Gabatarwa
Fate, abinci ne mai sauƙi wanda ke ɗaya daga cikin nau’o’in abincin Hausawa.Ana hasashen an raɗa masa wannan suna ne saboda yin sa ruwa-ruwa da ake yi. Saboda idan an zuba shi a wuri zai iya malale ko’ina, ba ya tsayawa wuri guda saboda ruwan da ke cikinsa. Hausawa na da tatsuniyar kacici-kacici dangane da fate, inda suke cewa: “Kogina ya kai ya kawo sai ta gefe-gefe nake wanka.” Akwai waɗanda ba su ɗauki fate a matsayin abincin da za a ci a ƙoshi ba, sai dai a matsayin abincin sauya ɗanɗano kawai, ma’ana sauyi daga abincin da aka daɗe ana ci yau da kullum.
Kashe-Kashen Fate
Fate ya kasu kashi-kashi, duba da nau’o’in kayan haɗin da aka yi faten da su, ko kuma hanyoyin da aka bi
domin sarrafa su.
A ƙasa
an kawo jerin wasu daga cikin nau’o’in fate kamar yadda ake samun su a wurare
mabambanta a ƙasar Hausa:
Faten Dankalin Hausa
Kayan haɗin faten dankalin Hausa:
i. Albasa
ii. Dankali
iii. Gishiri
iv.
Kayan yaji
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Tafarnuwa
viii.
Tarugu
ix. Tattasai
x. Tumatur
xi.
Zogale
Za a fere dankalin na Hausa, sai a saka shi a cikin ruwa don kar ya bushe. Za a jajjaga tattasai
da attarugu da albasa da tumatur da tafarnuwa a saka a tukunya a soya da mai. Idan ya soyu za a zuba ruwa kaɗan a saka magi da kayan ƙanshi
a juye dankalin a ciki.
Bayan ya kusa dafuwa sai a watsa zogale da kifi a rufe. Idan ya dafu za a ɗauko muciya a saka ana daddagawa har sai ya haɗe ko’ina. Za a bar shi da ɗan ruwa-ruwa
domin ya fi daɗin ci.
Faten Kabewa
Kayan haɗin faten kabewa:
i. Alayyafu
ii. Gishiri
iii. Kabewa
iv.
Kayan miya
v. Mai
vi. Nama
vii. Ruwa
A tafasa nama da kayan ƙanshi, idan ya dafu a sauke a aje gefe
guda. Daga nan za a jajjaga tattasai da tumatur da albasa da tarugu a sa mai a tukunya a soya kayan su soyu. Sanan a zuba ruwa tare
da tafasasshen
nama da sauran ruwan nama, idan ya tafasa, sai a yanka kabewar kamar yadda ake yankan
dankali, a wanke a zuba a ciki. Idan kabewa ta nuna za a yanka alayyafu
a zuba a ciki,
za a rage wuta sosai har ya dafu da ɗan ruwa-ruwansa.
Tsokaci
Fate wani nau’i ne na abinci daga cikin nau’o’in abincin Hausawa mai mutuƙar muhimmanci. Wannan ya sa suka ɗauke shi ɗaya daga cikin abincin da ake yi musamman da rana. Baya ga wannan, abinci ne mai sauƙin aiwatarwa da bai cika ɗaukar lokaci ba yayin dafa shi ; sannan ya kasance abin marmari ga mutane da dama. Wannan ya nuna Hausawa suna da dabaru a ɓangaren sarrafa abincinsu na gargajiya har da na zamani.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.