TAMBAYA (99)❓
Mal usman wai Dan ALLAH da gske
yan izala ne suka kawo rabuwar kawanan musulmi a Nigeria???
AMSA❗
Alhamdulillah
Amsar nan zata fito ne idan aka
duba menene asalin ita kanta Izalar
Izala kalmace ta larabci da take
nufin "kawar da" kuma cikakken sunanta shine "Izalatil Bidi'ah
wa iqamatis Sunnah" ma'ana "Kungiyar kawar da Bidi'ah da tsayar da
Sunnah", kenan kamata yayi kowa ya zamo dan Izala tunda ai duk musulmi na
kwarai zai so ya kawar da Bidi'ah kuma ya tsayarda Sunnar Annabi Sallallahu
alaihi wasallam, kungiya ce da marigayi Isma'ila Idris bin Zakariyya ya kafa ta
a shekarar 1978 a jihar Plateau Jos, sakamakon hana shi yada Da'awah da
gwamnatin zamaninsa tayi ba tare da qungiya ba, a lokacin da ya ajiye aikin
soja
Dalilin da yasa ya kirkiri
Jama'atu Izalatul Bidi'ah kenan, ya nemi shawarar Sarkin Musulmi na lokacin
amman yace masa yan Bidi'ah fa zasu kashe ka, yace na amince indai har za'a
yaqi Bidi'ah. Yace masa to ai bazai yiwu ka kawar da Bidi'ah ba tare da tsayar
da Sunnah ba, sai yace ka cike sunan da "Wa iqamatus Sunnah" ma'ana
"Da tsayar da Sunnah"
An haifi Malam Ismaila Idris a
kauyen Goskorom dake garin Plateau, Jos, a shekarar 1937. Mahaifinsa ya koyar
dashi har zuwa lokacin da yakai shekaru 15, daganan ya koma Bauchi inda yayi
karatun soro a hannun: Shaikh Magaji, Shaikh Kansurawa, Shaikh Mahmud Bello
(Limamin babban masallachin Bauchi), daganan ya koma Kano inda yayi degree a
bangaren Islamic Studies. Daganan ya sake komawa Bauchi ya fara aiki a primary
school. A 1969 ne, ya koma Kaduna, yayi shekaru 5 a matsayin Murshid (Mai bada
shawara a kungiyar Jama'at Nasr al-Islam) inda ya fara da'awah yana sukar
sufaye, saboda kausasawa a maganganunsa aka cire shi aka maida shi gidan Yarin
Kakurdi dake Kaduna
Daga nan kuma ya shiga soja
(Nigerian Army) inda aka nadashi Imam bayan yabar kungiyar Jama'at Nasr
al-Islam a shekarar 1974. Lokacin da yana soja ne ya kara samun damar isar da
da'awah ka'in da na'in hakan kuma ya zame masa qalubale, har aka yi masa
tranfer zuwa Ibadan, inda yayi watanni 3 kacal saboda hatsaniya da ya samu
tsakaninsa da Divisional Imam/Lt. Colonel akan bayar da Zakka. Daganan aka kara
maidashi Kontagora. A Kontagora mutane suka fara halartar masallachin sojoji na
Juma'ah la'akari da limamin sufi ne. Anan ma dai suka kara samun sa'insa silar
yanda yake da'awah, aka kara yi masa transfer zuwa tsohon wajensa, Jos. Anan
aka bashi Imam, ya ci gaba da yada da'awar sa tare da caccakar sufaye
Salon da'awarsa a ja hankalin
al'ummah da yawa, kuma har gayyatar sa ake garuruwa don yada da'awah. Kungiyar
Sufaye sun gaji da jin suka, nan da nan suka kai karar Shaikh Ismaila zuwa ga
Ministry of Defence. Duk da cewar ya samo goyon bayan Major Alhassan amman an
umarce shi da ya daina wannan da'awar da yake yi. Saboda yawan karya wannan
dokar da aka saka masa ne aka kore shi daga aikin soja a shekarar 1978. A haka
ya ci gaba samun magoya baya musamman daga Tijaniyya wanda silar wannan
daukakar ne ya kafa kungiyar Izala
Sannan kuma Shaikh Ismaila Idris
ya qalubalanci Sadaqat al-yawm al-thalit (sadakar 3) da Sufaye suke yi idan
mutum ya rasu. Da kuma addu'o'in da sufaye suke taruwa suyi kwana 7 da kuma
addu'ar 40 da ake yi. Da kuma lazimi da Tijaniyya suke da carbi, wasu suna 100
a kullum wasu kuma har 1,000. Da kuma irinsu ziyarar maqabartun shaihunnansu da
sufaye domin neman tabarraki, da khalwa (wanda suke cewa suna kebewa ne da
Allah) duk Shaikh Ismaila ya qalubalanci wannan ayyukan na bidi'ah
Haka kuma Izala ta tabbatar da
cewar Allah Azzawajallah ne kadai yasan ilimin gaibu, kuma Annabi Sallallahu
alaihi wasallam ne kadai yake iya bayyana mu'ujiza, kuma duk musulmai daya ne
(sai wanda yafi wani tsoron Allah), kuma sufanci shirka ne, kuma ba'a ganin
Allah a mafarki ko a zahiri (Saidai a Aljannah). Aqidar Izala shine duk wani
sabon abin da aka sako a addini to wannan bidi'ah ne, amman kofar ilimi da
ijtihadi a bude suke amman da hujja qwaqqwara
Izala ba da iya littafin
"Kitab al-tawhid" wallafar Shaikh Muhammad b. Abd al-Wahab (1703 -
1792) take amfani ba, saidai kungiyar tana amfani da littattafan magabata
irinsu: Ibn Taimiyya, Ibn al-Qayyim, Ibn Khathir, Ibn Abi Zayd al-Qayrawani da
wasu manyan malaman Ahlus Sunnah. Izala na bin mazhabin Malikiyya ne
Idan kuma muka koma tarihi zamu
tarar da cewar;
Daya daga cikin muhawarar da aka
tafka a 10 ga watan April na shekarar 1978, shine akan maganar Federal Shari'ah
Court of Appeal (FSCA) wato Kotun Shari'ar Musulunci ta Tarayya. A lokacin da
shugaban committe na majalissar zartarwa ya kawo muhawarar (debate) akan
shari'ah har aka buqaci za'a goge Section 180 (1) C - da suka saka masa
"Shari'ah Paragraph daga Tsarin Constitution" (wanda kamata yayi
shari'ar musulunci ace tana sama da constitution), wakilan musulmai suka
harzuqa suka fita daga majalisar
Tsohon shugaban kasa (Head of
State), Olusegun Obasanjo, ya buqaci duk wadanda suka tafi dinnan su dawo a ci
gaba da muhawarar. Bayan sati biyu, majalisa ta ci gaba da zartar da wancan
qudurin a 24 ga watan August, 1978. An qaddamar da sabon constitution zuwa ga
shugaban kasa ba tare da sashin shari'ah ba (FSCA) wanda daga baya aka shigar
dashi a 1 ga October, 1979
A karkashin sashi na: 240 (1),
doka tace: "Kowacce jiha dake karkashin gwamnatin tarayya akan ta zartar
da Shari'ah Court of Appeal
A wannan lokacin da Izala ta kafu
ne al'ummar musulmai suka kula da ci gaban daukakar Shaikh Abubakar Mahmud Gumi
(1922 - 2992), wanda manufarsa shine dirkake tare da shafe aqidar sufanci. Ba
wai a iya rubuce-rubucen sa na Hausa ya qalubalanci sufaye ba, har ma da
Tafsiransa da yake gabatarwa a gidan Radio na Kaduna, tsakanin 1970 zuwa 1974
Wallafar littafin sa mai suna
"al-aqida as-sahiha bi muwafaqat ash-shari'a (Imani a mahangar shari'ah)
ya janyo yaqi akan yan Bidi'ah, a shekarar 1972. Da kuma yan Tijaniyya da
Qadiriyya. Shaikh Nasiru Kabara (1925 - 1996), shugaban Qadiriyya a Nigeria,
wanda daga baya ya zama shugaban kungiyar na Africa, a wannan shekarar ne shima
yayi raddi ta hanyar wallafa littafinsa "kitab al-nasiha al-sahiha
fi'l-radd 'ala al-aqida al-sahiha" (Shawarar gaskiya akan sahihiyar aqida)
Haka shima batijjane Sani Kafinga
ya wallafa nashi: "al-Minah al-hamida fil-radd ala-fasid al-aqida"
(Kyaututtukan yabo zuwa ga wanda yake da naqasu a imaninsa)
Shaikh Gumi, bai rubuta wancan
littafin don kowa ya karanta ba saboda a ganinsa fassara shi zuwa harshen hausa
zai zama wani baqon abu a wancan lokacin. A lokacin da dalibinsa, Mallam
Isma'ila Idris (1937 - 2000), wanda malamin makaranta ne a da can, mai
karantarwa a masallachin Sultan Bello dake Kaduna, ya dinga debo hujjoji daga
cikin littafin Shaikh Gumi ya fara sukar sufaye, silar haka aka fara muhawara
mai zafi a yankunan da ake musulunci a kasa baki daya
Banbancin dake tsakanin Shaikh
Gumi da dalibinsa Malam Ismaila Idris shine, shi Shaikh Gumi ba ya kama sunan
kungiya kai tsaye saidai yayi jirwaye mai kamar wanka, yayin da shi kuma
Ismaila Idris kai tsaye yake cewa: Abu kaza haramun ne, wannan yayi karo da
sunnah, wane kafiri ne
(Duba Ostien, 2006 page 240)
Domin wasu karin bayanan game da
rayuwar Shaikh Gumi, duba: Loimeier, Roman, Islamic Reform da kuma Political
Change in Northern Nigeria, Evanston-Illinois: Northwestern University Press,
1997, pages na 148–171; da kuma tarihinsa, Sheikh Abubakar Gumi tare da
Ismaila. Tsiga, Where I stand, Ibadan: Spectrum Books Limited, 1992. Da kuma
Loimeier, 1997, page na 163
An tursasa Malam Ismaila Idris ya
daina koyarwa, a lokacin Shaikh Gumi yana Saudiyya, har ya dawo Kaduna ana ci
gaba da wannan taqaddama, Malam Ismaila yayi retire amman ya ci gaba da yada
da'awar: "al-aqida al-sahiha"
A takaice Izala ta kawo hadin kai
ga musulmi saboda an fahimci Sunnar Annabi Sallallahu alaihi wasallam sakamakon
kafata kuma kungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a
Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa
A yanzu haka, Dr. Abdallah Bala
lau shine shugaban ta na kasa baki daya
A karshe ina son mu tuna cewar,
su fa Mala'iku zasu tambayi mutum menene addininsa bawai minhaj dinsa ba
Muna roqon Allah ya rabamu da
bidi'ah ya tabbatar damu akan bin sunnar Annabi Sallallahu alaihi wasallam bisa
fahimtar magabatan farko (Salaf)
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.