Gabatarwa
Bayan ɗaukar fate a matsayin abinci da Bahaushe ya yi, yana kuma sarrafa shi cikin sigar da ake kira dafa-duka. Dafa-duka dai wata dabara ce daga cikin dabarun samar da abinci wanda ake haɗa dukkanin kayan haɗin abincin cikin sanwa guda yayin da aka zo dafawa. Kasancewar Bahaushe a kullum basirarsa da hikimominsa sukan ƙara haɓaka, yakan samu sauye-sauye da dama a ɓangarorin abincinsa na gargajiya da kuma na zamani. Wannan ya sa ci gaban zamani a ɓangagarorin abinci da abubuwan sha suka gaza yin nisan da za su yi wa tunanin Bahaushe ɓatan dabo.
Kashe-Kashen Dafa-Duka
Dafa-duka ta kasu
kashi-kashi kamar yadda sauran nau’o’in abinci suka karkasu. Kodayake, dafa-duka cimaka
ce da ta sha bamban da yadda ake yin ta a da da kuma yadda ake yin ta a yanzu. Wannan ya faru ne a sanadiyyar ci gaban zamani da kuma samun wasu dabaru da
hikimomi daga baƙin al’ummu. Ga
kashe-kashensu kamar haka:
Dafa-Dukan Shinkafa (Jollof
Din Shinkafa) Na Gargajiya
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan Yaji
iv. Mai
v. Ruwa
vi. Shinkafa
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Tumatur
A lokutan da suka shuɗe,
idan za a yi abinci nau’in dafa-duka,
akan niƙa tumatur da
tattasai da tarugu da albasa gaba ɗaya.
Daga nan, sai a
soya mai da
jajjagen tare da kayan yaji gaba ɗaya.
Idan ya soyu,
sai a yi sanwa a saka su tare da
gishiri. Idan sanwa ta tafasa za a ɗauko Shinkafa kowace iri (walau ta Hausa ko ta gwamnati). Haka za a bar ta kan wuta zuwa lokacin da ta dafu.
Dafa-Dukan Shinkafa da Wake (Jollof Din Shinkafa Da Wake) Na Gargajiya
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv.
Mai
v. Ruwa
vi. Shinkafa
vii. Barkono
viii. Wake
A ƙarƙashin 23.1.3 da ke babi na ashirin da uku, an yi bayanin
dafa-dukan shinkafa da wake a zamanance. Bambancin da ke tsakanin nau’o’in dafa-dukan gargajiya da ta zamani bai wuce na kayan
haɗi da yanayin sarrafawa ba. Kayan haɗin da ake amfani
da su a ta gargajiya ba su da yawa idan aka kwatanta su da ta zamani.
Dafa-Dukan Wake (Jollof Din Wake) Na Gargajiya
i. Kanwa
ii. Kayan yaji
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Tarugu da tattasai
vi. Wake
Ita ma wannan nau’in dafa-duka ana yin ta ne kamar yadda ake
yin sauran nau’o’in dafa-dukan da aka ambata a baya. Sau da dama akan tafasa waken tare da ‘yar
kanwa. Bayan ya tafasa, sai a zubar da ruwan sannan a ɗora sanwar dafa-dukan. Hikimar zubar da ruwan na farko ba ta wuce ta sabunta shi ba saboda baƙin da na farko kan yi a dalilin
sanya kanwar da aka yi.
Dafa-Dukan Dankalin Hausa
a. Dankali
b. Gishiri
c. Kayan miya
d.
Ruwa
Ana yin dafa-dukan dankali kamar yadda ake yin ta doya, wadda tuni aka yi
bayanin ta a baya a ƙarƙashin 9.1.5. Bambancin kawai shi ne, a nan ana sanya
dankali ne a maimakon doya.
Dafa-Dukan Taliya (Jollof Din Taliya) Na Gargajiya
Kasancewar taliyar gargajiya ta
bambanta da ta zamani, saboda ita taliyar gargajiya ana murza ta ne da wani
nau’in inji (injimi) da hannu. Bayan an kwaɓa garin
alkamar, akan mummurza ta da hannu domin a sanya a injin da yake samar da
siraran taliyar irin yadda ake buƙata. Daga nan sai a shanya ta
bushe. Da irin wannan nau’in taliyar ce ake dafa-dukan taliya a
gargajiyance. Kayan haɗin wannan nau’in dafa-duka ba
su da wani yawa, ba su wuce su:
i. Daddawa
ii. Kayan miya (idan an ga dama)
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Taliyar gargajiya
vi.
Yaji
Yadda ake dafa-dukan shinkafa
haka ake na taliya. Adadin ruwan da ake sanyawa a taliyar kaɗan ne idan aka kwatanta da wanda ake sanyawa a shinkafa. Dalili kuwa shi
ne, shinkafa ta fi shan ruwa da ɗaukar lokaci kafin dafuwa sama
da taliya.
Tsokaci
Dafa-duka cimaka (abinci) ce da ta tara abubuwa da yawa, kamar dai yadda
aka ga bayanin su
a sama. Daɗin daɗawa, akwai
wasu nau’o’in dafa-dukan
da za a iya samu a ƙasar Hausa bayan waɗannan da aka bayar, musamman idan aka yi
la’akari da yadda
kullum ake samun sababbin ilimomi ga al’umma a fannonin rayuwa
daban-daban, ciki har da yadda suke samar da abincinsu na yau-da-kullum.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.