Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Taba Alqur'ani Ga Daliba Ko Malama Mai Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, don Allah zan iya ɗaukar Alqur'ani izifi sittin a halin ina cikin rashin tsarki kuma ga shi za ni Islamiyya muna yin hadda ne. Kuma malam wata rana malaminmu ya kan ce ka miqo mai Alqurani kuma ba ka da tsarki ya za ka yi saboda wasu sun ce wai ba a son wanda ba muharraminka ba ya san ba ka da tsarki, don Allah a taimaka mana Allah ya qara basira ya kuma shirya mu a bisa tafarkin addini.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ya halasta mai haila ɗalibar Alqur'ani ko malamar Alqur'ani su taɓa shi a lokacin da suke kan darasi ko suke hanyar zuwa ɗauko darasi gwargwadon buqatarsu ko don wata maslaha, ko da kuwa izu sittin ne.

Haka nan duk hadasin da malamai suka ce yana hana ɗaukar Alqur'ani saboda shi, to ana ɗaga wa ɗalibai da malaman Alqur'ani qafa musamman a lokacin da buqatar darasinsu ta taso masu, ko wata maslaha da ta tilasta masu taɓawar musamman a fahimtar Mazhabarmu ta Malikiyya.

Duba Assharhul Kabeer ko Háshiyatud Dasuqiy (1/125, 126).

Amma idan ba ɗaliba mai koyon karatu ba ne, kuma ba malama mai koyar da karatun ba ne, to bai halasta su taɓa Alqur'ani a halin janaba ko haila ba a fahimtar mafi yawan malamai.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments