Ticker

6/recent/ticker-posts

Ciwon Da Ke Hana Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wane irin yanayin ciwo ne ke sanya mara lafiya ya ciyar? Ko olsa mai tsanani na iya shiga ciki?

𝐀𝐌𝐒��❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Allaah dai cewa ya yi

وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْر

Kuma wanda ya zama mara lafiya ko a cikin tafiya to sai ya biya a waɗansu adadin kwanaki na daban. Allaah yana nufin sauƙi ne gare ku, kuma baya nufin tsanani a gare ku. (Surah Al-Baqarah: 185).

A ƙarƙashin wannan ayar duk wanda ya shiga halin da za a kira shi mara lafiya ko matafiyi, to ya halatta ya ajiye azuminsa, ya rama a lokacin da ya samu iko.

Al-Qurtubiy a cikin Tafsirinsa: Al-Jaami’u Li Ahkaamil Qur’aan ya kawo bambancin fahimtar malamai a kan wannan matsalar ta azumin mara lafiya, a ƙarshe kuma ya zaɓi maganar Muhammad Bn Seereen (Rahimahul Laah) wanda ya ce:

مَتَى حَصَلَ الْإِنْسَانُ فِي حَالٍ يَسْتَحِقُّ بِهَا اسْمَ الْمَرَضِ صَحَّ الْفِطْرُ، قِيَاسًا عَلَى الْمُسَافِرِ لِعِلَّةِ السَّفَرِ، وَإِنْ لَمْ تَدْعُ إِلَى الْفِطْرِ ضرورة.

Duk lokacin da mutum ya shiga wani halin da ya cancanta sunan rashin lafiya ya hau kansa, to ajiye azumi ya inganta a gare shi. Wannan ƙiyasi ne a kan matafiyi saboda dalilin tafiya, ko da kuwa babu wata larurar da ta takura masa ga ajiye azumin. (Tafseer Al-Qurtubiy: 2/276).

Daga nan sai kuma ya kawo ƙissar Al-Imaam Al-Bukhaariy (Rahimahul Laah) wanda shi kuma ya ce

اعْتَلَلْتُ بِنَيْسَابُورَ عِلَّةً خَفِيفَةً وَذَلِكَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ، فَعَادَنِي إِسْحَاقُ بْنُ رَاهْوَيْهِ نَفَرٍ مِنْ أَصْحَابِهِ فَقَالَ لِي: أَفْطَرْتَ يَا أَبَا عَبْدِ اللَّهِ؟ فَقُلْتُ نَعَمْ. فَقَالَ: خَشِيتَ أَنْ تَضْعُفَ عَنْ قَبُولِ الرُّخْصَةِ. قُلْتُ: حَدَّثَنَا عَبْدَانُ عَنِ ابْنِ الْمُبَارَكِ عَنِ ابْنِ جُرَيْجٍ قَالَ قُلْتُ لِعَطَاءٍ: مِنْ أَيُّ الْمَرَضِ أُفْطِرُ؟ قَالَ: مِنْ أَيِّ مَرَضٍ كَانَ، كَمَا قَالَ اللَّهُ تَعَالَى:" فَمَنْ كانَ مِنْكُمْ مَرِيضاً"

Na yi ɗan rashin lafiya ba wani mai tsanani ba a garin Naisabur a watan Ramadan, sai Ishaaq Bn Rahwuyah da wasu ɗalibansa suka zo duba ni. Sai ya ce mini: ‘Baban Abdullahi, ka ajiye azumin ko?’ Na ce: ‘E.’ Ya ce: ‘Wato ka ji tsoron kar ka yi rauni a karɓar sassaucin ne ko?’ Sai na ce: Malaminmu Abdaanu ne ya ba mu hadisi daga Ibn Al-Mubaarak, shi kuma daga Ibn Juraij, ya ce: Na tambayi Ataa’u: ‘Wai wane irin rashin lafiya ne yake janyo a ajiye azumi?’ Sai ya ce: ‘Kowane irin rashin lafiya kawai. Kamar yadda Allaah Ta’aala ya ce: ‘Duk wanda ya zama mara lafiya a cikinku.’ (Tafseer Al-Qurtubiy: 2/277)

Wannan a kan rashin lafiyar da ake sa ran yiwuwar warkewa kenan.

Amma idan rashin lafiya mai tsanani ne wanda ake da marinjayin zaton cewa abu ne mawuyaci a warke, to sai malamai suka yi kiyasin mai larurar da kamar tsofaffi waɗanda Ubangiji Ta’aala ya faɗa a kansu cewa

وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِين

 Kuma yana a kan waɗanda suke ɗaukar Azumin da wahala bayar da fansa na abincin musakai. (Surah Al-Baqarah: 184).

Kuma babban malamin Tafsiri a cikin Sahabbai, wato Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce

لَيْسَتْ بِمَنْسُوخَةٍ، هُوَ الشَّيْخُ الْكَبِيرُ وَالْمَرْأَةُ الْكَبِيرَةُ لَا يَسْتَطِيعَانِ أَنْ يَصُومَا، فَيُطْعِمَا مَكَانَ كُلِّ يَوْمٍ مِسْكِينًا

Ita wannan ayar ba shafaffiya ba ce. Tsoho da tsohuwa ne waɗanda suka yi girma a shekaru har ba su iya yin azumin, sai su ciyar da abinci ga talaka a maimakon kowane yini guda. (Sahihi ne. Tafseer Al-Qurtubiy: 2/288).

Amma a kan rashin lafiya irin na olsa malamai sun nuna cewa, da ikon Allaah ana iya warkewa idan aka dace da magani. A ƙarƙashin haka, ba za a ce mai fama da larurar ya ciyar ba, sai fa idan bashi da iko da ƙarfin kai wa ga maganin.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Asslafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments