Shin Mace Mai Haila Ko Mai Jego Za Ta Iya Karanta Alqur'ani?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin mace mai haila ko jego zata iya karanta Alqur'ani da kallo ko da hadda a yanayi na lalura kamar ta kasance ɗaliba mai koyo ko kuma Malama mai karantarwa??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Babu laifi mace mai haila ko mai jego ta karanta Alqur'ani idan buƙatar hakan ta kama, kamar Malama Ko kuma ɗaliba da zata karanta abunda take koyo da dare ko da rana, amma ta karanta Alqur'ani dan neman lada da yin tilawarsa, abunda yafi falala shine kada tayi, saboda da yawa daga cikin malamai suna ganin rashin halarcin mai Haila ta karanta Alqur'ani".

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    MAI HAILA ZA TA IYA KARANTA ALKUR'ANI A WAYA? 📱

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Malam menene hukuncin macen da batada tsarki tadau wayar tayi karatu aciki?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Alqur'anin Application Nawaya rubutacce wanda ake karantawa, kona sauti wanda ake saurara baya ɗaukar hukuncin alqur'ani cikakke wanda ke rubuce acikin takardu. Ya hallata taɓa shi acikin wayar ko karantashi batare da tsarki ba, saboda rubutun alqur'anin dake cikin waya bakamar rubutunsa bane dake cikin takardu, Kawai wasu na'urorine suke bijirowa sannan saisu gushe, ba haruffa bane tabbatattu, waya kuma ta haɗa Qur'anin dawasu abubuwan.

    Amma karantashi acikin takardu sharaɗi ne kai tsaye sai idan mutum yanada tsarki, Saboda Abunda yazo acikin hadisi shahararre ( Baya halatta a ɗauki alqur'ani ko shafarsa sai wanda yake da tsarki) Dakuma abunda yazo na maganganun sahabbai da kuma tabi'ai, akan haka jamhurdin malamai suka tafi akai, Shine wanda yake da hadasi haramun ne yataɓa alqur'ani saboda tilawa kowanin tilawa.

    Abisa wannan zai bayyana garemu cewa Alqur'anin dake cikin waya da sauran na'urori wanda ake taskance abubuwa acikinsu baya ɗaukar hukuncin Alqur'anin dake rubuce acikin takardu, domin rubutunsa ya saɓa da wanda yake acikin takardu, bazaka samesu da siffofinsu da'ake karantasuba, saidai asamesu asifar yanada na'urar dake bayarda haruffan yayinda aka nema, saita bayyanar dashi a screen idan kuma ka tsallaka kan wani abun acikin wayar sai haruffan su kau, Abisa wannan ya halatta ɗaukar wayar ko shafarta, ya halatta karantashi, koda mutum baida tsarki.

    Alqur'anin dake rubuce acikin takardu Bai hallata shafarsa ko taɓa shiba saiga wanda yakeda tsarki kamar yanda yazo acikin hadisi, Amma waya ba'a kiranta Alqur'ani.

    Karanta Alqur'ani acikin waya saukakawane ga mai haila, da kuma wanda ɗaukar alqur'anin gaba ɗaya yake masa wahala, ko yake wajan dazai masa wahala yin alwala, saboda rashin tsarki.

    Saboda haka ya halatta macen dabata da tsarki ta karanta alqur'ani na appilication, ba haramun bane danta ɗauki wayar kotayi karatu dashi lokacin da batada tsarki.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.