Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Salaf Suka Kasance Suna Shiri Domin Fuskantar Watan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ya salaf suka kasance suna shiri domin fuskantar watan Ramadan Mai Albarka. Menene koyarwarsu, da matafiyarsu akan hakan? Kuma ya shauqin su yake ga wañnan wata??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dabi'ar magabata Kamar yadda yake a rubuce a cikin littafai' Wanda aka ruwaito da sanadinsu daga amintattu: cewa lallai su sun kasance suna rokon Allah Mai girma da ɗaukaka da yakaisu wañnan wata (Ramadan) kafin isowarsa. Domin abunda suka sani dangane dashi na Alkhairi da daraja dake cikinsa. Sannan bayan shigar watan: suna rokon Allah ya taimake su akan ayyukan Alkhairi, bayan Kuma Ramadan ya fita suna rokon Allah ya karɓa musu ayyukan dasuka gabatar acikin wañnan wata. Kamar yadda Allah Mai girma yake fada

وَالَّذِينَ يُؤْتُونَ مَا آتَوْا وَقُلُوبُهُمْ وَجِلَةٌ أَنَّهُمْ إِلَىٰ رَبِّهِمْ رَاجِعُونَ

Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu. (Suratul Muminun 60)

أُولَٰئِكَ يُسَارِعُونَ فِي الْخَيْرَاتِ وَهُمْ لَهَا سَابِقُونَ

Waɗancan sunã gaggãwar tsere a cikin ayyukan alheri, alhãli kuwa sunã mãsu tserewa zuwa gare su (ayyukan alheri). (Suratul Muminun 61)

Sun kasance suna qoqari wurin yin aiki, bayan sunyi aikin Kuma sai su dinga tunani shin Allah ya amsa ayyukan su ko Bai Amsa ba! Wañnan Kuma Yana faruwa dasu ne sakamakon sanin girman Allah da sukayi. Da sanin Allah baya amsan wani aiki sai Wanda akayishi da (iklasi) Kuma akayi Shi yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yakoyar. (Mutaba'a) sun kasance basa tsarkake kansu, Kuma suna tsoron abunda zai ɓata musu ayyukan su. Samun Aikin su ya karɓu yafi damun su fiye da wahalan yin aikin, domin fadin Allah Mai girma

إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِن المُتَّقِيْنَ

Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne. (Suratul Ma'ida 27)

Sun kasance suna rage neman duniya, suna kashe lokutansu a masallatai, suna kiyaye azumin su basa cutar da kowa. Suna kiyaye lokutan su cikin karantu littafin Allah. Basa sake da lokacin su ya tafi a asara, Kamar yadda mutane suke awannan lokacin. Suna raya dararen su da salloli . Yinin su Kuma cike take da azumi, karatun Qur'ani, zikiri da sauran ayyukan Alkhairi. Ba su kasance suna barin wa lokaci daidai da minti ɗaya ko second ɗaya ba face sun gabatar da Aikin Alkhairi a cikin sa.

WALLAHU A’ALAM

               

Fatwa: Sheikh Salihul Fauzan.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments