𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Menene hukuncin
wanda yayi istimna'i da rana ana azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, Istimná'i shi
ne mutum ya yi wasa da al'aurarsa har ya fitar da maniyyi ba ta hanyar jimá'i
ba. Yin hakan laifi ne babba, amma laifin yinsa a watan Ramadana yana qara
girmama fiye da a sauran watanni.
An tambayi Allama Ibn Utsaimeen
Rahimahullahu a game da wanda ya yi Istimná'i, shin kaffara ta wajaba a kansa?
Sai Allama ya ba da amsa da cewa: "Idan mai azumi ya yi wasa da al'aurarsa
(istimná'i) har ya fitar da maniyyi, to ya wajaba a kansa ya rama azumin wannan
yini da ya yi istimná'i a ciki, amma babu kaffara a kansa, saboda kaffara ba ta
wajaba sai idan jimá'i ne aka yi".
Duba Majmú'u Fataáwá na Ibn
Uthaimeen 19/233.
Kuma wanda ya sami kansa a wannan
mugun aikin, bai halasta a gare shi ya ci abinci ko abinsha a wannan yinin
saboda an ce azuminsa ya karye ba, wajibi ne a kansa ya kiyaye alfarmar watan
ta hanyar kamewa daga ci ko sha duk da karyewan azumin nasa. Sannan ya wajaba a
gare shi ya yi nadama tare da kyakkyawar tuba zuwa ga Allah, saboda wannan
babban zunubai da ya aikata na Istimná'i da kuma karya azumi, kuma ya yawaita
kyawawan ayyuka, saboda kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.✍
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
HUKUNCIN WANDA YA YI ISTIMNA'I DA RANA
ALHALI YANA AZUMI:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, mene ne hukuncin samari da yan mata da suke istimna'i, suna biyawa
kansu bukata da rana alhali suna azumi. shin kaffara ta wajaba a kansu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, Istimná'i shi ne mutum ya yi wasa da al'aurarsa har ya fitar da maniyyi
ba ta hanyar jimá'i ba. Yin hakan laifi ne babba, amma laifin yinsa a watan
Ramadana yana qara girmama fiye da a sauran watanni.
Abin Mamaki
ne wai Ana yin Azumi Ana Neman Gafaran Allah, Amma Wasu Ƴan Matan
Biyawa Kansu Bukata Suke yi gurin Kallon Alfasha Tsiraicin Arna, har Sai ta
Fitar da Maniyyi ko Maziyyi da Ranan Alhali Kuma Ana Azumi. Hakanan Maza Samari
Wani Budurwa Yake Ɗaukowa Yana Zina da Ita da Rana a Cikin
Watan Azumi Kuma Dukkan Su Musulmai ne Inna illahi Wa'inna illahin Rajee'um.
Subhanallah. Wanne Irin Masifa ce Wannan? Wanne Irin Bala'i Ce Wannan? Ke Kina
Son Biyawa Kanki Bukata Mene ne Zai Hanaki Yin Aure Koda Babu Kayan Lefe da
Sauran su? Kin Sa Buri a Ranki Samari Sun Ki Zuwa Ga Sha'awa na Tayar ki Kin ga
Gara Bin Umurnin Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Kin qi Yin
Aure Yaya Ba Za ki Rika Saɓawa Allah ba? Idan Allah ya ɗauki Ranki ba ki
Shiryawa Mutuwa me Za ki gayawa Ubangijin ki? Wallahi Ku Ji Tsoron Allah Ƴan Mata da Samari har da Matan Aure Masu Irin Waɗannan Ayyukan, Ba
Zaku Taɓa Tsira a Gaban
Allah ba a Ranan Alkiyama.
An tambayi
Allama Ibn Utsaimeen Rahimahullahu a game da wanda ya yi Istimná'i, shin
kaffara ta wajaba a kansa? Sai Allama ya ba da amsa da cewa: "Idan mai
azumi ya yi wasa da al'aurarsa (istimná'i) har ya fitar da maniyyi, to ya
wajaba a kansa ya rama azumin wannan yini da ya yi istimná'i a ciki, amma babu
kaffara a kansa, saboda kaffara ba ta wajaba sai idan jimá'i ne aka yi".
Duba Majmú'u
Fataáwá na Ibn Uthaimeen 19/233.
Kuma wanda
ya sami kansa a wannan mugun aikin, bai halasta a gare shi ya ci abinci ko
abinsha a wannan yinin saboda an ce azuminsa ya karye ba, wajibi ne a kansa ya
kiyaye alfarmar watan ta hanyar kamewa daga ci ko sha duk da karyewan azumin
nasa. Sannan ya wajaba a gare shi ya yi nadama tare da kyakkyawar tuba zuwa ga
Allah, saboda wannan babban zunubai da ya aikata na Istimná'i da kuma karya
azumi, kuma ya yawaita kyawawan ayyuka, saboda kyawawan ayyuka suna tafiyar da
munana.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.