Ta Kashe ’Yarta Da Kuskure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

     Assalamu Alaikum. Yarinyata ce ’yar watanni goma sha-huɗu ta farka daga barci tana son shan ruwa. Akwai ruwa a cikin gorar faro a tsakar ɗaki sai na ɗauka na ba ta. Ashe ba ruwa ne a ciki ba, ‘hydrogen’ da mata suke yin lalle da shi ne! Tana gama sha sai ga kumfa ta bakinta, daga nan sai mutuwa. To ko akwai azumin kaffara a kai na?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Daga wannan bayanin, ya fito a fili cewa, wannan kisa na kuskure ne. Ba na-gangar ko mai kama da gangar ba. Kuma abin da Allaah Ta’aala ya ce shi ne

    وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٍ أَن یَقۡتُلَ مُؤۡمِنًا إِلَّا خَطَـࣰٔاۚ وَمَن قَتَلَ مُؤۡمِنًا خَطَـࣰٔا فَتَحۡرِیرُ رَقَبَةࣲ مُّؤۡمِنَةࣲ وَدِیَةࣱ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰۤ أَهۡلِهِۦۤ إِلَّاۤ أَن یَصَّدَّقُوا۟ۚ

    Kuma wanda ya kashe mumini a bisa kuskure to sai ya ’yanta baiwa mumina, kuma ya bayar da diyya ga iyalinsa, sai dai ko idan sun yi sadaka da hakan (sun yafe). (Surah An-Nisaa’i: 92)

    Har zuwa inda ya ce

    فَمَن لَّمۡ یَجِدۡ فَصِیَامُ شَهۡرَیۡنِ مُتَتَابِعَیۡنِ تَوۡبَةࣰ مِّنَ ٱللَّهِۗ

    Kuma wanda bai samu hakan ba sai ya yi azumi na watanni biyu a jere. (Surah An-Nisaa’i: 92)

    Don haka abin da ke a kan wannan baiwar Allaah shi ne

    1. Diyyar kuɗi dinar dubu guda (kusan daidai da N93,912,000.00 a yau), kamar yadda yake tun a zamanin Khalifah Umar Bn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu). Haka Al-Imaam Abu-Daawud (4519) ya riwaito, kuma Al-Albaaniy a cikin Al-Irwaa’u: 2247 ya hassana shi.

    Dangin matar waɗanda suke mawadata masu cin gadonta ne za su tara kuɗaɗen domin a biya masu gadon marigayiyar, watau mahaifinta da ’yan uwanta ban da mahaifiyarta. Sai dai ko in sun yafe mata.

    2. Sai kuma ta yi kaffara da ’yanta bawa mumini ko baiwa mumina. Idan kuwa ba ta samu iko ba, sai ta yi azumin watanni biyu a jere.

    Akwai fatawar da As-Shaikh Ibn Baaz (Rahimahul Laah) ya amsa a kan mahaifin da ya take ɗansa da mota a bisa kuskure, wadda ta yi kusan kama da wannan.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    08164363661

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.