Ticker

6/recent/ticker-posts

'Ya'yan Itatuwa Da Sauwowin Da Hausawa Ke Amfani Da Su a Matsayin Abinci

Gabatarwa

Bahaushe  ya ɗ auki ’ya’yan itatuwa  a matsayin abinci kamar yadda ya ɗ auki ganyaye da sauran nau’o’in abinci . Yana sarrafa su domin samar da wasu daga cikin abincinsa ko abin sha kamar dai yadda aka bayyana a sama, musamman a babin da ya yi magana game da nau’o’in lemo. To ko bayan wannan  ma, akwai ’ya’yan itatuwan da ake cin su haka nan. Wannan ne nau’in abincin tsinki ka ci. Wato dai da zarar an tsinki ɗ an itace, sai batun ci.

A ɓ agare guda kuma, akwai nau’in abinci da ya shafi saiwa. Wato jijiyoyi ne na wasu tsirrai wa ɗ anda ake amfani da su a matsayin abinci. Duk da cewa mafi yawa dafa su ake yi, akwai ’yan ka ɗ an da ake iya ci haka nan ba tare da an dafa ba. Wannan babi zai mayar da hankali wurin kawo ire-iren saiwoyi da ’ya’yan itatuwan da Bahaushe  ke amfani da su.

Aduwa

Aduwa bishiya ce babba mai ƙ aya wadda kuma ƙ ayarta ta fi ta magarya da kurna ƙ arfi da girma. Haka ma ’ya’yan aduwa  sun fi na magarya da kurna girma. ’Ya’yan ta k oraye (korra) ne idan suna ɗ anye. Idan sun nuna kuwa, sai su koma ruwan ɗ orawa. Ana ɓ are ɓ awon kafin a sha. Sanna n kuma a cikin sa akwai ƙ wallo.

Aya

Aya ma cikin ƙ asa take zuba ’ya’yanta , tana da y a’ya ƙ anana sannan l auninsu ya kasance ruwan ƙ asa. Ana iya cin aya haka ɗ anyarta ba tare da an soya ba . Ana kuma iya shanya ta ta bushe sannan a mata suyar sikari ko na gishiri. Yayin suyar, za a ɗ an sanya mata ruwa tare da gishiri ko sikari. Daga nan sai a saka cikin tukunya , a yi ta juyawa bisa wuta . Sannan akwai ɗ aya daga cikin nau’in aya da ake ji ƙ awa a ruwa. Za ta kumbura ta yi taushi sanan launinta zai kasance ruwan madara-madara. Ɗ an ɗ anonta kuwa na kasancewa nono-nono.

Bado

Bado  nau’in tsiro ne da ke fitowa kuma yake rayuwa a cikin ruwa. Ba shuka shi ake yi ba , y ana fitowa ne da kansa cikin rafuka da tafki da ma ƙ ananan gulabe. Ganyensa yana kasancewa ne saman ruwa. Shi kuwa ɗ an badon yana zama a ƙ asan ruwan. Da farko bado yana y in fure fari mai kyau. Yayin da furen ya rufe sannan ya lan ƙ washe ya koma cikin ruwa, wannan  na nuna ɗ an ba ɗ on ya nuna kenan.

Ɗ an ba ɗ o na da koren launi daga baya. Idan an ɓ are shi, yana kasancewa sala-sala kamar na lem o; yana ɗ auke da ’ya’ya masu kama da maiwa  ko gero  ko dawa . Saboda haka ne ma ake cewa, akwai nau’o’in bado kamar haka:

a. Badon maiwa

b. Badon gero

c. Badon dawa

Ana iya cin wannan  bado haka nan. Sai dai ya fi da ɗ i idan aka kwa ɗ a shi da mai da yaji. Wani lokaci kuma akan sanya ƙ uli.

Dabino

Dibino bishiya ce mai tsawo sosai (duk da akan samu masu ƙ arancin tsawo, musamman a zamanin yau). Takan yi ’ya’ya a can sama. Shi ma yakan yi nono-nono, wanda jikin kowane nono guda akan samu ’ya’ya da dama. Idan dabino ya ƙ osa, akan hau a rufe shi domin ya nuna sosai a sama. Ana yin haka ne ta hanyar lullu ɓ e kowane nono da buhu ko algarara. Hakan zai kasance tamkar nukawa aka yi, kuma an kare shi daga fitinar tsuntsaye ko jifa n yara.

Bayan dabino ya nuna, za a iya cin sa yana ɗ anye- ɗ anye (a nan ba ana nufin ɗ anyen nuna ba). Ana kuma iya ajiye shi ya bushe sosai, inda launinsa ke komawa ruwan ƙ asa (ko ya bushe ba safa i yake yin tauri ba). A cikin dabino akwai ɗ a wanda ake kira ƙ wallon dabino. Shi ma ana sanya shi cikin wasu nau’o’in lemo.

Dankali

Wannan na ɗ aya daga cikin abincin Bahaushe  da ke cikin rukunin saiwoyi. Akwai nau’in dankali guda biyu, wato dankalin Hausa  da kuma dankalin Turawa. Bahaushe ya fi amfani da dankalin Hausa (wanda ana kuma kiran sa da suna kudaku). Wannan ya faru ne sakamakon ƙ asar Hausa ta fi kar ɓ ar tsir o n dankalin Hausa sama da na dankalin Turawa. Akan ci dankalin Hausa haka nan ba tare da an dafa ba (amma ba domin yunwa  ba, sai dai a ci ka ɗ an kawai).

An fi samun dankali a lokacin sanyi ; kuma a wannan  lokaci ne ya fi yawaita a kasuwannin ƙ asar Hausa . A siffa kuwa, dankali fari ne, kodayake yana sirkawa da launin ruwan ƙ asa- ƙ asa . Dankalin Hausa nau’i ne na saiwa da ake dafawa ko soyawa. Akan fere  dankali kafin a soya. Idan kuma dafawa za a yi, ana iya sanya shi haka nan ba tare da an fere ba. Bayan ya da f u , za a yi amfani da cokali ko wu ƙ a wurin ɗ ebe bayansa. Sannan ana iya yin amfani da shi wurin ha ɗ a wasu nau’o’in abincin Bahaushe  kamar dai yadda aka yi bayanin wasu daga cikinsu a sama. Bayanan nan, ana iya cin dafaffen dankali da yajin ƙ arago.

Ɗinya

Ɗ inya  ma babbar bishiya ce mai rassa. Tana kama da bishiyar kanya. Da ɗ in da ɗ awa, ’ya’yanta na kama da na kanya. ’Ya’yan ɗ inya korra ne kafin su nuna. Idan sun nuna kuwa suna komawa ba ƙ a ƙ e , s annan jikinsu kan yi laushi. A ciki n kowacce kuwa akwai ƙ wallo da ake samu . Ana tsotsar ɗ inya r ne sannan a jefar da ƙ wallon na ciki.

Ɗorawa

Ɗ orawa  ma bishiya ce babba da ke da rassa. Ta so ta yi kama da tsamiya , amma ’ya’yanta sun fi na tsamiya kauri da tsayi. ’Ya’yan na kasancewa nono-nono. A kowane jikin nono akwai zangarniy un ɗ orawa da dama. A cikin kowace zangarniya kuwa akwai ’ya’ya da yawa. Bayanta yana da launi ruwan ƙ asa ,  sannan c ikin ta ku m a yake da launin ruwan ɗ orawa. Daga launinta ne ma ake kwatancen ruwan ɗ orawa. Akwai kacici-kacicin Bahaushe  da ke cewa daga nesa na hango layun ƙ awata, wato dai ɗ orawa.

Durumi

Durumi  bishiya ce babba mai tsawo da fa ɗ i mai ɗ auke da rassa. Tana ’ya’ya da suka ɗ an ɗ ara na magarya girma , s ai dai ba su da ƙ wallo a ciki nsu kuma suna da koren launi. A ciki n ‘ya’yansa akwai wani ɗ an gashi-gashi , ɗ an ɗ anonsa kuwa ya na da ɗ an bauri-bauri. Akwai wa ɗ anda ke cin sa a matsayin goro, musamman mata da ke da ciki. Yara sun fi cin irin wannan  nau’in ɗ an ’ya’yan itace.

Gawasa

Wannan ma bishiya ce da ke girma tare da rassa. Girman ’ya’yan ya kai kwatankwacin na makani. Idan ta nuna , launin bayanta ruwan ƙ asa n e , sannan a na fere  ta kafin a ci. Launin cikinta kuwa ruwan madara ne. Tana da ƙ wallo a cikinta , ku ma wannan   ƙ wallon nata ana fasa shi sannan a ci abin da ke ciki.

Giginya

Giginya  doguwar bishiya ce wa d da ta kai dabino tsayi, sannan takan iya fin ta a kauri. Tana yin ’ya’ya ne a can sama tamkar na goruba , s ai dai ita ’ya’yanta manya ne sosai. Idan suka nuna, suna da launin ruwan ɗ orawa. Bayan giginya fata ce ba ƙ o ƙ o ba , s annan a cikinta akwai ƙ wallo ko ƙ wallaye. A wani lokaci a kan samu mai ƙ wallo ɗ aya ko biyu ko uku, har ma sama da haka .

Gwanda

Gwanda  ma bishiya ce wadda ba ta yin rassa sai dai tsawo kawai. Sannan takan yi ’ya’yanta a can tsololuwa, wato ƙ arshenta. Wannan ne ma ya sa Bahaushe  ke da kacici-kacici da ke cewa: ’Yan matan gidanmu masu nonuwa a tsakar ka, wato dai gwanda.Bayan gwanda kore ne kafin ta nuna. Bayan ta nuna kuwa, yana kasancewa ruwan ɗ orawa. A ciki kuwa akwai ƙ ananan ’ya’ya ba ƙ a ƙ e. Ana ɓ are gwanda a sha ta haka nan , s annan ana iya sarrafa ta cikin wasu nau’o’in lemo.

Goruba

Goruba  bishaya ce mai siffar giginya , s ai dai ba ta kai giginya girma da tsawo ba. ’Ya’yanta kuwa masu tauri ne, musamman idan sun nuna. Launin bayansu ruwan ƙ asa ne. Sannan a ciki akwai ƙ wallo mai tauri. Wani lokaci yara na fasa wannan   ƙ wallo domin su ci abin ciki, wanda shi ma sai an ji ƙ a sosai yake yin laushi. Idan tana ɗ aya kuwa, ana iya ciro ta domin a ci abin cikin da ake kira ɓ oto ko kwalshi.

Gyaɗa

Bahaushe  na da kirarin gya ɗ a  wato gya ɗ a mai sihiri, a ɓ are a ga biyu, a murje a ga hu ɗ u, a tauna a ji gar ɗ i; ba don ki yi yawa ba , da sai ɗ an wane da wane, sai ɗ an sarki . Gya ɗ a  a ƙ asa take ’ya’yanta. ‘Ya’yanta ƙ anana ne da suke kasancewa cikin kwalfa/ ɓ awo. Wannan ɓ awo nasu na da launin ruwan madara. A ciki ne kuma ake samun ’ya’ya masu launin ja ko fari (wato gya ɗ a mai bargo). Wata k w alfar na zuwa da ɗ a ɗ aya, wata biyu, har ma akan samu uku ko hu ɗ u.

Gya ɗ a  ba abinci ne da za a ci domin a ƙ oshi ba. Sai dai ana yin amfani da ita yayin samar da nau’o’in abinci daban-daban. Wannan ya ha ɗ a da nau’o’in miya  da sauransu. Ana iya cin gya ɗ a  haka nan ba tare da an dafa ba. Hanyoyin sarrafa gya ɗ a sun ha ɗ a da:

a. Dafawa a cikin kwalfa/ ɓ awonta

b. Soyawa a cikin kwalfa/ ɓ awonta (ta-soyu)

c. Soyawa bayan an ɓ are (mandawa/amaro)

d. Gasawa

e. Da gya ɗ a ake yin mangya ɗ a

f. Da gya ɗ a ake yin ƙ uli/ ƙ arago

g. Ana miyar gya ɗ a

h. Ana sanya gya ɗ a a cikin miya

i. Ana sarrafa ta domin yin kayan ƙ walama kamar su ƙ am- ƙ am, baba-dogo, da sauransu.

Jinɓiri (Ɗanye Wake )

Wake  tsiro ne da yake ya ɗ o ( kodayake akan samu wake n da ba ya ya ɗ o. A maimakon haka, yana ɗ an tsawo ne ka ɗ an). Yana yin ’ya’ya da suke kasancewa a jere jikin ɓ awonsu. ’Ya’yan da ake samu cikin ɓ awo guda na da yawa. Jim ɓ irin wake  shi ne irin waken da aka ciro wa ɗ anye shataf, wato ba tare da ya fara ƙ o ƙ arin bushewa ba, sannan kuma ba tare da ’ya’yan ciki sun yi ƙ wari sosai ba. Irin wannan  wake ana dafa shi a ci. Irinsa ne da aka tambayi kare me aka dafa a gidanku? Sai ya ce: Na ga dai ana sunsunawa ana jefarwa. Wato dai bayan an dafa, to ana cinye ’ya’yan cikin a jefar da ɓ awon.

Kaɗe

Ka ɗ e  ma bishiya ce da ke da rassa , sannan y a’yan na da launin kore kafin su nuna. Bayan su ya na komawa kore-kore amma ba kore sosai ba. A cikinsu akwai ƙ wallo da ke da sul ɓ i tamkar leda. Wannan ɗ an na da launin ruwan ƙ asa.

Kankana

Kankana  nau’in tsiro ne mai ya ɗ o kamar tumatur, sai dai ganyenta da karanta da ’ya’yanta duk sun fi tumatur girma nesa ba kusa ba. ’Ya’yan kankana sun kasance masu girma sosai , kuma l auninsu kore ne tun kafin su nuna har ma bayan sun nuna. A jikin su akwai ratsin tsagen ruwan madara-madara. Cikinta kuwa ja ne jaw ur, tare da ƙ ananan ’ya’ya masu launin ba ƙ i-ba ƙ i ko ruwan ƙ asa- ƙ asa. Akan samu cikin kankana ya kasance ruwan madara musamman idan ba ta yi nunan da ya kamata ba, ko kuma ƙ asar wurin da aka shuka ta ba ta da kyau sosai. Ana shan kankana, tun daga kan ɓ awon ta har cikin ta da ma ’ya’yan ciki. Sannan ana ha ɗ a launukan lemo daban-daban da ita.

Kanya /Kaiwa

Kanya  babbar bishya ce da ke da matu ƙ ar kama da ɗ inya. Hatta ’ya’yanta irin na ɗ inya ne, sai dai su ba masu taushi ne sosai irin na ɗ inya ba . Launinsu kore ne idan suna ɗ anyu. Idan sun nuna kuwa, launinsu na komawa ruwan ɗ orawa. Suna da hula ta sama nsu . Akwai ’ya’ya a cikinta da adadinsa na iya kai hu ɗ u ko sama da haka. Yara sun fi shan irin wannan  ’ya’yan bishiya.

Karas

Karas  ma nau’in tsiro ne da ke ɗ iya a ƙ ar ƙ ashin ƙ asa. Ganyensa na kasancewa ɗ an ka ɗ an a sama , kuma yana da launi ja . Shi ma haka ake ci ba tare da an dafa ba. Sai dai akan sarrafa shi cikin wasu nau’o’in abinci kamar dafa - duka ko miya  ko wasu nau’o’in lemo.

