Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Mutum Ya Yi Zina Da Wata Mace, Shin Ya Halatta Gareshi Ya Auri 'Yarta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Akkaramakallahu barka da war haka. Allah ya qara basira da nisan kwana. Malam ina da wata tambaya ne wacce wani ya tambayeni ita, Haqiqa tambayar tafi qarfina shine Nace masa ya bari zan tambayo masa nima. Malam Yana tambayar Halaccin Auren wata yarinya da yake nema ne, Amman abin cikensa ya gano Cewa Ya taɓa soyayya da uwar yarinyar a Wani gari can shekarun baya da suka wuce Har sun ta6a Zina da uwar. Yanzu Kuma ya tsinchi kansa a wannan yanayin, A cewarsa Yanzu sun shaqu da yarinyar har sun fara maganar Aure, Amman fa yarinyar Bata San wannan labarin ba. To shine yake tambayar Ya halatta ya cigaba da neman auren yarinyar ko Kuma Aure ya haramta a tsakanisu Saboda wannan dalilin? Allah ya taimaki Malam wannan ita ce tambayar.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ita zina haramun ce. Kuma babu saɓani atsakanin malamai game da girman laifin dake cikinta, Amma duk da haka bata haramta abinda aure ke haramtawa.

Don haka ya halatta ka auri ita wannan yarinyar mutukar dai ba kaine kayi sanadiyyar zuwanta duniya a wannan zinar da kayi da mahaifiyarta ba.

Ibnu AbdilBarri acikin littafinsa Al Istizkar (Juz'i na 5 shafi na 463) ya ce "Malamai sunyi saɓani game da shin idan mutum yayi zina da wata mata, shin ya halatta gareshi ya auri 'yarta ko mahaifiyarta? Ko kuma idan ya taɓa aikata zina da wata mace, shin ya halatta Ɗansa ko mahaifinsa ya aureta? Shin zina tana haramta abinda aure ke haramtawa?

Malik ya faɗa acikin Muwatta cewa "Yin zina da mace ba zai sanya mutumin da yayi zinar da ita ɗin ya haramta ga 'Yarta ko mahaifiyarta ba. Amma idan mutum ya aikata zina da mahaifiyar matar da yake aure, to wannan bazai sanya matarsa ta haramta gareshi ba, sai dai za'a yanke masa hukuncin kisa ne (ta hanyar jefewa) zina bata haramta abinda halastaccen aure ke haramtawa.

Wannan shine fatawar Ibnu Shihab Azzuhriy da Rabee'ah, kuma ita ce fatawar Laythu bn Sa'ad da Shafi'iy da Abu Thaur da Dawuduz Zahiriy kuma ita ce fatawar Abdullahi dan Abbas (ra).

Karshen abinda na cirato daga chan ɗin kenan. Amma wasu malaman suna bada shawarar cewa kada mutum ya auri 'yar matar da ya taɓa zina da mahaifiyarta saboda yin hakan zai Qara sanya yawan haɗuwa ko chudanya tsakaninsa da waccen matar (wato uwar matarsa) saboda gudun kada shaiɗan ya sake rinjayarsu zuwa ga komawa cikin laifin nan da suka taɓa aikatawa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments