za su faɗa masa ba.

    Karatu

    Duba jerin baƙaƙe da wassula tare da ayyana furucinsu a zuci ko furta su da baki

    A bai wa wanda ya kawo ɗinki haƙuri domin an yi masa rashin gaskiya.

    Tela na iya yi wa kwastoma karatu. Kuma yakan iya yin ishara ga ɗan uwansa tela da ke kusa domin ya taya shi yin karatun. Misali, idan tela ya ambaci cewa: “Dole sai da karatu,” to ɗan uwansa da ke kusa na iya fahimtar cewa yana so ne ya taya shi ba da haƙuri ga kwastoma.

    Sakin Layi

    1. Kaucewa daga kan wata hanya/turba

    Yin shaidar zur game da rashin gama wa wani ɗinkinsa.

    Tela na iya kare ɗan uwansa ta hanyar yin shaidar zur. Misali, yana iya faɗa wa kwastoma cewa: “Ɗazun nan yake magana cewa, yau zai kammala ɗinkinka.”

    Gauniyya/ Gauni

    Gawurta ko tsanani

    Warin ƙashi

    An fi amfani da wannan lafazi yayin gulmar wani ko wata mai warin ƙashi da ya/ta shigo shago. Tela na faɗa wa ɗan uwansa wannan kalma domin an karar da shi cewa mai warin ƙashi ya shigo.

    Tushen Bayani: Hira da teloli

    3.2 Jimlolin Hausar teloli a garin Gusau

    A nan yana da kyau a fahimci cewa, da dama daga cikin jimlolin Hausar teloli na da dangantaka ta kai tsaye da kalmomin. A irin wannan yanayi, akan sanya kalmomin ne a cikin jimloli yayin magana. A ɓangare guda kuwa, akan samu jimloli kai tsaye a matsayin wani ɓangare na Hausar teloli. Dangane da kalmomin da aka kawo a jadawali na 1 da ke sama, za a iya amfani da su cikin jimloli kamar haka:

    Jad 2: Misalan yadda ake amfani da kalmomin teloli cikin magana

    Kalma

    Misalin Jumla

    Ma’ana

    Hassan/Hassan Bala

    Maza, Hassan Bala ya zo?

    Wannan ɓarawo ne.

    Raɓawo

    Maza, ka ga raɓawo?

    Wannan ɓarawo ne.

    Badakuwa

    Maza, akwai badakuwa.

    A taya ni tsuga tsada a wannan.

    Karatu

    Don Allah ku taya ni karatu.

    Don Allah ku taya ni bayar da haƙuri.

    Sakin layi

    Sakin layi fa kawai na yi.

    Ban tabbatar da gaskiyar lamarin ba, kawai na faɗa ne.

    Gauniyya/Gauni

    Yau mun samu gauniyya.

    Wani mutum ko wata mata ko waɗansu mutane masu warin ƙashi sun shigo.

    Tushen Bayani: Hira da teloli

    ɓangare guda kuwa, akwai jimloli kai tsaye da teloli sukan yi amfani da su. Sukan bai wa waɗanan jimloli ma’anoni na musamman wanda hakan ne ya mayar da su keɓantattu kuma na rukunin telolin. Yana da kyau a lura cewa, misalai da aka kawo a jaddawali na biyu (Jad 2) da ke sama, kalmomi ne aka yi misalin yadda ake amfani da su cikin jimloli. Hakan na nufin cewa, ana iya amfani da su cikin waɗansu sigogin jimloli na daban.

    Jad 3Jimlolin Hausar telolin Gusau da ma’anoninsu

    Jumla

    Ma’anar Asali

    Sabuwar Ma’ana

    Nama ya tsiro masa a ido.

    Tsokar nama ya yi tsiro a cikin idon mutum.

    Bacci ya ci ƙarfin tela har ya hana shi aiki.

    Ya tafi lazumi.

    Ya tafi yin addu’a.

    Ya tafi ya kwanta domin yin bacci.

    Ya yi fakare.

    Ya yi sakaƙe/kurum.

    Ya tara kayan mutane da yawa bai ɗinka ba, kuma ya gudu.

    Laho ne.

    Rago ne.

    Ba ya zuba mai a janareta sai wani ya zuba ya tayar da janaretan sai shi kuma ya lalaɓo  ya yi amfani da shi.

    3.3 Alamomi

    Bayan furucin baki, teloli sukan yi amfani da alamomi domin sadarwa. Amfani da alamomi sananne ne kuma sababben al’amari. A wannan bagire, teloli sukan yi amfani da ire-iren alamomin bisa manufofi mabambanta, ba kamar yadda aka san su a maganganun yau da kullum ba. Waɗansu daga cikinsu su ne:

    A. Shafa kai

    A sadarwar yau da kullum, shafa kai na nuni ga jin kunya. Ga telolin Gusau kuwa, idan tela ya shafa kai to yana ishara ne ga ‘yan uwansa teloli cewar bai kammala aikin kwastoman da ya zo ba. Hakan zai ba da damar ‘yan uwan aikin nasa su ƙirƙiri hanyar da za su ɓullo wa kwastoman domin ba shi uzuri.

    B. Ƙulli/Ɗauri

    Ɗaurewa ko ƙulle igiya ko tsumma ko leda, da sauransu, ba ɓoyayyen al’amari ba ne. Abu ne da ake gudanarwa yau da kullum. Sannan ba dole ne ya kasance yana da wata ma’ana ta musamman ba. Ga teloli kuwa, akwai nau’ukan ƙulli da ake yi wa kaya da ke ba da maana ta musamman. Misali, tela na iya yin salon ɗauri a kayan kwastoma domin nuna wa sauran abokan aikinsa cewa ko mai kayan ya zo kada a ba shi su domin mai kayan bai biya kuɗin aiki ba.

    3.4 Kalmomi masu alaƙa da nauin ɗinki

    Wani ɓangare kuma na Hausar telolin garin Gusau shi ne abin da ya shafi nau’ukan ɗinki. Kowanne daga cikin rukunonin teloli da ake da su, suna da keɓantattun kalmomi da suka shafi nau’in aikinsu. Wannan ya haɗa tun daga kan kayan aiki zuwa yanayin gudanar da aikin, har abin da ya shafi kayayyakin da ake samarwa. Za a kalli waɗannan kalmomi ƙarƙashin waɗansu rukunonin teloli da ake da su a garin Gusau.

    3.4.1 Kalmomin telolin taka-taka

    An kawo taƙaitaccen bayani game da telolin taka-taka a ƙarƙashin A da ke ƙasan 2.1 a sama. Akwai kalmomi da suka fi keɓanta ga waɗannan teloli. An kawo waɗansu daga ciki a ƙarƙashin jadawali na 4 da ke ƙasa.

    Jad 4: Kalmomin telolin taka-taka:

    Kalma

    Ma’anar Asali

    Sabuwar Ma’ana

    Keke

    Laulawa

    Keken Ɗinki

    Guru

    Abin da ake ɗinkawa da fata a ɗaura a damatsa domin kariya ko buwaya.

    Bel ɗin da yake juya keken ɗinki, ko kuma nau'un ɗinki.

    Raƙumi

    Nau’in dabba

    Wani dogon ƙarfe da ke tare da gyaren ƙasa.

    Takalme

    Takalmi

    Abin da yake danne ƙyalle yayin ɗinki.

    Buzuzu

    Wani nau’in ƙwaro

    Wani abu a fuskar keke wanda zare kan shiga cikinsa yayin ɗinki.

    Baka

    Ɗan ice mai lanƙwasa da ake ɗaurawa zare mai ƙarfi wanda cikinsa ake ɗana kibiya domin harbawa.

    Ƙarfen keken ɗinki ne da ke yin sama da ƙasa yana jan zare yayin ɗinki.

    Haƙori

    Sashe ne na cikin baki masu zubin fararen ƙasusuwa da ke jere sama da ƙasa, waɗanda da su ake taunar abinci.

    Wani ƙarfe mai kamar haƙori mai jan yadi idan ana ɗinki.

    Laka

    Ƙashin gadon baya.

    Wani ƙarfe ne a ƙasan keke mai noti ko ƙusa.

    Ƙundu

    Ciki ko tumbi

    Wani ƙarfen keke ne zagayayye wanda a kan sa ƙoshiya a ciki.

    Giya

    Barasa – abin sha da ke saka maye

    Ƙarfen keke ne a gefen dama wanda ake ribas da shi.

    Hannu

    Ya shafi wani sashe na jikin mutum

    Ƙarfen keke ne a gefen dama wanda ake ribas da shi.

    Kwabo

    Nau’in kuɗi da aka taɓa amfani da shi a Nijeriya

    Wani ƙarfe ne mai ɗan faɗi na wajen haƙori.

    Fuska

    i. Duba fuskar mutum ko dabba.

    ii. Ɓangaren da ke gaba na wani abu kamar gida.

    Ƙarfen keke ne a gefen hagu, na ɗauke da buzuzu wanda ya rufe gaban keken.

    Doki

    Nau’in dabba da ake hawa

    Bodin keken ɗinki, wato gun da ake ɗora kan keken

    Sanda/ Sanduna

    Busasshen dogon itace da yawanci ake ferewa a gyara

    Dogayen ƙarafunan da ke ɗauke da takalme ko allura.

    Tushen bayani: Hira da teloli

    Bayan waɗannan, akwai kuma kalmomi da ke da alaƙa da nauukan ɗinki da telolin taka-taka ke yi. Sun haɗa da:

    ‘Yar-Shara: Nau'in riga ce wadda ba ta da hannuwa. Tun tuni Bahaushe na da wannan nau’in riga. Duk da haka, akwai sauye-sauye na kwalliya da salo da ake yi wa rigar a zamanance.

    ‘Yar-Bunguɗu: Nau’in riga ce da hasashe ya nuna cewa ta samo asali ne daga fasahar telolin Bunguɗu.

    Buba: Nau’in rigar mata ce marar kwalliya da ke da zagayayyen wuya.

    Ɗan-Itori: Nau’in wando ne da ake yi wa ƙarin hantsa har ƙasa.

    Adda: Waɗansu ƙyallaye ne da ake ƙara wa babbar riga ko riga yar-shara a gaba da baya.

    Sace: Babbar riga ce mai kama da ‘yar shara wadda ake yi wa ƙari.

    Tsefewa: Warware ɗinki (misali, warware wani ɗinki da aka yi domin gyarawa)

    3.4.2 Kalmomin telolin barnina (fonis)

    Telolin Barnina wato Fonis na da sunaye na musamman da suka shafi nau’ukan ɗinkunan da suke samarwa da matakan gudanar da ɗinkunan. Sun haɗa da:

    Jad 5: Kalmomin telolin barnina (fonis) da ma’anoninsu:

    Kalmomi

    Ma’anonin da maɗinka suka ba su

    Kika

    Nau'in ɗinki ne mai kama da haƙori.

    Kwashe

    Ɗinki ne mai ɗan tsawo da faɗi.

    ‘Ya’ya

    Ɗigagga ne da ake yi domin gyaran ɗinki.

    Sharaba

    Wata tufkar zare ce wadda ake sa wa aiki.

    Singa

    Ɗinki ne mai kama da na taka-taka.

    Zubi

    Wannan na nufin fitar da sigar aikin da za a yi.

    Ɗauri

    Yin ɗinkin sama na kwashe

    Ciko

    Yin kwalliyar aiki bayan zubi

    Fulawa

    Fitar da kwalliya masu kama da fulawa a jikin ɗinki

    Zaga-Zaga

    Nau’in ɗinki kwashe ne da ake yin sa wara-wara

    Madogara: Hira da teloli

    3.4.3 Kalmomin telolin cunko da aikin sama

    Telolin Cunko da na Aikin Sama na da kalmomi na musamman da suke amfani da su. Waɗannan kalmomi sun shafi yanayin aikinsu da kayan aikinsu da kuma nau’ukan kayayyaki da suke ɗinkawa. Za a iya lura da cewa, kai tsaye kalmomin na da ma’anoni na musamman, saɓanin waɗanda aka san su da su a magana ta yau da kullum. Daga cikin kalmomin akwai:

    HarsheƘarfe ne a fuskar keke wanda shi yake motsa keken.

    SitiyariWani ɗan ƙarfe ne mai ƙululu a ƙasan kekeDa shi ake sarrafa keke lokacin aiki.

    Satila: Ɗan ƙarfe ne wanda shi ke rarrabewa tsakanin zaren ƙasa  da na sama.

    Dawakai: Ƙarafa ne gaba da baya waɗanda sukan sarrafa keken ɗinki gaba ɗaya.

    Baka:     Telar (keken) sama ne kawai ke da shiƘarfen keke ne da ke jan zare.

    GuiwaSunan ƙarfe ne wanda ke sarrafa dawakai.

    BuzuzuAbu ne da ke sarrafa saƙar keke.

    KunneWani ƙarfe ne wanda ke saman fuskar telar (keken) sama.

    KorkoroWani ƙarfe ne mai kwararo wanda ake zura zare a cikinsa.

    ƘunduƘarfen keke ne wanda yake ƙarƙashin keken ɗinki inda ake sarrafa zaren ɗinki.

    Aska:     Sunan ɗinki ne da ake yi wa babbar riga.

    Wundi: Aiki ne da akan yi wa wata riga mai zagayayyen wuya

    Kaftani: Aiki ne da ake yi wa wuyan rigar maza.

    ZabuniSunan kaya guntaye (marasa tsayi) waɗanda mafi akasari jinin sarauta kan sa. Akan yi musu cunko ko aikon sama.

    TimbuktuSunan wani nau’in aikin cunko ne.

    Buba:    Aikin cunko ne na mata.

    4.0 Sakamakon bincike

    Wannan bincike ya gano cewa, telolin suna da wata hanyar sadarwa a tsakanin junansu, wadda idan mutum bai san wannan sirrin magana ba, to ba zai iya fahimtar saƙon da ake isarwa ba. Duk da haka, salailai da sigogin da ake furta maganganun sun bambanta daga shago zuwa wani shago. Haka kuma, akan samu bambancin ma’anar kalmomi tsakanin nau’ukan teloli daban-daban da ake da su. Hakan kuma na faruwa ne musamman sakamakon bambancin kayan aiki da yadda ake gudanar da aikin.

    Waɗansu daga cikin kalmomi da jimlolin da ake samu cikin Hausar teloli sun kasance akwai su a Hausar yau da kullum. Bayan an ɗauke su, sai aka ba su waɗansu ma’anoni na daban. Misalansu sun haɗa da “ƙundu da kunne da buzuzu da sauransu. Wannan kuwa ya yi daidai da iƙirarin hanyar da aka ɗora aikin ta “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” Kuma hakan ya bayyana cewa, teloli sun samar da kuka na musamman a gidansu, wato sana’ar ɗinki. Bayan su kuwa akwai waɗanda ƙirƙira ce kai tsaye, wato ba a san kalmar ba a Hausar gama-gari. Daga cikin misalansu akwai sharaba da dinga.

    Lura da waɗannan bayanai, ana iya taƙaita cewa:

    a.       Hausar teloli na iya bambanta da sananniyar Hausa ta fuskar kalmomi ko jimloli.

    b.       Kalmomin da ake samu cikin Hausar teloli na iya kasancewa ƙirƙirarru, ko kuma waɗanda ake da su a Hausar asali amma sai aka ba su waɗansu ma’anoni na daban.

    c.        Ana amfani da Hausar teloli wajen fayyace sunayen abubuwa ko bayanin waɗansu al’amura da ke faruwa ko kuma domin sakaya zance.

    A bagiren al’ada, Hausar teloli na iya kasancewa wata hanya ta gulma da zunɗe da ƙulla munafurci da yaudara. Tana iya zama hanyar ƙulla damfara da zamba ga abokin kasuwanci ko da kuwa a gaban idonsa ne. Duk waɗannan kuwa halaye da ɗabi’u ne da suka ci karo da koyarwar al’adun Hausawa nagartattu.

    5.0 Kammalawa

    Sana'ar ɗinki sana'a ce mai daɗaɗɗen tarihi a ƙasar Hausa, wadda takan samar da tufafi da danginsu ga al'ummar Hausawa. Ta tattara abubuwan nazari a fannin ilimi, musamman idan muka yi la'akari da fannonin nazarin harshen da al'ada. Nazarin Hausar kalmomi na iya taimaka wa fagen nazarin harshen Hausa da sababbin kalmomi tare da bunƙasa farfajiyar nazarin walwalar harshe, musamman abin da ya shafi Hausar rukuni ta sana’a. Ta fuskar al’ada binciken zai kasance hannunka mai sanda game da gyaran halaye da ɗabi’un da suka shafi damfara da zamba da ƙarya da gulma da munfaruci da sauran munanan ɗabi’u da halaye makamantan waɗannan. Bayan haka, ankararwa ne ga sauran al’umma domin fahimtar wainar da ake toyawa.

    Manazarta

    1.       Alhassan H. da wasu, (1984). Zaman Hausawa, na biyu. Nothern Nigeria Publishing Company.

    2.       Bashir, A. (2012). The Morphosyntax of Diminutive in Hausa. [Kundin digiri na ɗaya da ba a wallafa ba]. Jami’ar Bayero, Kano, Nijeriya.

    3.       Bashir, A. & Sambo, M.W. (2021). “Suffixation and Reduplication in Zamfara Dialect of Hausa Language”. Interdisplinary Approach to the Study of African Languages. Festschrift in Honour of Francis Egbokhare. ISSN: 978 – 978 – 966 – 297 – 5. Pp236-243.                                                 

    4.       Bunza A.M. (2004). Waƙƙƙen ƙa'idojin rubutun Hausa. Ibrash Islamic Publication Center Ltd.

    5.       Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a farfajiyar adabi da aladun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720-727.

    6.       Bunza, A.M(2017). Dabarun bincike a nazarin harshe da adabi da al'adun Hausawa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    7.       Garba, C.Y(1991). Sana'o'in gargajiya a ƙasar HausaBaraka Press and Publishers Limited.

    8.       Muhammad, A. (2021). Sana'a sa'a: Yankan farce a garin Gusau[Kundin digiri na farko da ba a wallafa ba]. Jami’ar Tarayya Gusau, Zamfara, Nijeriya.

    9.       Muhammad, M.S. (2020). Bahaushiyar al’ada. Bayero University Press.

    10.    Sani, A-U. (2022). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya. www.doi.org/10.13140/RG.2.2.24862.61764.

    11.    Sani, A-U., Buba, U. & Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara...: Biɗa da Tanadi a tsakanin Hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, (1)2, pp44-50. https://www.gajrc.com/media/articles/GAJHSS_12_44-50_aLnXk46.pdf.

    12.    Yahaya, S. U. (2021). Damben Hausawa a zamanance [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.



    [1] Sani, Buba, & Mohammad, (2019 p. 44) sun bayyana cewa “Hasali ma, Hausawa sun shahara ta fuskar noma da kasuwanci da fatauci da sauran sana’o’i daban-daban. Ficen da Hausawan suka yi a ɓangaren sana’o’in fatauci da kasuwanci ya taimaka matuƙa wajen bazuwarsu zuwa wurare daban-daban. Hausawa sun  kafu a ire-iren waɗannan wurare tare da cigaba da gudanar da sana’o’insu.

    [2] A can da, sana'ar ɗinki sai ɗan gado. A yanzu kuwa, ana koyo a cibiyoyin koyar da sana'o'i da shagunan ɗinki daban-daban. Wannan dama ce ga kowa. Hakan ne kuma ya sa ake samun ƙaruwar gasa a cikin sana’ar.

    [3] Akwai ayyuka daban-daban da aka ɗora su a kan Bahaushiyar hanyar gudanar da bincike. Daga cikinsu akwai Bunza, (2019) da Sani, Buba, & Mohammad, (2019) da Yahaya, (2020) da Sani, (2022).

    [4] Akwai shagunan teloli a dukkannin waɗannan yankuna da aka ambata. A cikinsu, wurare biyu da suka yi fice a matsayin cibiya ko matattarar maɗinka su ne Bakin Kasuwa Gusau da Sabongari.

    [5] Kalmar sana’a ba sabuwa ba ce ga Bahaushe. Tana nufin hanyar amfani da fasaha da hikima da kuma kayan aiki domin sarrafa wani abin amfani da za a iya sayarwa ko a musanya da wani abu mai daraja. Domin samun ƙarin bayani game da sana’a da kasuwanci, ana iya duba Muhammad, (2020).

    [6] Mafi akasarin telolin Gusau ‘yan ci-rani sun fi tafiya kudancin Nijeriya da kuma wajen ƙasa, kamar Libiya da Nijer da Togo da sauransu.

    [7] Sana’ar ɗinki na da matuƙar amfani a ƙasar Hausa. Daga cikin amfaninsa akwai (i) samar da tufafi da danginsu ga al'umma da (i) samar da rufin asiri ga masu sana’ar da (iii) hana zaman banza tsakanin al'umma da (iv) samar da kuɗin shiga ga hukuma da (v) kyautata mu'amula tsakanin al'umma, da sauransu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.