Ticker

6/recent/ticker-posts

Bushara Da Zuwan Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah. Wane irin albishir Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yake yiwa alummarsa kafin watan Ramadan ya kama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam, Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya Kasance yana yiwa alummarsa bushara da zuwan Ramadan. Kamar yadda hadisi ya tabbbata daga Abu Huraira yace: naji Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa

إِذَا دَخَلَ رَمَضَان ُفُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّة ِوَغُلِّقَت ْأَبْوَابُ جَهَنَّم َوَسُلْسِلَت ْالشَّيَاطِينُ

Ma’ana: Idan watan Ramadan ya shigo ana buɗe qofofin rahama da qofofin aljanna,kuma ana rufe qofofin jahannama, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Bukhari suka ruwaito shi a lambata 3277 da Muslim a lamba ta 1079.

Haka kuma an ruwaito daga Anas Ibn Mālik yace (Watan) Ramadan ya shigo sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: Haqiqa wannan wata (na Ramadan) ya halarto muku, acikinsa akwai wani dare wanda yafi watanni dubu alheri. Duk wanda aka haramta masa (samun alherin da ke cikinsa) haqiqa an haramta masa alkhairi dukansa. Kuma babu wanda ake haramtawa alherinsa sai wanda bashi da rabo. Ibn Majah ya ruwaito shi kuma Albani yace hadisin hasan ne.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments