A kowace al’umma abinci na taka muhimmiyar rawa ga kowane mutum idan har shi mai lafiya ne. Haka abin yake ga Hausawa, su ma suna tinƙaho da irin nasu abinci kamar yadda kowace al’umma ke tinƙaho da nata. Tuwo na daga cikin abincin Hausawa, da kusan ya kasance jagaba daga cikin nau’o’in abincin da ake da su a ƙasar Hausa. Tuwo a ƙasar Hausa Mahadi ne mai dogon zamani. Tun lokaci da Hausawa suka wayi gari suka sami kansu suke yin abinci nau’in tuwo. Kusan shi ne abinci babba a cikin abincin Hausawa na ci. Ga al’ada, idan baƙo ya ziyarci gidan Bahaushe, bayan ruwa da fura, tuwo shi ne abu na gaba da za a karrama baƙon da shi. Makaɗa Abdu Wazirin Ɗanduna ya fito da wannan al’ada a shahararriyar waƙarsa ta Sarkin Ƙaraye Abubakar inda yake cewa:
Jagora: A zamanin nan Sarki na da rai,
: Idan watan azumi ya kwan tara,
: Sai a aiko sarki na kira,
: Sai kwa in je Ƙaraye gurin Garba,
: In na je ya kai ni masaukina daban,
: Kuma masaukin yarana
daban,
: A masaukina an yi shirye-shirye,
: Ga tuwo mai nama in ji
Na’amadu,
: Ga ruwan sha in ji uban Bello,
: Ga fura mai nono in ji uban Daje,
: Ga ruwan sanyi Garba ya aje,
: Ga gasasshen nama ya ajiye,
: Ya ajiye yaji a waje ɗaya,
: Mu tashi cin nama mu baɗa mashi.
Yara/Gindi: Sarkin Ƙaraye Abubakar.
Hausawa sun haƙiƙance cewa, kashe-kashen tuwo ya ta’allaƙa ne da irin bambance-bambancen da
ake samu ta fuskar yadda ake samar da nau’o’in tuwon da ake da su. Akwai nau’in da ake yi mai tauri,
kamar yadda kuma akwai nau’in da ake mayar da shi ruwa-ruwa kafin ya zamo tuwo,
da dai sauransu. Hakan ya sa tuwo ya kasu kashi-kashi a wajen Hausawa ta fuskar
yadda ake sarrafa shi, da kuma abubuwan da ake haɗawa yayin
samar da tuwon. Wannan ɓangare na aikin na ɗauke da nau’o’in
tuwon da ake samu a ƙasar Hausa, tare da
bayanin yadda ake sarrafa kowannensu.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.