𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene hukuncin wani farin ruwa
ko wani danshi-danshi dake fitowa Mace ta gabanta (farji), Shin idan ta ganshi
a pant ɗinta lokacin
da zatayi Sallah dolene saita cire pant ɗin
kokuma zata iyayin Sallah dashi ahaka?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dangane da Magana akan Farin-Ruwan
dake fito daga farjin Mace Mālamai sunyi Saɓāni
akansa
1. Qauli nafarko shine Mazhabin
SHĀFI'IYYA dakuma HANĀBILA Suntafine akancewa ruwan dake fitowa daga
Farjin-Mace mai tsarkine danhaka koda yātaɓa
tufāfinta to zata iyayin Sallah dashi ahaka bāsai tā wankeba, sukace bābu wani
dalilin dayazo yanuna cewa wannan ruwan ba mai tsarki bane, kuma dama a Asali
komai amatsayin mai tsarki yake sai in ansāmu wani dalilin da yazo yace abu
Kazā-da-Kazā bā mai tsarki bane
2. Qauli nabiyu kuma shine
Mazhabin MĀLIKIYYA da HANAFIYYA Suntafi akan cewa ruwan dake fita daga farjin
Mace najasāne, danhaka idan yataɓa
tufāfi to dolene sai anwankeshi sannan ayi Sallah dashi, to amma Maganar datafi
INGANCI acikin Zantukan da Mālamai sukayi itace, Alal-HaQiQā wannan ruwa kokuma
danshin dake fita daga Farjin-Mace ba najasa bane, Saboda ba'asamu wani dalili
dayanuna cewa najasa neba.
Bāya gahaka kuma Sai Mālamai suka
sākeyin wani Sabānin akancewa Shin ko fitar wannan ruwan yana'iya warware
Alwala kokuma ā'ā?
Mafi rinjayen Mālamai sukace
fitarsa yana warware alwala, domin sunaganin cewa ruwan dakefita daga
Farjin-Mace hukuncinsa daidai yake da hukuncin Mace Mai jinin Istahāra, shiyasa
suka kafa hujja dacewa Mαиzoи Aʟʟαн
(Sallallahu alaihi Wasallam) Yā umarci Mai jinin Istahāra dacewa tariƙayin
alwala akowacce Sallah, danhaka sukace shima wannan Danshin ko ruwan dake fita
daga farji za'a riskar da hukuncinsane da na mai Istahāra
Amma agefe ɗaya akwai Mālaman dasuke
ganin cewa fitar wannan ruwa baya warware alwala kamar yadda (Ibn-Hazm) Yakāwo
acikin littafinsa maisuna: (Al-Muhallā-Bil-Āsār) to saidai Mālamai dayawā
sukace wannan Maganar tasa bashida wani ingantaccen dalili akanta
Danhaka kenan Maganā mafi inganci
acikin zantukan da Mālamai sukayi akan wannan Mas'ala itace, cewa ruwan dake
fitowa daga Farjin-Mace idan yakasance yāfitone daga cikin asalin mahaifā
(wanda kuma dāmā gālibi ta mahaifar yake fitowa) sukace to ruwane mai tsarki
danhaka koda yātaba tufafi ko Pant to za'a iyayin Sallah dashi bātare da an
wankeba, amma idan wannan ruwa yāfitone daga ƙofar da fitsāri yake fitowa to najasane, sannan kuma idan Mace
tanada alwala sai taga wannan ruwan yāfito
mata to alwalarta tā
warware danhaka dole sai tasake wata
Allah ta'ala yasa mudace
AMSAWA: Mυѕтαρнα Uѕмαи
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.