Hukuncin Nafilolin Da Ake Yi A Kowace Ranar Azumi Na Ramadan

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaamu Alaikum. Malam, shin yaya matsayin irin nafilolin da ake turo wa mutane a kan kowane kwanakin Ramadan da kalar addu’ar da mutum zai yi, da irin nafilar sallar da za a yi a kowace rana ko dare na Ramadan, da kuma irin surorin da za a karanta a kowace raka’a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Waɗannan duk suna daga cikin ƙirƙirarrun al’amura ne a cikin addini, bayan wucewar mutanen kirki. Domin babu wata aya ko wani hadisi sahihi da ya tabbatar da su.

    Kuma da ma musulunci, kamar yadda manyan malamai irin su Ibn Al-Qayyim (Rahimahumul Laah) suka faɗi, shi ne: Maganar Allaah da maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) kaɗai, sai kuma maganar Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum).

    Abin da ya tabbata a cikin Sunnah Sahihiya shi ne yawaita ayyukan alkhairi a cikin Ramadan, kamar

    1. Tilawar Alqur’ani.

    2. Sauraron tafsirinsa da ƙara fahimtarsa.

    3. Sallolin nafila.

    4. Addu’o’i.

    5. Sadaka.

    6. Sada zumunci.

    7. Sadar da alkhairi ga jama’a, da sauransu.

    A wurin sallar ba a ce a keɓance irin surori ko adadin raka’o’in kowace raka’a ba, haka kuma ba a keɓance wani nau’i ko lafazin addu’o’in kowace rana ko dare ba.

    Malamai kuma sun yarda cewa: Daga cikin hanyoyin da Bidi’a ke saɗaɗowa ta shiga cikin addini, akwai: Duk ibadar da Allaah ko Manzonsa suka sake ta haka nan ba da ƙaidi ba, sai kuma wani ko wasu su yi mata ƙaidi da wuri ko lokaci ko adadi!

    Mun dai riga mun san cewa: Dukkan bidi’a ɓata ce, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) ya yi bayaninsa a cikin hadisai sahihai, kamar hadisin Al-Irbaad Bn Saariyah (Radiyal Laahu Anhu) wanda Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah suka fitar da shi, cewa

    Watarana Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) ya yi mana limancin sallah [Sallar Asubah], sai kuma ya fuskanto mu ya yi mana wa’azi mai ratsa jiki, wanda ya sa idanu suka zubar da hawaye kuma zukata suka ƙara tsoro, sai wani mutum daga cikin Sahabbansa ya ce: Ya Manzon Allaah! Kamar wa’azin mai ban-kwana?! To, ka yi mana wasiyya mana!

    Sai ya ce: {Ina yi muku wasiyya da jin tsoron Allaah, kuma da ji da biyayya ko da kuwa bawa ne Bahabashe aka shugabantar a kanku, domin daga cikinku duk wanda ya yi tsawon rayuwa a bayana to kuwa zai ga saɓani mai yawa. Don haka, sai ku kama Sunnata da Sunnar Halifofin nan Shiryayyu, tabbatattu a kan shiriya a bayana, kuma ku damƙe ta da turamen haƙora. Kuma ku yi nesa da ƙirƙirarrun al’amura, domin kowace ƙirƙira bidi’a ce, kuma kowace bidi’a ɓata ce}.

    A cikin wata riwaya ta An-Nasaa’iy ya ce: {Kuma kowace ɓata tana cikin Wuta}.

     (Dubi ƙarin bayanin wannan hadisin a cikin Sharhin Al-Arba’uunas Salafiyyah # 3).

    Allaah ya datar da mu ga yin riƙo da sunnah da nisantar bidi’a.

     WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.