Tuwon Rogo/Alabo
i. Dawa
ii. Rogo
iii. Ruwa
Tuwon alabo yana da bambanci da sauran nau’o’in tuwo da aka yi bayani a sama. Alabo dai rogo ne da aka fere aka shanya ya bushe. Za a daddaka busasshen alabon a turmi domin ya zama Æ™anana. Daga nan sai a kai shi niÆ™a inji. Bayan an dawo da shi, za a tankaÉ—e.
A gefe guda kuwa, za a É—ora ruwa
kan tukunya. Bayan ruwan ya tafasa, za a yi talge
amma da garin dawa. Bayan talgen ya nuna, sai a tuƙa tuwon da wannan garin rogo da aka tankaɗe.
Sai dai ba a sanya ruwa sosai a wannan nau’in tuwo. Bayan an tuÆ™a, za a rufe domin ya sulala, daga nan
sai batun kwashewa.
Tsokaci
Tuwon rogo na da daɗin ci ga tsofin da ba su da haƙora. Wannan na faruwa ne a adalilin
laushin da tuwon ke da shi. Ana iya haÉ—iye shi ba tare da taunawa sosai ba. An fi cin wannan nau’in tuwo da miyar yauÆ™i, wato irin su lalo da karkashi.
Tuwon Semo
i. Ruwa
ii. Samonbita
Zamani ne ya zo da garin samo, kuma ana sayar da shi ne a shaguna. Akwai waÉ—anda ke zuwa a buhuna, akwai kuma na cikin fakiti. Bayan
an É—ora ruwan zafi, kafin a saka garin samo za a rage
tukunyar a jiye a gefe. Kafin a sanya garin cikin ruwa, sai an kwaɓa shi da ruwan sanyi sannan a zuba shi cikin ruwan zafin. Za a rufe ya ɗan dafu kafin a buɗe a tuƙa. Bayan nan ma za a rufe domin ya sulala, sannan a sake
tuƙawa, sai batun kwashewa.
Bayan wannan hanya, ana iya yin talge sai kuma a zuba
sauran gari. Yadda ake talgen kuwa shi ne, za a
deɓi garin semon kaɗan a kwaɓa sannan a zuba cikin tukunyar. Bayan
ya ɗafu sai a riƙa barbaɗa sauran garin ciki sannan a tuƙa. Za a bar shi ya sulala, sai kuma a
sake tuƙawa kafin a
kwashe. Ana cin wannan nau’in tuwo da kusan kowace irin miya. Sai dai ya fi daÉ—i da miyar yauÆ™i.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.