Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallar Tahajjud A Masallaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum dafatan malam yana cikin koshin lafiy Amin. malam ni tambayata ita ce yana da kyau mutum yayi sallar Tahajjud a masallaci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace “Mafificiyar sallarku (tahajjud) wacce kuka yita a gidane sai dai sallar farilla kawai ”(Dubi Tirmizi Bisharhil Ahuz 2\00).

An ruwaito acikin Bukhari mafificiyin sallar mutum a gidansane sai dai sallar Farilla kawai.

(Dubi Fathul Bary 3\0 ko Umdatul Qary.

Acikin Hadisin Abdullahi bn Sa,ad yace “Na tambayi Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam akan sallar mutum tahajjud a gidansa dayinta a masallaci wanne yafi? sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace “shin baka ganin gidana ba wanda yafi shi kusa da masallaci, amma nayi sallah a gidana (tahajjud ) yafi nayi sallah amasallaci sai dai sallar farilla” (Dubi Ibn Majah 1\39).

An karbo daga Zaidu bn Sabit (RA) daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa “Sallar mutum agidansa tafi sallarsa a masallacina. (wato masallacin Annabi). sai dai sallar farilla”(Dubi Abu Dawud 1\9, taglikutta aliq 1/ 239 Nailal Audar 3\5 ko Ash shama,il 150).

Don haka yin nafilar tahajjud a gida yafi yinta akowani masallaci falala. tunda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yafifita nafila agidage a bisa masallacinsa.

Ananne Hafizu bn hajar yake cewa: yin tahajjud agida lallai shiyafi falala ga al’umma gaba ɗaya, domin shine amsar da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya baiwa mai tambaya, fatahul bary juzu’I na 3 shafi na 25\6 Abu daud juzu’I na1 shafi na 69 Tajujjami’u juzu’I na 1 shafi na 332 Nailul Audhar juzu’Ina 3 shafi na 95 Tagliqutta’aliq juzu’I na 1 shafi 239 Ashshama’il shafi na 157

Amma duk da haka rafkanannu acikin garuruwan kasannan (Nigeria) suna karfafa mata akan fitowa masallaci da tsakar dare domin yin sallar Tahajjud. Alhali Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yace da ummu Humaidu Allah ya yarda da ita, yayin da tazo gurin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam tace “ Ya Rasulullahi inaso nayi sallah tare da kai” sai yace “Na sani kinaso kiyi sallah tare dani, amma kiyi sallah a’yar kurin ɗakinki yafi kiyi sallah a falonki, kiyi sallah a tsakar gidanki yafi kiyi sallah a masallacin mutanenki, kuma kiyi sallah a masallacin mutanenki yafi kiyi sallah a masallacina wannan”.(Ahmad ne ya ruwaito 6\71 da Ibn Khuzaima acikin sahihinsa 3\5 da Ibn Abdul Barri acikin Tamhid 23\98).

Wannan yana nuna sallar mace ta farillah a cikin gidanta yafi tayi a masallaci to yaya kuma Nafila. Donhaka yin tahajjud a gida yafi yinta a masallaci a wajen mace ko namiji.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments