𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum warahmatullah Malam muna godiya da
fatawoyi, Allah yabiya da gida Aljannah, Ina tambayane akan "mace zata iya
hana mijinta kwanciya da ita idan baya bata ci da sha da kulawa?"
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuh.
Ciyar da mata akan mijinta wajibi ne matukar yana da halin
ciyarwa, wannan kuma dalili ne kai tsaye daga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi kamar yadda Amru ɗan
Ahwas Al'jushamy Allah ya kara masa yarda ya ruwaito wanda hadisin Imamun
Nawawy ya kawo shi acikin littafinsa RIYADUS-SALAHIIN a babi na 34 babin
wasiyya ga mata hadisi na 276 wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya ce ku kyautata masu a ɓangaren
zamantakewa da kuma ciyarwa.
Asali ma saboda haka ne ma Allah maɗaukaki ya fifita maza akan mata, saboda
namiji shine yake da karfin da zai fita ya nemo abinci saboda haka ne ma Allah
maɗaukaki Acikin
Al'qur'ani yake cewa
الرِّجَالُ
قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ وَبِمَا
أَنفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ ۚ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِّلْغَيْبِ
بِمَا حَفِظَ اللَّهُ
MA'ANA "Maza masu tsayuwa ne akan mata, saboda abinda
Allah Ya fifita sãshensu da shi akan sãshe kuma saboda abinda suka ciyar daga
dũkiyõyin su, To, sãlihan mata mãsu biyayyah ne, masu tsarẽwa
ga gaibi saboda abinda Allah Ya tsare"
To amma a harkar zamantakewa na rayuwa akan samu wani lokaci
da Allah yakan jarabci bawansa ta hanyar toshewan hanyar samun abincinsa har
yakaiga ya rasa abinda zai ciyar da iyalinsa acikin gida, kuma bashi da yadda
zaiyi to anan ke a matsayin ki na matarsa sai kiyi hakuri har Allah ya kubutar
daku daga wannan kangin domin shi Allah idan yanason bawansa sai ya jarrabeshi,
don haka idan har haka ne ya faru to a dika yin hakuri da abinda miji ya kawo
har Allah ya bada mafita, muna addu'a Allah madaukaki ya buda kofar samun
halal.
Ana kuma iya samun miji wanda yana da wadata amma kuma
iyalinsa suna cikin qunci wato yana barinsu da yunwa, To koda ace haka ne yake
faruwa bai halatta ba a gareki idan ya nemeki a matsayin ki na matarsa kiqi
amince masa ba, domin kuwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi
ya tsawatar akan haka a wajaje da dama, kamar yadda shima akace masa ya ciyar
dake kuma zalunci haramun ne, Allah dakansa ya hana yin zalunci kuma Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tabbatar mana da cewa shi
zalunci, wani baqin duhu ne a ranar tashin Qiyamah, Allah ya tsare mu.
Hadisi ya inganta daga Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda
ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce
"Idan mutum ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa, sai taqi ta amsa masa to
zata kwana (wato zatayi barci) tana cikin fushin Allah kuma Mala'iku zasuyi ta
tsine mata har ta wayi gari" wannan hadisin Imamun Nawawy ya kawo shi
acikin littafin sa Riyadus-Salahiin a babi na 35 babin da yake magana akan
Hakkokin Miji akan matar sa hadisi na 281.
Kinga wannan hadisin yana nuna wajibi ne idan miji ya kirayi
matarsa ta amsa masa, kai kuma mijinta ga wani hadisi da zamu ambata maka daga
Annabi Sannan kuma Hadisi ya inganta daga Mu'awiya ɗan Haidata Allah ya kara masa yarda ya ce,
nace ya Manzon Allah menene hakkin matar ɗayanmu
akansa? Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce "Ku
ciyar da ita Idan kukaci, kuma Ku tufatar da ita Idan kuma kukayi tufafi Sannan
kada Ku dika dukansu akan fuskokinsu Sannan kada Ku dika roka masu fushin Allah
Sannan kada Ku dika bujire masu (wato kuna yin hijra) sai dai acikin gida (wato
rashin kwanciyar aure da ita)" Abu Dawud, Riyadus-Salahiin hadisi na 277 A
wata Riyawa daga Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda ya ce, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce "Yana daga cikin cikon
kamala na mumini zaku sameshi mai kyakkyawan hali, Sannan kuma mafi alkhairi
daga cikin Ku shine wanda yake mai alkhairi ga Iyalensa" shima duba
Riyadus-Salahiin hadisi na 278.
Don haka dai ke 'Yar uwa kiyi hakuri idan mijin ki bashi
dashi, domin ni nasani da ace gashi yau mai gidan ki ya kawo maki haramun kinci
kinyi kiba ranar Qiyamah kuma ace gashi zaku tafi wuta, to yafi ace kinyi
hakuri kin kwana da yanwa anan duniya da ace gobe Qiyamah kun tsinci kanki a
wuta, don haka kuyi hakuri har Allah ya hore maku, amma idan mijin ki yana da
wadata amma baya azurta ku da abinda zaku ci to anan ma ba'ace idan ya nemeki
kada ki amsa masa ba, a'a kiyi masa Nasiha idan kuma haka bazai yiwu ba to ki
kaishi kara wajen magabata in Allah ya yarda zasuyi masa Nasiha, ko kuma ki
hadashi da malaman unguwar ku suyi masa Nasiha in Allah ya yarda komai zai dai
dai ta, ba'a iya rayuwa idan babu abinci idan haka yaki ya gyaru sai ta kaishi
kotu, Allah ya tsare mu, Allah yasa mudace.
WALLAHU A'ALAM
Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.