Kurna

Kurna  na da matu ƙ ar kama da magarya. Sai dai ta fi magarya a komai, tun daga kan girman bishiyar kanta har ya zuwa girman ’ya’yan. Hausawa  na da karin maganar da ke cewa: Ko da gani ko da girgiza kurna ta fi magarya.

Kwaruru/Gujiya /Maiƙoƙo

Mai ƙ o ƙ o na da kama da gya ɗ a . Shi ma ’ya’yansa cikin ƙ asa suke, sannan cikin ƙ walfa/ ɓ awo. Ita ma ana bin hanyoyi daban-daban domin sarrafa ta. Daga cikinsu akwai:

a. Ana dafa ta tare da kwalfarta, wanda ita ake kira kwaruru

b. Akan ɓ are ta a ɗ anyarta sannan a dafa, wanda ita ake kira lubbatu

c. Ana iya ɓ are ta a shanya ta bushe, sannan a soya [1] , wannan  ita ake kira ƙ waras- ƙ waras. [2]

Ƙwame/’Ya’yan Kuka

Daga bishiyar kuka  ake samun ƙ wame. Ɗ iyan da kuka ke yi shi ake kira da wannan  suna. Ana iya barinsa ya bushe kafin a cira , w ani lokaci ku m a akan cire shi tun bai bushe ba. Bayansa kore ne kafin ya bushe. Idan ya bushe kuwa yana zama ruwan ƙ asa. Sannan akwai gashi-gashi a bayan. Idan aka fasa shi, akwai zare-zare da gari  a ciki, fari sol ko ruwan madara. Sannan akwai ’ya’ya a jejjere cikin wannan gari. Ana shan ƙ wame haka nan, sannan ana ha ɗ a wasu nau’o’in abinci da shi. Daga ciki har da kayan ƙ walama irin su garin bu ɗ us da gudi.

Lemon Tsami

Lemon tsami  na da matu ƙ ar kama da lemon za ƙ i a siffa. Sai dai shi ƙ arami ne, bai kai girman na za ƙ i ba. Sannan bishiyarsa na da ƙ aya. Ba a faye shan lemon tsami haka nan ba. An fi sarrafa shi cikin wasu nau’o’in abinci, musamman lemon sha.

Magarya

Magarya  ma bishiya ce, wadda idan an bar ta za ta iya ɗ an yin tsawo. Tana da rassa sannan tana da ƙ aya. ’Ya’yanta ƙ anana ne, sai dai ba su kai na kurna ba. Kafin ta nuna, bayanta kore ne shar. Idan ta nuna kuwa, tana komawa ruwan madara ko ruwan ƙ asa. Ana cin bayan ne sai kuma a bar ƙ wallonta da ke ciki. Shi ma wannan   ƙ wallo ana iya daka shi a sanya sikari sannan a samar da ƙ walama da shi.

Makani/Gwaza

Makani ko gwaza na daga cikin jerin abincin Bahaushe   ƙ ar ƙ ashin saiwoyi. Itacensa ba ya tsawo. Girmansa na iya zama ɗ aya da na dankalin Hausa , s ai dai an fi samun ƙ anana a cikinta fiye da dankali . Bayan t a na da launi n ba ƙ i tare da layi-layi mai launin jaja-jaja. Ana dafa ta ne da ɓ awon t a. Bayan t a dafu , ana amfani da cokali ko wu ƙ a ko ma a sanya hanu wurin ɓ are ɓ awon. Cikinta yana da launin ruwan foda Sannan yakan kasance mai yau ƙ i-yau ƙ i. Bayan an dafa gwaza akan iya daka ta kamar sakwara. Ana iya yin miya  a ci da gwaza.

Mangoro

Bishiryar mangoro na girma sosai , kuma takan yi fa ɗ i da tsayi tare da rassa. ’Ya’yan mangoro na da launin kore kafin su nuna. Bayan sun nuna kuwa, suna komawa runwan ɗ orawa, ko ja a wani lokaci , kuma s una da ƙ wallo a tsakiya. Mangoro  na daga cikin ’ya’yan itatuwan da ake sha da zarar an cira. Wato dai ba sai an dafa ba.

Nunu

Nunu  bishiya ce da ke girma tare da rassa , l aunin ɗ an ruwan ɗ orawa ne idan ya nuna . Haka ku ma cikinsa launin ruwan ɗ orawa ne , sannan a cikinsa akwai ƙ wallo.

Rake

Rake kara ne mai kama da na dawa , s ai dai yana da launin ba ƙ i ko kuma kore-kore. An fi shukawa a fa d ama ko wuri mai tara ruwa sosai. Yakan yi shekara guda da dasawa kafin ya kai lokacin da za a more shi. Yayin da aka ɓ are ɓ awon rake, za a tarar da cikin fari ne mai tattare da ruwa mai za ƙ i. Ana shan rake haka nan, kuma ana iya sarrafa shi cikin wasu nau’o’in lemo. Da rake ne kuma ake samar da sikari.

Rogo

Rogo  ma ɗ aya ne daga cikin nau’in abinci dangin saiwa. Yana da tsawo ba kamar dankali ba , ɓ awonsa ruwan ƙ asa ne. Amma idan aka ɓ are, cikinsa fari ne tas. Tsakiyarsa akwai zare-zare. Yana daga cikin abincin da ake shukawa a ƙ asar Hausa . Ana iya dafa shi a ci da yajin ƙ arago. Sannan ana iya sarrafa wasu nau’o’in abinci na daban da shi. [3] Wani lokaci ma ana iya gasa shi a ci.

Tanzarin

Wannan ma wani nau’in lemo ne . Ya fi lemon tsami  girma , amma bai kai lemon za ƙ i ba. Sannan wannan  nau’in lemo na da za ƙ i sama da lemon za ƙ i. Ana shan sa haka nan ko kuma a sarrafa shi domin samar da lemon sha.

Taura

Taura ma babbar bishiya ce mai rassa. ’Ya’yanta korra ne kafin su nuna. Idan kuwa suka nuna , s u na komawa ruwan ƙ asa - ƙ asa . Idan an ɓ are wannan   ɓ awo n , za a tarar da cikinta kore ne a kodayaushe. Sannan cikinsa akwai ƙ wallo. Ga al’ada,y ara sun fi cin taura.

Tsamiyar Biri (Tuwon  Biri)

Ita ma tsamiyar biri bishiya ce da ke da ’ya’ya. ’Ya’yan sun kasance kamar tsamiya , sai dai girmansu bai kai na tsamiya ba. Idan aka ɓ are, ’ya’yan ciki suna da launin ruwan ɗ orawa , sannan s una da za ƙ i da ɗ an tsami -tsami ka ɗ an.

Kammalawa

Lallai Hausawa  na da ’ya’yan itatuwa  daban-daban wa ɗ anda suka ha ɗ a da wa ɗ anda ake shukawa da ma wa ɗ anda suke tsirowa da kansu kamar dai yadda aka gani a sama. Sannan daga bayanan da ke sama, za a fahimci cewa, ko bayan ci ko shan ’ya’yan itatuwa da ake yi, ana amfani da su wurin sarrafa wasu nau’o’in abinci ko abin sha daban- daban.[1] Wannan suya ba da mai ake yi ba. Ana sanya ta ne kawai cikin tukunya  a yi ta juyawa har sai ta tsattsage.

[2] An samu wannan  suna ne daga irin sautin da ke fita yayin da ake cin wannan nau’in abinci.

[3] Da rogo  ne ake yin garin kwaki. Sannan ana iya busar da shi ya zama alabo ; w anda kuma da alabon ana iya yin nau’o’in abinci da dama.

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments