Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yi Mafarkin Aljani Ya Sadu Da Ni Ina Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam ya ibada, jinnul ashiq (Wato aljanin soyayya) yana saduwa dani Koda Ina azumi, yaya hukuncin azumi na?

Lokacin da nake yarinya na kasance Ina mafarkin an dakko mu nida Yan gidanmu za'a yanka mu duka, Dan Allah me haka yake nufi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Yawancin irin wannan saduwar da shaiɗanun Aljanu ke yi da mutane, yana faruwa ne acikin barci. Amma hukuncinsa yana dangantuwa ne zuwa ga fitar maniyyi ko rashin fitarsa.

Akwai hadisi wanda Malaman hadisi da dama sun fitar dashi ta hanyar Ummu Salamah, da Nana A'ishah da kuma Anas bn Malik (Allah ya yarda dasu baki ɗaya).

Acikin riwayar Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya bayar da fatawa ga matar da taga irin abinda mazaje ke ganinsa acikin barci (wato mafarkin saduwa) yace "zatayi wanka". Acikin riwayar Imamul Bukhariy ya Qara da cewa "idan taga ruwa (Wato maniyyi).

Sai Nana Ummu Salamah tare da mamaki tace "Dama irin haka yana faruwa?"

Sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace mata "ta ina ake samun kamanni?".

Shaikh Isma'eel As-San'aniy yace irin wannan ta faru ga mataye da yawa daga matan Sahabbai. Misali akwai Khaulatu bintu Hakeem acikin riwayar Imamu Ahmad da Nisa'iy da Ibnu Maajah. Ya faru kuma ga Sahlatu bintu Suhail (ra) acikin riwayar Tabaraniy. Hakanan ya faru ga Busratu bintu Safwan acikin riwayar Abubakr ibnu Abee Shaibah.

Wannan hadisin hujjah ne akan cewa lallai mace takan ga irin abinda namiji yake gani acikin barcinsa, amma abinda ake nufi idan har tayi inzali (Wato taga fitar maniyyi ajikinta bayan ta farka).

To amma idan mutum (namiji ko mace) ya yi mafarkin jima'i amma yayin da ya farka ya duba jikinsa bai ga maniyyi ba, to yin wanka bai wajaba akansa ba. Kamar yadda Shaikh Abdurrahman Al-Akhdhariy ya faɗa acikin shahararren littafinsa (Matnul Akhdhariy) acikin babin dake magana akan abubuwan dake wajabta wanka..

Hakanan ko kinga fitar maniyyi ko baki gani ba, azuminki yana nan kalau bai karye ba. Wanka kawai zakiyi idan har kinga alamar maniyyin.

Amsar tambayarki ta biyu :Irin waɗannan mafarkan shirme ne kawai irin wanda shaiɗanu ke haddasawa. Amma yafi faruwa alokacin da mutum ya kwanta ba tare da yin addu'a ba. Musamman ma waɗanda ke fama da matsalar shafar Aljanu.

Maganin abun shi ne kije ayi miki ruqyah domin rabuwa da jinnul ashiq ɗin, sannan idan zaki kwanta barci ki rika yin alwala, ki karanta ayatul kursiyyi kafa ɗaya, Suratul Ikhlas da falaqi da nasi kafa uku-uku.

WALLAHU A'ALAM. 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments