Ɗan Bagalaje
Kayan haɗin ɗanbagalaje:
i. Alabo
ii. Albasa
iii. Attarugu
iv. Gishiri
v. Manja
vi. Ruwa
vii. Tattasai
Za a daka alabo ya yi laushi sannan a tankaɗe. Daga nan za a sanya ruwa a kwaɓa. A ciki za a yanka albasa da tattasai da attarugu sannan a sanya gishiri. A gefe guda kuma, za a aza kasko bisa wuta sannan a sanya manja. Za a riƙa zuba wannan kwaɓaɓɓen garin alabo sannu a hankali ana soyawa tamkar yadda ake suyar ƙosai. Ana cin ɗan bagalaje ne da yaji.
‘Yar Tsame
Kayan haɗin ‘yartsame:
i. Albasa
ii. Gero
iii. Kanwa
iv. Mai
v. Ruwa
Hanyar sarrafa
‘yar tsame daidai take da ta masar gero da aka yi bayani a ƙarƙashin 13.1 da ke baya. Bambancin kawai shi ne, ana soya
masar gero ne a cikin tanda. Ita kuwa ‘yar tsame ana soya ta ne a cikin kasko
tamkar ƙosai. Yawanci ‘yar
tsame ba ta kai masa girma ba. Wannan ke ba ta dama ta soyu sosai a cikin mai
fiye da masar geron.
Ƙwalan
Kayan haɗin ƙwalan:
i. Alabo
ii. Albasa
iii. Attarugu
iv. Gishiri
v. Manja ko man gyaɗa
vi. Ruwa
vii. Tattasai
Yadda ake ƙwalan yana da matuƙar kama da yadda ake ɗan bagalaje (kamar yadda aka yi bayani a sama ƙarƙashin 13.1.4). Bambancin kawai shi ne, ana kwaɓa ƙullun ƙwalan ne ruwa-ruba ba kamar na ɗan bagalaje ba. Bayan haka, ana soya shi ne a tanda ko ƙaramin kasko tamkar yadda ake soya masa. Za a riƙa ɗiga mai kaɗan sannan a zuba ƙullun ɗan kaɗan. Yayin da ɓangare guda ya soyu, sai a juya zuwa ɗaya ɓangaren. Za a riƙa yi ana ɗiga mai kaɗan-ƙaɗan har ya yi yadda ake so. Ana cin ƙwalan da yajin borkono.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.