Ticker

6/recent/ticker-posts

Farfesun Nama, Tsiren Nama, Soyayyen Nama, Gasasassen Nama Da Sauran Hanyoyin Sarrafa Nama Da Kifi

Gabatarwa

Allah  ya halicci dabbobi  da tsuntsaye iri-iri , Ya kuma huwace wa ɗ an Adam wa ɗ annan dabbobi da tsuntsaye a matsayin wani nau’i na abinci da kuma ƙ arin ni’ima a gare su . Sai dai addinin Musulunci ( addinin da mafi rinjayen Hausawa  ke bin koyarwarsa ) ya han a su cin nama n was u daga cikin wa ɗ annan halittu na dabbobi . Akwai hanyoyi daban-daban da Hausawa ke bi domin sarrafa nama. Wannan ya ha ɗ a da dafawa ko soyawa ko gasawa da dai makamantansu. Baya ga haka, nau’in kayan ha ɗ i n da ake sa wa nama yayin sarrafa shi na iya kasance wa wani abin la’akari idan ana son bayyana bambancin ire-iren nama n da ake da su a ƙ asar Hausa . Bugu da ƙ ari, a duk lokacin da ake maganar ire-iren nama n da Bahaushe   ya ke ta’ammuli da su, dole ne a tuna da nau’o’in halittun dabbobin da ake samun naman daga gare su. Wannan babi ya karkata akalarsa ne kan tattauna ir e-iren wa ɗ annan batu tuwa .

Farfesun Nama

i. Albasa         

ii. Attarugu                 

iii. Daddawa             

iv. Gishiri

v. Kanimfari   

vi. Kayan yaji             

vii. Man gya ɗ a            

viii. Nama

ix. Ruwa        

x. Tattasai

Yayin samar da farfesun nama, za a wanke  nama n sosai a sanya shi cikin tukunya r da aka zuba ɗ an ruwa daidai gwargwado a cikinta a matsayin ruwan sanwa . Sannan za a sanya gishiri da albasa   a ciki. Za a bar shi (naman) ya tafasa sosai har sai ya fara taushi. Daga nan sai a sanya kayan yaji ciki tare da jajjagen tarugu da tattasai da kuma daddawa. Yayin da naman ya dafu, za a ga ya rabu da ƙ ashi.

Soyayyen Nama

i. Albasa          

ii. Barkono      

iii. Gishiri        

iv. Kayan yaji

v. Mai              

vi. Nama         

vii. Ruwa

A duk lokacin da ake bu ƙ atar samar da soyayyen nama, za a tafasa naman bayan an wanke  shi . Yayin tafasawar , za a sanya gishiri tare da albasa , amma ba a sanya ruwa da yawa , ana so a sanya ruwan daidai gwargado yadda naman zai iya s h anyewa. Bayan an tafasa shi, sai a soya shi sama-sama. Daga nan za a sanya mangya ɗ a cikin tukunya  ko abin suya. Za a ri ƙ a sanya naman ciki ana soyawa. Bayan ya soy u , sai a tanadi yaji domin ci.

Tsiren Nama

i. Albasa          

ii. Barkono      

iii. Gishiri       

iv. Kayan Yaji

v. Ƙ uli              

vi. Nama         

vii. Ruwa

Duk da a zamanance akan yi tsire cikin gidaje domin amfanin mutanen gida, a da an fi yin tsire domin sayarwa. A bisa haka, an fi samun tsire wurin mahauta (rundawa) . An a sayar da tsire ne a kusa da tukuba, inda nan ne ake gasa tsire. [1]

Dangane da ya d da ake samar da tsire kuwa, za a wanke  nama n sannan a yayyanka shi lafe-lafe. Daga nan za a sossoka shi jikin tsinken tsire. A gefe guda kuwa, za a tanadi ƙ uli- ƙ uli wanda aka daka tare da kayan yaji. Za a turbu ɗ a wannan  nama n da aka sossoke a cikin garin ƙ ulin yadda duk zai baibaiye jikinsa. Za a hura wuta  a kan tukuba , daga nan kuma a sossoka tsinkayen tsiren su gewaye wutar (su yi wa wutar da’ira/kuri) . Haka za a bar su, zafin wutar ya ri ƙ a gasa naman. Za kuma a ri ƙ a yi ana juyawa.

Gasasshen  Nama

i. Gishiri          

ii. Kayan yaji              

iii. Mai

iv. Nama         

v. Ruwa                      

vi. Tafarnuwa

Wannan dabara ta na ɗ aya daga cikin hanyoyin sarrafa nama mafi sau ƙ i. Ba a bu ƙ atar tafasa nama kafin fara gasawa. Da zarar an gyara nama n an wanke  shi , s a i a ɗ ora shi bisa wani ƙ arfe mai raga-raga [2] sannan a ɗ ora bisa wuta , amma ana barin wutar daidai yadda zafin ta zai ri ƙ a bugan naman da aka ɗ ora a bisanta . Yayin da ake gasa shi, za a iya yayyafa masa mai, musamman idan naman ba mai kitse sosai ba ne. Daga nan sai a sanya masa kayan yaji a bisansa idan ya fara nuna .

Farfesun Kayan Ciki

i. Albasa                      

ii. Barkono                 

iii. Gishiri       

iv. Daddawa               

v. Kayan ciki               

vi. Kayan yaji

vii. Mai                       

viii. Ruwa                   

ix. Tattasai da tarugu

Za a wanke  nama sannan a tafasa shi tare da albasa  da kayan yaji da kuma gishiri. Bayan ya tafasa, idan akwai sauran ruwa a cikin tukunyar akan zubar da shi. A gefe guda ku m a , za a yi jajjagen tarugu da tattasai da albasa. Abu na gaba kuma , sai a yi sanwa da ɗ an ruwa ka ɗ an ba mai yawa ba. Bayan ruwa n ya tafasa, sai a sanya wannan  jajjage da nama ciki. Haka za a bar su su ƙ arasa nuna tare.

Farfesun Kai

i. Albasa                      

ii. Gishiri         

iii. Kai             

iv. Daddawa

v. Kayan ƙ amshi        

vi. Mai             

vii. Ruwa        

viii. Tarugu

ix. Tattasai                  

x. Tumatur

Za a wanke  kai tsaf (walau na akuya, rago, tunkiya, ko kuma na sa), sannan a sanya a tukunya  tare da ruwa da gishiri da albasa  da daddawa. Za a bar shi ya ɗ auki lokaci sosai har sai ya fara saki. A gefe guda kuwa za a jajjaga tumatur da tarugu da albasa da tattasai. Za a iya soya su sama-sama [3] ko kuma a sanya su haka nan. Sannan ba a so su yi yawa sosai. Za a zuba su cikin tukunyar tare da kayan ƙ amshi. Yadda ake farfesu, haka ake na kai da kuma na bindins a (wutsiya/jelarsa).

Kilishi

i. Barkono       

ii. Gishiri         

iii. Kayan yaji            

 iv. Mai

v. Nama          

vi. Ƙ uli- ƙ uli     

vii. Ruwa

Za a gyara nama lafe-lafe a zuba masa gishiri wanda aka kwa ɓ a da ruwa , sannan s ai a shanya shi. A gefe guda kuma , za a kwa ɓ a ƙ uli- ƙ uli da yaji , sai a barba ɗ a  su kan naman da aka shanya ya d da za su bushe tare. Idan a na bu ƙ ata za a iya yanka albasa . Bayan ya bushe, sai a kunna wuta  sannan a aza shi a sama nta, z a a ri ƙ a yi ana jujjuyawa. Da zarar ya gasu, kilishi ya samu ke nan.

Farfesun Kaza

i. Albasa         

 ii. Gishiri         

iii. Daddawa   

iv. Kayan yaji

v. Kaza           

vi. Mai             

vii. Ruwa       

 viii. Tarugu

ix. Tattasai      

x. Tumatur

Ya d da ake farfesun sauran nau’o’in nama, haka ake yin na kaza. Bambancin kawai shi ne, ana amfani da naman kaza ne a maimakon naman rago ko na sa da makamantansu.

Soyayy iyar Tattabara

i. Albasa          

ii. Barkono (tonka)    

 iii. Gishir         

iv. Kayan yaji

v. Magi            

vi. Mai                         

vii. Ruwa        

viii. Tattabara

Yadda ake suya r tattabara ya na kama da na sauran suya da aka yi bayani a sama. Bambancin kawai shi ne, ita tattabara ba a tafasa namanta kafin a soya. Hakan kuwa na faruwa ne a sakamakon taushi da namanta ke da shi.

Farfesun Kifi

i. Albasa         

 ii. Daddawa    

iii. Kayan Yaji            

 iv. Kayan miya

v. Kifi              

vi. Mai             

vii. Ruwa

Za a yi amfani da lemon tsami  ko ɗ o ɗ ɗ oya domin a wanke  kifi n , sai a bar shi ya tsane. A gefe guda kuwa, za a jajjaga tattasai da tarugu da albasa  a soya sama-sama (za a iya amfani da su ba tare da an soya ba). Bayan wannan  ya samu, sai a tanadi kayan yaji.

Yayin da mai farfesun kifi ya tabbatar da kammaluwar abubuwan da aka bayyana a sama, abu na gaba da zai tunkara shi ne , ɗ ora sanwa amma da ruwa ka ɗ an, daidai adadin kifin da ake da shi. Bayan ruwa n ya tafasa, sai y a sanya wannan   kifi a ciki . Da zarar ya fara jin wuta , sai y a saka jajjagen da aka tanada da gishiri da kuma daddawa.

Kammalawa

Ha ƙ i ƙ a , Ubangiji ya wadata ɗ an Adam da nau’o’in nama iri-iri. Wannan babin ya kawo wasu nau’o’in dabarun sarrafa nama ne gwargwado daga cikin wa ɗ anda ake da su. Sai dai za a iya ha sa shen cewa, hanyoyin sarrafa nama a ƙ asar Hausa  ba su wuce wa ɗ anda aka bayyana a sama ba. Sai dai akan iya samu n wasu ‘yan bambance-bambancen da ba su taka-kara sun karya ba.



[1] Sa’id, (2006: 441) ya ba da ma’anar kalmar tukuba da cewa: “tarin ƙ asa da aka gyara don gasa tsire a kai.”

[2] Ƙ arfe n e na musamman da ake amfani da shi yayin gasa nama ana kiran sa da suna zarga.

[3] Za a iya sanya ‘yar kanwa ka ɗ an kafin a soya kayan miyar. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments