Gabatarwa
A ƙarƙashin 17.0 an kawo bayanai dangane da nau’o’in ‘ya’yan itatuwan Bahaushe na gargajiya. A cikin babin na goma sha bakwai, an kawo ire-iren ‘ya’yan itatuwa da wasu nau’o’in saiwowin na gargajiya da Bahaushe yake amfani da su tun shekaru aru-aru. A wannan babi kuwa, za a mayar da hankali ne kan saiwowi da ‘ya’yan itatuwan da ba na gargajiya ne zalla ba ga Bahaushe. Sun kasance haka ne a dalilan ko dai Bahaushe ya same su ne daga baƙin al’ummu ko kuma ba a ƙasarsa ake shuka su ba. Wannan babi na ɗauke da misalansu tare da ɗan tsokaci dangane da kowanne.
Abarba
Ita ma abarba a ƙasa take haihuwa. Ganyenta daga sama
na kasancewa ɗan kaɗan.
Takan girma sosai har takan
fi gwanda. Ɓawon bayanta na
da ƙarfi sosai, sannan na da launin runwan
ƙasa-ƙasa. Cikinta kuwa ruwan madara ne. Ana shan abarba haka
nan, sannan ana sarrafa ta cikin wasu launukan lemo.
Ayaba
Ayaba bishiya ce da ba ta da rassa. A maimakon haka,
tana fito da wasu tsiro ne daga jikinta ta gefe. Yawanci, idan ayaba ta yi haihuwa guda kawai takan mutu ko a sare ta. Daga nan sai sauran tsiron da
suka fito gefenta kuma su ci gaba da girma. Su ma kowanne za ta yi haihuwa guda ɗaya
sannan sai
a sare ta.
Haka abin zai ci gaba.
’Ya’yan
ayaba na kasancewa a jere reras jikin abin da ake ce wa nonon ayaba.
Bayan sun ƙosa (wanda har lokacin da suka ƙosa launinsu na kasance kore), sai a
yanke wannan nonon a ruɓa
shi ta hanyar sanyawa cikin buhu ko babbar leda ko wani abu mai kama da haka,
sannan a ajiye cikin ɗaki.
Da zarar
ta ruɓa, za a ji ƙamshinta na tashi. A wannan lokaci
launinta na komawa ruwan ɗorawa.
Cikinta kuwa fari ne yayin da aka ɓare ta. Ana cin ayaba haka nan ko kuma a
sarrafa ta
cikin wasu nau’o’in lemo
Agwaluma
Wannan ma ɗan bishiya ne. Launin bayanta ja ne, sai dai akan samu
launin ruwan goro. Yawanci, a
cikinta akwai ’ya’ya huɗu ko biyar. Ɗanɗanonta
na da ɗan tsami-tsami; sannan kuma tana da ɗanƙo.
Dankali
Wannan na ɗaya daga cikin abincin Bahaushe da ke cikin rukunin saiwoyi. Akwai nau’o’in dankali guda biyu, wato dankalin Hausa da kuma dankalin Turawa. A ƙarƙashin 17.4 an yi
bayanin dankali. A nan kuma ana magana ne kan dankalin Turawa. Shi ne nau’in
dankalin da ba a cika shuka shi a ƙasar Hausa ba. A
Nijeriya, an fi shigo da shi daga Kudancin ƙasar.
Ɗan Furut
Ɗan furut bishiya ce da ke da rassa a
cikin ƙasa. Sannan
bishiyar na da tsawo sosai.
‘Ya’yan bishiyar na da launin kore kamin su nuna. Idan
suka nuna,
launinsu yakan koma
ja. Kamar sauran
‘ya’yan bishiya, shi ma ɗan furut a cikinsa akwai ƙwallo
mai girma wanda kuma yake da
launin ruwan
madara.
Faru
Faru yana kama da inibi, sai dai tsarin launinsu ya bambanta, saboda shi faru launinsa ya fi kama da ruwan
ƙasa. Sannan inibi ya fi shi girma. Ɗanɗanonsa
na ɗauke da tsami-tsami da zaƙi-zaƙi.
Gazari
Gazari yana da launin ruwan ƙasa-ƙasa. Cikinsa ma idan aka ɓare,
yana da irin wannan launin na ruwan ƙasa-ƙasa. Yana da ɗan tsawo amma bai kai na rogo ba. Haka ma kaurinsa bai kai na rogo ba. Ana
dafa shi ne tare da gishiri, kuma
sannan ana
cinsa haka nan.
Gwandar Masar
Gwandar Masar bishiya take yi mai rassa. ’Ya’yan suna da
siffar abarba daga ɓangaren bayansu. Sai dai su gewayayyu ne
kamar lemo. Launin
bayanta kore ne, kuma sannan cikinta yana da launin fari ko ruwan madara. Ana shan ta
haka nan bayan an
ɓare bayan.
Inibi
Inibi, ’ya’yan bishiya ne da ya yawaita a ƙasar Hausa. Sai dai mafi yawa shigo da shi ake
yi daga ƙasashen ƙetare. ’Ya’yansa ƙanana ne masu launin ja da baƙi-baƙi.
Kukumba
’Ya’yan kukumba na da ɗan tsayi,
launin jikinta kuma kore ne. Ana iya fere shi a yayyanka, sannan a ci haka nan. Akwai nau’o’in abinci da dama da ake haɗawa da shi a matsayin sinadari,
ciki har da wasu samfuran lemo (kamar dai yadda aka yi bayani a sama). Yanayin cikinsa duka nama ne, wato ba shi da
’ya’ya.
Kashu
Kashu bishiya ce da take da tsayi tare da girma da kuma rassa.
’Ya’yanta na kasancewa korra
kafin su nuna. Idan sun nuna kuwa, launin na komawa ja ko ruwan ɗorawa. Ana shan kashu haka nan, sannan ana iya sanya shi
cikin wasu nau’o’in lemo.
Kwakwa
Kwakwa nau’o’i biyu ce kamar haka:
Akwai babbar kwakwa, akwai kuma kwakwar manja. Dukkaninsu bishiya suke yi mai tsayi, amma ba
su da rassa. Babbar kwakwa tana da ƙwallo
mai ɗan girma. Bayan ƙwallon yana da launin ruwan ƙasa-ƙasa
tare da ɗan zare-zare. Ɓawonta yana da ƙarfi sosai. Idan aka fasa shi, cikinsa yana da launin ruwan ƙasa-ƙasa. Idan
aka ƙara fasa wannan cikin mai launin
ruwan ƙasa- ƙasar (wato fasawa
karo ta biyu ke nan), za a
tarar da shi
fari sol, tare da ruwa a
ciki. Bahaushe na da kacici-kacicin da ke cewa, tafkina tsakiyar ɗaki, wato dai ruwan da ke cikin kwakwa. Ana
cin wannan nau’in kwakwa haka nan, kuma ana sarrafa ta domin a haɗa:
a. Kwakumeti
b. Lemon kwakwa
c. Biredi
d. Cakuleti da
sauransu
Lemon Zaƙi
Shi ma lemon zaƙi yana yin bishiya babba. ’Ya’yansa sukan kasance mulmulallu, wato a zagaye
tamkar ƙwallo. Suna da
launin kore kafin su nuna; bayan sun nuna launinsu yana
komawa ruwan ɗorawa. Bayan an ɓare ɓawon,
za a tarar da cikinsa
sala-sala, azara-azara. Ana shan lemon haka nan, sannan ana sarrafa shi domin samar da wasu
nau’o’in lemon sha kamar yadda aka bayyana a babukan da suka gabata.
Oro/Malu
Wannan nau’in ɗan bishiya ne, wadda ita ma bishiyar girma
take yi tare da rassa. Idan ɗan ya nuna, launin bayansa na kasancewa
ruwan madara. Yana da ƙamshi
sosai, kuma ɗanɗanonsa
na ɗauke da zaƙi-zaƙi da kuma tsami-tsami.
Kammalawa
Lallai Hausawa suna
da ’ya’yan itatuwa daban-daban, wasu daga cikin
su shukawa suke yi; yayin da wasu daga cikin su kuma tsirowa suke yi da kansu kamar dai yadda aka gani a sama. Bugu da ƙari, idan an
fahimci bayanan da ke sama, za a gano cewa, ko bayan ci ko shan waɗannan ’ya’yan itatuwa, ana amfani da su wurin sarrafa wasu
nau’o’in abinci ko abin sha daban-daban.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.