Ticker

6/recent/ticker-posts

Miji Mai Shan Giya

TAMBAYA (81)

Dan Allah malam ina son ka taimakamin da addua da zan Rika karantawa Allah ya raba mijina da shan giya

AMSA:

Alhamdulillah

To da farko dai muna roqon Allah Subhanahu wata'ala ya taimaka miki ki ci gaba da hakurin zama dashi tare da ci gaba da roqon Allah Subhanahu wata'ala ya shirye shi ya daina aikata wannan mummuna aikin, domin kuwa wannan yana daya daga cikin jarabawar da Allah Subhanahu wata'ala yake ga bayinSa

Na biyu kuma, ki same shi ido da ido ki tambayeshi me zai fada game da fadin Allah Subhanahu wata'ala akan wannan ayar

( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ )

المائدة (90) Al-Maaida

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.

Amsar da zai baki itace zata tabbatar miki da ko zai ji tsoron Allah ko Kuma zai danne gaskiya ya ci gaba da bin son zuciyarsa. Ki ce masa shin yanzu haka kake son ka taso yayanmu su ga kana shan giya ? Shin zaka so suma su dinga koyi dakai ? Da sauran tambayoyi makamantan wadannan cikin hikima da siyasa

Dangane da kuma hukuncin shari'ah akan zama tare dashi, ya halatta ki ci gaba da zama tare dashi a matsayinsa na musulmi indai har hakan bazai cutar da lafiyar ki da kuma lafiyar yayan ki ba

Shaikh Ibn 'Uthaymeen (Rahimahullah) yace: "Ina ganin idan har ta bashi shawara akan ya daina shan giyar kuma yayi biris da shawarar to tana da damar zuwa wajen alqali ya raba auren nasu. Amman da akwai dalilan da yasa bai kamata a raba auren ba, saboda tana da Yaya tare dashi, rabuwar ka iya haifar da wasu matsalolin na daban. Indai har laifinsa bai Kai laifin kafirci ba to babu zunubi akanta idan ta hakura ta ci gaba da zama tare dashi saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo. Amman idan ya zamana laifin sa yakai na kafirci kamar barin sallah to ya zama wajibi ta gaggauta rabuwa dashi"

Al-Liqa' al-Maftooh, Q. 518

Shawara ta biyu kuma itace: Ta miqawa Allah Subhanahu wata'ala lamuranta ta hanyar yin addu'ar Istikhara kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar, sannan tayi tunani da nazari akan abinda take tunanin shine mafita a gareta, ta sanar da iyayenta da waliyyanta. Kamar yanda riwaya ta tabbata cewar: "Babu wanda yake rashi idan yayi addu'ar Istikhara haka ma ba wanda yake da na sani idan ya nemi shawarar mutane. Ko dai ta zabi rabuwa dashi ko kuma ta tsaya, ta barwa Allah Subhanahu wata'ala zabin, tayi haquri da sakamakon da zai biyo baya domin samun ladan hakuri

Allah Subhanahu wata'ala yace

 وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ )

البقرة (155) Al-Baqara

Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri

Wallahu ta'ala a'alam

~ Islam Guide

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments