Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mai Azumin Da Ya Suma

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Wanda yake cikin azumi sai kuma ya suma, daga baya kuma sai ya farfaɗo. Shi ne ake tambaya: Azuminsa na nan ko ya karye?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Kamar yadda shari’ar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ce take da ikon bayani a kan yadda ake yin kowane aikin ibada har da Azumi, to ita ce dai take da ikon bayanin abubuwan da suke karya Azumin.

A cikin duk abubuwan da suka zo a cikin Al-Kitaab Was Sunnah game da masu ɓata azumi, babu ɗaya da ke nuna cewa gushewar hankalin mai azumi ta hanyar suma yana ɓata azumin!

Don haka dai, gushewar hankali ta hanyar barci ko suma ko farfaɗiya ma, ba su ɓata azumi. Idan ya farfaɗo sai kawai ya yi alwala, ko kuma wanka ya cigaba da sallah da azuminsa.

Allaah ya warkar da duk marasa lafiyan cikinmu, ya sa larurarsu ta zama kaffara ga laifukansu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments