𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin wanda Maziyyi
yafito masa yana Azumi, Shin azuminsa ya lalace ko bai lalace ba??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alal-Haƙiƙa Malamai Fuƙaha'u
sunyi Saɓani dangane
da hukuncin cewa Shin Maziyyi yana iya ɓata
azumi ko a'a, Sannan dolene sai Mutum yarama wannan azumin kenan kokuma a'a?
Mazhbin HANABILA da MALIKIYYA
suntafi akan cewa Maziyyi yana ɓata
azumi idan yakasance Mutum shi ne ya yi Sababin fitarsa da gangan, kamar ya
Shash-Shafa jikin Matarsa, ko ya rungumeta, ko ya yi wasa da'ita, ko ya yi mata
Kiss (sumbata), kokuma wani abu makamancin haka wanda zai sashi yaji daɗi har Maziyyin yafita
sukace azuminsa ya lalace, amma HANAFIYYA sukace idan yakasance bai taɓa jikintaba kawai kallonta
ya yi tayi har Maziyyi yafita to azuminsa yananan bai ɓaciba, yayinda sukuma MALIKIYYA suke ganin
cewa ai koda ta hanyar kallone yafita to azumi ya lalace, daga cikin Dalilansu
sunkafa Hujja da Hadisin A'isha Matar Mαиzoи Aʟʟαн
( Sallallahu alaihi Wasallam ) wanda take cewa
"
ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ( ﷺ ) ﻳﻘﺒﻞ ﻭﻫﻮ ﺻﺎﺋﻢ، ﻭﻳﺒﺎﺷﺮ ﻭﻫﻮ ﺻﺎﺋﻢ، ﻭﻟﻜﻨﻪ ﻛﺎﻥ
ﺃﻣﻠﻜﻜﻢ ﻹﺭﺑﻪ "
( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ )
MA'ANA
Mαиzoи Aʟʟαнn (Sallallahu alaihi Wasallam ) Ya kasance
yana sumbatar (Matansa) yana azumi, haka kuma yana rungumar (Matansa) yana
azumi, Saidai yafiku mallakar bukatarsa
Sukace Annabi (Sallallahu alaihi
Wasallam) bayayin abinda zai tayar masa da Sha'awa, danhaka kenan duk wanda ya
yi abinda yasa har Maziyyinsa yafita to wajibine sai yarama
Amma Mazhabin HANAFIYYA dakuma
SHAFI'IYYA suntafine akan cewa Kwata-Kwata fitar Maziyyi ta kowace irin hanyace
baya karya azumi, Misali: yafitane ta hanyar wasa da Matarsa, ko runguma, ko
Sumbata (Kiss), ko kallon wani Film ko Hoto na batsa, ko Mutum ya yi wasa da
gabansa amma Maniyyi bai fitoba saidai Maziyyi, kokuma wani abu makamancin
haka, Hujjarsu anan ita ce, sukace babu wani Dalili daga Al-Ƙur'ani
ko Hadisi da yake nuna cewa Maziyyi yana ɓata
azumi,
Saidai magana mafi inganci
dangane da wannan Mas'ala kamar yadda dayawa daga cikin Malamai sukafi
rinjayarwa ita ce, fitar Maziyyi ta kowacce irin hanya baya lalata azumi, domin
kuwa idan akace Maziyyi yana lalata azumi to akwai Mutanen da saboda ƙarfin
Sha'awarsu hakan zai kaisu ga sai sun rama kusan dukkan azumi 30 ɗin dasukayi, wanda hakan
kuma zai zama wahalane agaresu, ita kuma Shari'a tazone danufin ta sauƙaƙa,
domin akwai wanda indai zai kalli Matarsa to kuwa sai Maziyyi yafito masa,
Saidai Malamai sukace Makaruhine Mutum ya yi dukkan wani abinda yasan cewa zai
iya tayar masa da Sha'awa har Maziyyinsa yafita alhali yana Azumi
шαʟʟαнυ-α'αʟαm
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.