Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Mutum Yana Cikin Yin Sahur, Sai Yaji Kiran Sallah (Assalatu)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum malam Idan mutum yana cikin yin sahur, sai yaji kiran sallah (Assalatu) yaya zaiyi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. A irin wannan halin mutum zai qarasa abin da ke hannunsa ne. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira yace: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: "Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiyeta, har sai ya biya buqatarsa."

Amma anan sai ayi hattara, kada amayar da irin wannan dabi'a tazama al'adar kullum.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments