Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Ci Abincin Sahur Daidai Lokacin Ketowar Alfijir

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam, Ina mura Na sha magani kuma Ina da niyyan daukar azumi, sakamakon maganin na makara cin sahur 5:00 daidai na falka, sai na yi amfani da 5 minites na ci abinci, wato 5:05 kenan mallam ya matsayin azumina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa matuqar lokacin da mutum ya ci abincin sahur Alfijir na gaskiya ya keto koda da minti ɗaya ne, to ba shi da azumi, sai ya rama wannan azumin. Amma idan daidai qarfe biyar ɗin nan Alfijir na gaskiya bai riga ya keto ba, to azuminki ya inganta, in kuwa Alfijir na gaskiya ya riga ya bayyana ko da kuwa da minti ɗaya ne, to lallai ba ki da azumin wannan yinin.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments