𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene hukuncin wani ruwa brown
dake fitowa ta gaban mace kafin tafara al'ada?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To shidai wannan nau'i na ruwa
brown dayake fitowa mata ya kasune gida uku
①-kodai yafito kafin haila.
②-kokuma yafito bayan mace tagama haila.
③-kokuma yafito alokacin da mace take haila.
① Idan yakasance yafitone kafin haila abinda
malamai sukace shine, idan yakasance wannan ruwa kamar wata muqaddimace tazuwan
jinin haila to hukuncinsu ɗaya
da haila, tayadda ruwan yanazuwa kuma kafin ya ɗauke
sai jini yabiyo bayansa, kokuma kafin yafito mace taji wata alama datasaba
jinta idan zatayi al'ada, dagabaya kuma saitaga wannan ruwa brown yafito to
zata dakatar dayin sallah.
② Amma idan mace taga wannan ruwa batare
dataji wata alama nazuwan hailaba, kokuma yakasance ansamu tazara kamar kwanaki
biyu ko samada hakan tsakanin zuwan ruwan saikuma ya ɗauke to hukuncin tsarkine akanta.
③ Hakanan idan mace taga wannan ruwa
yazomata bayan tagama al'ada tayi tsarki to shima bakomai akanta zataci gaba
dayin sallah dakuma azumi, saidai akwai malaman dasuke ganin cewa zuwan wannan
ruwa kafin jinin haila kokuma yazo bayan angama jini to duk hukuncinsu ɗaya awani QAULIN na
Malamai.
Ammadai magana mafi inganci itace
zuwan wannan ruwan bayan gama jinin al'ada indai ansamu 'yartazara tsakanin ɗaukewar jinin dakuma
zuwan ruwan to wannan baya hana mace tacigaba dayin ibadarta.
Amma idan yakasance mace taga wannan
ruwane atsakanin al'adarta kamar ace tayi kwana biyu jini yana zuwa mata akwana
na uku kuma saitaga wannan ruwa yafito sannan akwana na huɗu ko na biyar saitasake
ganin jini, to wannan ruwa hukuncinsa ɗaya
da jinin al'ada, mace zata jirane harsai ya ɗauke
sannan tayi wanka.
Mai neman karin bayani sai yaduba
Waɗannan litattafai
kamar haka
ﺍﻟﺪﻣﺎﺀ ﺍﻟﻄﺒﻴﻌﻴﺔ ﻟﻠﻨﺴﺎﺀ ( ﺹ 19 )
ﺛﻤﺮﺍﺕ ﺍﻟﺘﺪﻭﻳﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺜﻴﻤﻴﻦ ( ﺹ 25 )
ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ ( 18/296 )
ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ( 1/202 )
ﺍﻟﻤﺠﻤﻮﻉ ( 2/422 )
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.